An rataye babban dan kasuwa a Bangladesh

Image caption Mir Quasem Ali shi ne shugaban jam'iyyar Jama'atul Islami

Hukumomi a Bangladesh sun zartas da hukuncin kisa akan wani fitaccen dan kasuwa, kuma shugaban jam'iyyar musulunci a kasar mafi girma, Jama'atul-Islami.

Mir Quasem Ali, shi ne mutun na shida da aka rataye a kasar, bayan wata kotu ta musanman ta same shi da aikata laifukan yaki.

Gwamnatin kasar ce ta kafa kotun domin ta binciki wasu zarge-zargen aikata laifi a lokacin yakin neman 'yan cin kasar shekaru 45 da suka wuce.

A lokacin da kotun ta samu Mir Quasem Ali da laifi, kotun ta ce bisa umurninsa ne, magoya bayan sojojin Pakistan suka far ma birnin Chittagong a shekara ta 1971.

Sai dai masu suka, sun zargi gwamnatin da yin amfani da kotun wajen kawar da abokan hamayya.

Labarai masu alaka