Brazil: Ana adawa da sabuwar gwamnati

Hakkin mallakar hoto Reuters

A kasar Brazil, 'yan sanda sun yi amfani da barkonon-tsohuwa wajen tarwatsa dubban jama'ar da ke zanga-zanga.

Dubban mutanen sun bazama tituna a birnin Sao Paulo don yin zanga-zangar kyamar sabuwar gwamnatin Michel Temer.

Kazalika an yi wata zanga-zangar rashin amincewa da wanda ya gaji Dilma Rouseff din a birnin Rio de Janeiro.

Masu zanga-zangar sun yi ta furta wasu kalamai, suna cewa "Temer ya sauka" ya yi gaba, kuma galibinsu sun sanya jajayen tufafi launin jam'iyyar Workers Party ta tsohuwar shugabar kasar.

Labarai masu alaka