Rikicin Gabon: An kama sama da mutane 1,000

Jami'an tsaro a kasar Gabon sun kama sama da mutane 1000 a kwana na biyu na rikicin da ake yi a kasar bayan 'yan kasar sun ki amincewa da sakamakon zaben.

An kashe mutane uku a wani hargitsi a Libreville, babban birnin kasar.

An fara zanga-zanga ne a lokacin da aka sanar cewar an sake zaben shugaba Ali Bongo a matasyin shugaban kasar a zaben da aka yi ranar Laraba.

Shugaban jam'iyyar hamayya Jean Ping, wanda ya ke a boye, ya shaidawa BBC cewar an saka bam a shelikwatar jam'iyyarsa.

Majalisar dinkin duniya da Amurka da kasar Faransa wace ta yi musu mulkin mallaka ta yi kira da kwatanta gaskiya a sakamakon zaben.

Labarai masu alaka