Fursuna ya zama magajin gari a Pakistan

Hakkin mallakar hoto AFP

An rantsar da wani fursuna a matsayin magajin garin birni mafi girma a Pakistan, Karachi.

Waseem Akhtar na jam'iyyar MQM ya lashe zaben da aka yi a makon jiya da gagarumar nasara.

Bayan kotu ta janye tuhumar da ake yi masa, an futo da shi daga kurkuku zuwa babban filin taro na kasar domin shan rantsuwar kama aiki.

An kama shi ne a watan Yuli bisa zargin cewa ya taimakawa 'yan ta'adda wajen basau gida, lokacin da yake minista shekaru tara da suka wuce.

Mr. Akhtar yace nasar tasa ta tarihi ce, sannan ya bayyana tuhumar da ake yi masa da cewa sharria aka yi masa.

Labarai masu alaka