Wani abu mai kara ya fashe a Los Angeles

Hakkin mallakar hoto AP

Wasu rahotanni da ba a tabbbatar ba na harbin bindiga, wanda daga baya 'yan sanda suka bayyana a matsayin "karar wani abu mai karfi", ya sa mutane sun gudu daga filin saukar jiragen sama da ke birnin Los Angeles, a Amurka.

Mutane sun gudu daga filin jirgin inda suka bar kayansu a daren ranar Lahadi da suka ji rahoton harbe-harben.

An dakaratar da motoci shiga filin jirgin saman, sannan aka hana jirage tashi da sauka, amma a yanzu an ci gaba da aiki.

'Yan sandan birnin sun wallafa a shafinsu na Twitter cewa babu wanda aka harba kuma babu wanda ya ji rauni.

Sannan suka kara da cewa suna bincike a kan karar.

Makonni biyu da suka wuce ma sai da aka rufe wasu bangarori na filin jiragen sama na JFK da ke birnin New York, bayan rahotannin harbi wanda daga baya aka tabbatar ba gaskiya ba ne.

Filin jiragen sama na birnin Los Angeles ne na bakwai a mafi yawan hada-hadar tashi da saukar jiragen sama a duniya.