Mugabe ya gargadi alkalai kan zanga-zanga

Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe ya soki alkalan kasar wadanda suka ba masu adawa da gwamnati izinin yin zanga-zanga wacce ta rikide zuwa tarzoma.

Ya ce alkalan sun nuna halin rashin ko-in-kula game da zaman lafiya, sannan ya gargade su da kada su rika yin sakaci wajen yanke hukunci.

Wani jagoran 'yan adawa, Tendai Biti, ya zargi Mista Mugabe da yunkurin yi wa bangaren shari'a barazana.

A ranar Litinin, magoya bayan bangaren adawa za su je kotu domin kalubalantar hanin yin zanga-zanga na makonni biyu da aka musu.

A 'yan makonnin nan, an yi ta yin zanga-zanga da tarzoma a kasar ta Zimbabwe yayin da matsalar tattalin arziki a kasar ke kara yin muni.

Labarai masu alaka