Lafiyata ƙalau — Robert Mugabe

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tun shekarar 1987 Robert Mugabe yake shugabancin Zimbabwe

Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe, ya musanta rade-radin da ake yi cewa ba shi da koshin lafiya.

Har ma kuma ya yi arashi, a inda ya ce "ya mutu kuma ya farko."

Mugabe, mai shekara 92, ya mayar da martani ne a lokacin da yake hawa jirgi zuwa birnin Dubai.

Robert Mugabe ya ce zai je Dubai din ne domin ya gudanar da wasu harkokin da suka shafi iyalansa.

Sai dai kuma akwai zargin cewa shugaban zai je neman magani ne domin ba shi da lafiya.

A farkon wannan shekarar ne dai, matar Mugabe, Grace ta ce mijinta zai ci gaba da mulkin kasar ko da kuwa yana cikin kabarinsa.

A baya-bayan nan 'yan kasar ta Zimbabwe na ta faman yin zanga-zanga domin nuna kin jinin kangin tattalin arzikin da kasar ke ciki.

Labarai masu alaka