Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Donald Trump ya lashe zaben Amurka
  2. Mista Trump ya ce shi shugaban Amurkawa ne baki daya
  3. Hillary Clinton ta amsa shan kaye
  4. Republican sun kare rinjayensu a majalisar dattawa da ta wakilai
  5. Trump ya lashe Ohio, North Carolina, Alabama, Kentucky, Indiana, West Virginia, Mississippi, South Carolina, Texas, Kansas, Dakotas, Tennessee, Oklahoma, Wyoming, Nebraska, Arkansas, Louisia
  6. Clinton ya lashe Virginia, New York, Vermont, New Jersey, DC, Massachusetts, Maryland, Delaware, Illinois, Connecticut, Rhode Island

Rahoto kai-tsaye

Daga Usman Minjibir, Nasidi Adamu Yahya da Naziru Mikailu

time_stated_uk

Sai a tara a karo na gaba

To jama'a da haka muka kawo karshen wannan sharhi da muke kawo muku game da zaben Amurka, inda Donald Trump ya doke Hillary Clinton domin samun nasara. 

Sai a kasance da shafinmu na BBCHausa.com domin cigaba da samun bayanai kan zaben da kuma sauran labarai. 

Bari mu barku da hotunan mutanen da suka yi aiki kan wannan shafi da sauran rahotannin da kuka ji:

Ma'aikatan BBC
BBC
Ma'aikatan BBC
BBC
Ma'aikatan BBC
bb

Yadda shirinmu ya gudana a Facebook

Ga karin bayani kan irin shirye-shiryen da muka gabatar muku kan zaben kasar Amurka. A yi kallo lafiya

View more on facebook

Shugaban Phillippines ya yi wa Trump san-barka

Shugaban kasar Philippine Rodrigo Duterte ya taya murna ga Donald Trump, a cewar wani ministan kasar. 

Duterte "Yana sa ran yin aiki tare da sabuwar gwamnatin domin inganta dangantaka tsakanin Philippines da Amurka ta hanyar mutunta juna da cin gajiyar juna da kuma tabbatar da dimokradiyya da mulki na gari a tsakanin mu", in ji ministan.    

Rodrigo Duterte ya ce zai yi aiki tare da Trump
Getty Images

Tanzania ta taya Trump murna

Shugaban kasar Tanzania John Magufuli ya taya shugaban Amurka mai jiran gado murnar nasarar da ya samu, yana mai ba shi tabbacin ci gaba da kawance tsakanin kasashen biyu.

View more on twitter

Zan sa Amurka a gaba - Trump

Donald Trump
Reuters

Mista Trump ya ce yana sa ran kulla yarjejeniya mai kyau da sauran kasashen duniya:

Babu wani mafarki ko hasashe da ba a iya cimma wa ba. Amurka ba za ta sake karbar wani abu da ba shi ne mafi kyau ko inganci ba. Dole ne mu sake kwato kasarmu, sannan mu cigaba da burin samun nasara da cigaba. A kodayaushe zan saka Amurka a gaba.

Donald Trump

Zan zama shugaban kowa da kowa - Trump

Donald Trump ya shaida wa magoya bayansa cewa: "Na yi alkawari ga dukkan Amurkawa cewa zan zama shugaba na kowa da kowa. Kuma hakan na da muhimmanci a gare ni".

Ga wadanda suka yi goyon bayana, duk da cewa ba su da yawa, ina mika hannu na gare su domin neman shawarwari ta yadda za mu yi aiki tare domin hada kan kasarmu". 

Ku yi hakuri da jiran da kuka yi

 "Ina gode muku matuka. Ku yi hakuri saboda mun ajiye ku anan kuna ta jiranm u, lamari ne mai cike da rudani," a cewar sabon shugaban mai jiran gado.

Turmp ya bayyana

Donald Turmp ya bayyana a gaban magoya bayansa

Labarai da dumi-dumiClinton ta 'amince da shan kaye' a zaben Amurka

Wasu majiyoyi na cewa 'yar takarar shugabancin Amurka ta jam'iyyar Democrats, Hillary Clinton ta amince da shan kaye a zaben shugaban kasar, wanda Donald Trump ya lashe.

An ce ta kira Donald Trump domin taya shi murna.

Labarai da dumi-dumiTrump ya 'lashe zaben Amurka'

Kamfanin dillancin labarai na Associated Press (AP) ya bayyana Trump a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin Amurka.

View more on twitter

Labarai da dumi-dumiTrump ya isa dandalin magoya bayansa

Gidan talabijin na CNN ya rawaito cewa Donald Trump na kan hanyar isa otal din Midtown Hilton, inda magoya bayansa suka taru domin bikin murnar lashe zabe.

Le Pen ta taya Trump murna

Shugabar jam'iyyar masu ra'ayin rikau ta National Front Marine Le Pen ta taya Donald Trump murna a daidai lokacin da ya kama hanyar lashe zaben Amurka da aka yi a ranar Talata, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce "Fatan alheri da murna ga sabon shugaban Amurka Donald Trump da kuma al'ummar Amurka da aka 'yantar!".

Kuri'un jin ra'ayin jama'a sun nuna cewa Le Pen za ta iya lashe zagayen farko na zaben shugabancin kasar Faransa. 

Sai dai za ta sha kaye a zagaye na biyu.

Marine Le Pen
Getty Images

Labarai da dumi-dumiOfishin kamfen din Clinton ya yi raddi

Shugaban ofishin yakin neman zaben Hillary Clinton John Podesta ya ce ba za su ce komai a kan sakamakon zaben kasar ba tukunna. 

Ya ce, "Ana ci gaba da kidaya kuri'u ... Akwai jihohi da dama da muke yin kankankan don haka babu abin da za mu ce a yanzu." 

Mista Podesta ya kara da cewa "ya kamata mutane su je gida su yi bacci domin za a sanar da sakamakon zaben ne gobe."

Jamus ta 'kadu' da jin Trump na kan gaba

Ministar tsaron Jamus Ursula von der Leyen ta shaida wa gidan talabijin din kasar cewa ta yi "matukar kaduwa" da jin cewa dan takarar jam'iyyar Republican Donald Trump na kan hanyar lashe zaben Amurka, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters. 

Ursula von der Leyen ta ce akwai matsala idan Trump ya ci zabe
Reuters
Ursula von der Leyen ta ce sun sha mamaki

Mexico ta kira taron manema labarai

Ministan Kudi na kasar Mexico Jose Antonio Meade da kuma shugaban bankin kasar Agustin Carstens sun kira taron manema labarai wanda za a yi da yammacin ranar Laraba.

Ana sa ran za su tattauna kan faduwar darajar kudin kasar peso, da kuma katangar da Mista Trump ya nace cewa zai gina tsakanin Amurka da kasar a lokacin yakin neman zabensa.

Ana sa ran za a tattauna kan faduwar darajar kudin kasar
Getty Images
Ana sa ran za a tattauna kan faduwar darajar kudin kasar

Republican ta rike rinjayen da take da shi a majalisar wakilai

Jam'iyyar Republican ta lashe zaben majalisar wakilai, abin da ya ba ta damar ci gaba jan ragamar majalisar bayan shafe shekara shida tana kai.

Kamfanin dillancin labarai na  Associated Press ya Democrat sun gaza samun rinjaye.

Ana ci gaba da kirga kuri'u sai dai Republican ta lashe kujeru 218, fiye da adadin da ake bukata domin samun rinjaye.

Majalisar dokokin Amurka
Getty Images

Ra'ayoyinku kan zaben Amurka

Jama'a da dama na tafka muhawara a shafinmu na BBC Hausa Facebook kan sakamakon zaben Amurka da ke fitowa inda Donald Trump yake kan gaba:

To sai mu ce Allah ya ba ta (Clinton) nasara, amma fa gaskiya cikinmu ya duri ruwa ganin yadda Donald Trump yake kan gaba a sakamakon zaben kasar

Rukaiyya Usman Fari Jebuwa

Hakika ana tabka gumurzu tsakanin Trump da Hillary, amma mudai fatan shi ne Allah ya ba wa Amurkawa shugaba mai son hada kawunan al'ummar kasar ba tare da nuna bambanci ba

Muhammad Sulei Garin Rijiya

Ina fatan daga karshe Mrs Hillary za ta yi galaba kan abokin karawarta domin ta kasance mace ta farko a mukamin shugabancin Amurka.

Abdulkadri Hussaini Jambil

Trump ya lashe zaben manyan jihohi

Donald Trump ya lashe manyan jihohi irin su Florida, Ohio, Iowa da kuma North Carolina. 

Haka kuma ya lashe Utah, Alabama, Kentucky, South Carolina, Nebraska, Indiana, West Virginia, Mississippi, Tennessee, Oklahoma da kuma Texas, kamar yadda gidan talabijin na ABC ya yi hasashe.

Trump ya kuma ci zaben Georgia, Missouri, Montana, Louisiana, Arkansas, Kansas, North Dakota, South Dakota, Idaho da Wyoming - dukkan su jihohi ne na masu ra'ayin rikau.

Trump ya ce zai hana Musulmi shiga Amurka
Getty Images

George W Bush bai yi zaben shugaban kasa ba

Tsohon shugaban Amurka, George W Bush, wanda dan jam'iyyar Republican ne, bai zabi Donald Trump da Hillary Clinton ba.

Mai magana da yawunsa ya ce bai zabi kowa ba a bangaren shugaban kasa, amma a bangaren 'yan majalisar dokoki ya zabi jam'iyyar Republican. 

Babu wani daga cikin iyalan Bush da ya yi wa Mr Trump yakin neman zabe ko kuma zabensa.

George W Bush ya zama shugaban Amurka sau biyu
Getty Images
George W Bush ya ce bai ga dalilin yin zaben shugaban kasa ba

Clinton ta lashe Nevada

Hillary Clinton ta lashe kuri'un jihar Nevada, wacce jam'iyyar Republican ke lashewa a tarihi, sai dai yanzu lamarin ya sauya saboda karuwar al'ummar Latin masu amfani da harshen Spaniya.   

Clinton
BBC

Darajar Dala ta fadi

Darajar Dalar Amurka da kudin peso na kasar Mexico ta fadi yayin da kasuwar shunku ta Dow ta yi asarar maki 650. Lashe zaben da Mr Trump ya yi  a Ohio babban tagomashi ne a gare shi domin kuwa babu wani dan takarar jam'iyyar Republican da ya zama shugaban Amurka ba tare da lashe zaben jihar ba. Ya kuma lashe zaben Iowa, wacce rabonta da zaben dan jam'iyyar Republican tun shekarar 2004.

Darajar Dala ta fadi
Getty Images

Magoya bayan Clinton na kuka

Magoya bayan Clinton na cikin rudani ganin yadda sakamakon zaben ke fitowa.

Magoya bayan Clinton
Getty Images

Babbar nasara ga Amurka - mashawarcin Trump

Wani babban mashawarci ga Donald Trump, Curtis Ellis, ya shaida wa BBC cewa "Wannan abin alfahari ne. Dare ne mai muhimmanci ga Amurka  da sauran al'ummar duniya."

Magoya bayan Trump
AFP

Georgia ta zabi Trump

Al'ummar jihar Georgia sun zabi Donald Trump da jam'iyyar Republican. 

Tun shekarar 1996 suke zabar jam'iyyar, amma Mista Trump zai yi murna domin ganin cewa kuri'un jam'iyyar sun dan ragu a shekarun baya-bayan nan.

Trump na daf da lashe zaben Amurka

Hillary Clinton da Donald Trump
BBC
Clinton dai na gaban Trump da maki hudu kacal a kuri'ar jin ra'ayin jama'a kan wanda ya fi farin jini

Dan takarar jam'aiyyar Republican Donald Trump ya shiga gaban Hillary Clinton a fafutukar lashe muhimman jihohi domin zamowa shugaban Amurka.

Wannan na nufin ya kama hanyar zamowa sabon shugaban Amurka.

Magoya bayan Trump

Trump ya kama hanyar lashe zaben Amurka

Dan takarar jam'aiyyar Republican Donald Trump ya shiga gaban Hillary Clinton a fafutukar lashe muhimman jihohi domin zamowa shugaban Amurka.

Karanta karin bayani

Trump ya yi awangaba da Florida

Hasashe ya nuna cewa Donald Trump ya lashe zaben jihar Florida mai matukar muhimmanci, wacce ke da kujerun wakilai 29.

Trump
BBC

Arewacin Carolina ta fada hannun Trump

Donald Trump ya sake lashe muhimmiyar jihar nan ta Arewacin Carolina.

Trump
BBC

Ma'anar lashe kujerun jihar Ohio

Nasarar da Donald Trump ya yi a jihar Ohio ba karamar nasara ba ce a gare shi domin ba a taba samun wani dan jam'iyyar Republican ba wanda ya ci zaben shugabancin kasar ba tare da lashe kuri'un jihar ba. Wani hasashen ma na nuna cewa wannan karon Trump ne ya lashe kuri'un jihar Michigan wadda rabonta da zabar dan jam'iyyar Republican tun 1988.

Tun shekarar 1988 rabon da jam'iyyar Republican ta ci Makwabciyar Ohia wato Michigan
BBC
Duk dan takarar shugabancin kasar da zai ci sai ya lashe kujerun jihar Ohio tukunna

Yadda Rashawa ke kallon nasarar Trump

Wakilin BBC a Moscow ya bayyana cewa: 

Wani mai goyon bayan Trump ya shaida min cewa nasararsa za ta bai wa duniya mamaki... kafafen yada labaran Amurka za su dora alhakin hakan kan masu kutsen kwamfiyuta na Rasha.

In Moscow, 1 Trump fan tells me: "If he wins it'll be a complete flip of the world...the US media will blame Russian hackers" #Election2016

John McCain zai koma majalisa

Kafafen yada labaran Amurka na hasashen cewa Sanata John McCain ya sake lashe zabe a jihar Arizona.

Sanatan mai shekara 80, ya taba tsayawa takarar shugaban kasa bai yi nasara ba.

Abin da zaben Amurka ya janyo

Ƙimar Dalar Amurka da kudin kasar Mexico wato Peso da kasuwar shunku ta Dow Futures sun faɗi ƙasa warwas sakamakon hasashen cewa Hillary Clinton ba za ta kai labari ba.

Colorado ta fada hannun Clinton

An yi hasashen Hillary Clinton ta lashe zaben jihar Colorado.

Clinton
BBC

Clinton ta lashe Virginia

Hasashe ya nuna cewa Hillary Clinton ta lashe kujerun jihar Virginia.

Clinton
BBC

Me ake ciki a Majalisar Wakilai?

Har wa yau, da alama jam'iyyar Republican wadda take iko da Majalisar Wakilan kasar za ta ci gaba da rike kambunta a zauren majalisar.

Kakakin Majalisar Paul Ryan ya shaida wa manema labarai cewa yana fatan za su nasara a zabukan.

Yana kuma sa ran ci gaba da rike mukaminsa a sabuwar majalisar.

Trump ya lashe kujerun Ohio

Hasashe ya nuna cewa Donald Trump ya lashe kuri'un da aka kada a jihar Ohio da gagarumin rinjaye.

Trump
BBC

Jihohin da 'yan takara suka lashe

Dan takarar jam'iyyar Republican, Donald Trump ya lashe kuri'un jihohin da ke Yammacin kasar na tsakiya da kuma kudanci, a inda ita kuma 'yar takarar Democrat, Hillary Clinton ta share jihohin Arewa Maso gabashi, kamar yadda gidan talbijin na ABC News ya yi hasashe.

Trump da jama'arsa
BBC
Trump da jama'arsa suna kallon sakamakon zabe

Har yanzu akwai sauran rina a kaba

A yayin da kafafen yada labarai kamar New York Times da sauransu ke cewa Donald Trump na kan hanyar yin nasara, akwai bukatar a sani cewa har yanzu akwai sauran aiki ja a gaba. 

Akwai muhimman jihohi da ba su bayyana sakamakonsu ba.

Har yanzu ba a san yadda za ta kaya ba a jihohin Ohio da Pennsylvania da Virginia da Florida da kuma North Carolina.

Kan-kan-kan a muhimman jihohi

Clinton da Trump
Getty Images

Donald Trump da Hillary Clinton na tafiya kan-kan-kan a muhimman jihohi da fafatawa ta yi zafi sosai.

Babu tabbas kan inda sakamakon zai kaya a jihohin da suka hada da Florida da Ohio da kuma Virginia.

Gidan talabijin na ABC News ya yi hasashen cewa Mista Trump ya yi nasara a jihohin Kudancin kasar, yayin da Hillary Clinton ta samu galaba a jihohin Arewa.

Ana bukatar dan takara ya samu kuri'u 270 daga cikin manyan wakilai masu zaben shugaban kasa 538 (wato electoral college) domin samun nasara.  

Amurkawa sun yanke hukunci

Al'ummar Amurka sun yanke hukunci kan mutumin da zai jagorance su a tsawon shekaru hudu masu zuwa tsakanin Hillary Clinton da Donald Trump.

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta BBC ta nuna cewa Clinton na gaban Trump da maki hudu kacal.

Duka Misis Clinton da Mista Trump sun kada kuri'unsu a mazabu daban-daban a birnin New York.  

Masu kada kuri'a
Getty Images

An samu dogayen layuka a wasu jihohin, abin da ke nuna yadda jama'a suka fito sosai.

Wasu wuraren kada kuri'ar sun samu matsalolin na'ura, abin da ya haifar da jinkiri.

Barkanmu da warhaka

Jama'a da fatan kun tashi lafiya. 

Masu iya magana na cewa rana ba ta karya sai dai uwar diya ta ji kunya.