Congo: Mutane miliyan bakwai sun samu riga-kafi

Hukumar kiwon lafiya ta MDD ta gudanar da allurar riga-kafin kamuwa da cutar Yellow Fever ko farar masasara ga mutane sama da milyan 7 cikin kwanaki goma a Congo.

A cewar hukumar, wannan wani babban aikin gaggawa ne da ba a taba yi ba a Afirka.

Hukumar ta WHO ta yi gargadi game da barkewar cutar da ke hallaka jama'a da ta bulla a Angola, kuma ta bazu zuwa Congo.

Cutar ta kasance wata barazana mai tayar da hankali a Afirka da ba a dauka da muhimmanci ta bangaren kiwon lafiyar al'umma ba.

Har yanzu akwai karancin ruwan magani wajen fuskantar wannan cuta, to sai dai hukumar ta WHO na aiki tare da masu yin magunguna domin samar da wadataccen riga-kafin.

Labarai masu alaka