Samsung ya dakatar da sayar da Galaxy Note 7

Hakkin mallakar hoto Ariel Gonzalez
Image caption Samsung ya ce za a ba duk wadanda suka sayi wayoyin wasu sabbi a madadin su.

Katafaren kamfanin lataroni na Samsung ya dakatar da sayar da sabon wayar tafi da gidanka bayan da aka samu rahotanni fashewar batir a wasu wayoyin.

Kamfanin na kasar Koriya ta Kudu ya sayar da fiye da wayoyi miliyan biyu samfurin Galaxy Note 7 tun bayan da aka kaddamar da wayar a wasu kasashe goma makwanni biyu da suka gabata.

Samsung ya ce za a ba duk wadanda suka sayi wayoyin sabbin wayoyi a madadin su.

Wannan lamari dai babban koma baya ne ga Samsung ya yin da ya rage mako guda kamfanin Apple dake gasa da Samsuung ya kaddamar da sabuwar wayar iPhone.

Labarai masu alaka