BH: Za mu ja hankalin duniya - Dangote

Dangote da Bono
Image caption Dangote na sahun gaba wurin tallafawa 'yan gudun hijirar

Jakadan hukumar 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ,Paul David Hewson wanda aka fi sani da Bono, kuma shahararen mawaki a Burtaniya, ya ziyarci jahar Borno da ke arewa-maso-gabashin Najeriya.

Bono ya je Maiduguri bisa gayyatar Alhaji Aliko Dangote, wani babban attajiri a Najeriya domin taimakawa wajen samar da agaji ga al'umar shiyyar arewa masu gabashin Najeriya da rikicin Boko Haram ya jefa cikin mawuyacin hali.

Attajirin ya ce za su hada-gwiwa ne da mawakin wajen jan hankalin kasashen duniya domin su taimaka wajen raya gidauniyar tallafa wa dimbin mutanen da rikicin boko-haram ya daidaita, lamarin da ya ce na bukatar biliyoyin daloli.

Gomnan jihar ta Borno, Alhaji Kashim Shettima ya yi amfani da wannan dama domin radawa sananan titunan na hanyar Baga da ke Maiduguri sunan Alhaji Aliko Dangote.

Haka kuma gidajen da ake gina wa 'yan gudun hijirar da yawansu ya kai dubu 6 wadanda attajirin ya bayar da Naira Bilyan 2 domin a gina su za a rada musu sunan attajirin.

Labarai masu alaka