China za ta fara aiki da yarjejeniyar dumamar yanayi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan mataki dai na nufin cewa kasar Sin za ta rage amfani da kwal a matsayin makami

China ta amince za ta fara aiki da yarjejeniyar yaki da sauyin yanayi ta duniya da aka cimma a birnin Paris, bara.

Kwamitin majalisar dokokin kasar ne ya amince da yarjejeniyar, gabannin taron kasashen duniya masu karfin masana'antun da za a fara gobe Lahadi a birnin Hangzhou.

Amurka ta yi haramar fara aiki da yarjejeniyar, kuma ana sa ran shugaba Obama da takwaransa na kasar Sin, Xi Jinping za su yi wata sanarwar hadin-gwiwa a nan gaba.

Ana da yakinin cewa yarjejeniyar rage hayaki mai gurbata muhallin za ta yi tasirin ne kawai idan manyan kasashen da ke fitar da kashi 55 bisa dari na hayakin a duniya suka fara aiki da ita a hukumance.

Labarai masu alaka