Nigeria: 'Yan kasuwa na neman aikin gwamnati

Image caption Matasa a shagon dinki a birnin Kano

Matasa 'yan kasuwa a Najeriya wadanda suka yi ilimi mai zurfi, sun fara barin kasuwancin, a inda suka shiga jerin miliyoyin matasan da ke neman aikin gwamnati.

Hakan dai sun ce dole ne sakamakon rashin ciniki da suke fuskanta.

A baya dai matasa da dama musamman a johohi kamar jihar Kano, inda kasuwanci ya zama wani abun tunkaho, ba sa damuwa da yin aikin gwamnati.

Sai dai kuma yanzu haka al'amarin ya sauya sakamakon kuncin rayuwa da wasu ke ganin kasar na fuskanta musamman ta fannin tattalin arziki.

Ga dai rahoton Mukhtar Bawa daga Kano, a inda ya tattauna da wasu 'yan kasuwar da suka bar kasuwancin nasu domin neman aikin gwamnati.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Labarai masu alaka