Najeriya: PENGASSAN za ta shiga yajin aiki

Hakkin mallakar hoto AFP

Kungiyar manyan ma'aikatan mai a Najeriya wato PENGASSAN ta yi barazanar shiga yajin aiki idan gwamnati ba ta aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma a baya ba.

Kungiyar ta ba wa gwamnatin kasar wa'adin makwanni biyu ko ta tsunduma a cikin yajin aiki.

PENGASSAN ta ce gwamnati ta gaza aiwatara da yarjejeniyar sda suka cimmma wata guda ya wuce.

Haka kuma kungiyar ta yi zargin cewa akwai kamfanonin da dama na kasashen waje da ke aiki a Najeriya su ma sun ki aiwatar da abubuwan da yarjejeniyar ta tanada.

PENGASSAN ta nemi gwamnati ta gaggaut zartar da kudirin dokar nan ta inganta bangaren man fetur, wato PIB, ta kuma biya wasu ma'aikata alawus-alawus din su, sannan ta kuma sa baki kan kora ma'aikata da wasu kamfanonin mai ke yi.

Kungiya ta yi barazanar cewa matukan gwamnati ta gaza biya mata bukatun, to za ta tsunduma yajin aiki.

A watan yulin da ya gabata ne kungiyar ta shiga yajin aiki kan wasu batutuwa da suka shafi hakar mai da kuma alawus alwasu din ma'aikata.