Rikicin Syria: An watsa guba a Aleppo

Hakkin mallakar hoto UGC

Mutane 80 ne suka jikkata bayan da aka yi zargin cewa dakarun gwamnatin Syria sun watsa bama-bamai masu 'ya ya da suke dauke da sinadarin Chlorine daga cikin jirgi mai saukar ungulu a garin Aleppo.

Masu aikin jin kai na gaggawa sun ce mutane sun rika fuskantar matsala da numfashi sakamakon harin da aka kai a yankin Sukkari.

Sai dai ba bu wata majiya mai zaman kanta da tabbatar da sahihancin rahoton.

Wani bincike da Majalisar dinkin duniya ta gudanar , ya ce gwamnatin syria ta yi amfani da sinadarin chlorine a lokuta biyu.

Sai dai gwamnati Syria ta sha musanta zargin da ke cewa tana amfani da makamai masu guba.

Labarai masu alaka