Takaitacce

  1. Moussa Dembele
  2. Bayern Munich ta ci Chelsea 3-2
  3. Sanchez ya matsa sai ya bar Arsenal
  4. Lukaku na son kafa tarihi a Man United
  5. Chelsea za ta kashe makudan kudade
  6. Man United 'za ta iya daukar' Sanches
  7. West Ham ta sayi Javier Hernande

Rahoto kai-tsaye

Daga Naziru Mikailu da Mohammed Abdu

time_stated_uk

Nan muka kawo karshen shirin

Da fatan za ku tara a shirinmu na gobe domin jin wasu labarin wasanni

Kwantan wasan Firimiyar Nigeria

Kai tsaye
LMCNPFL

Burnley ta dauki Bardsley

Burnley ta kammala daukar mai tsaron bayan Stoke City, Phil Bardsley. Dan wasan mai shekara 32 ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyu a Turf Moor.

Kai tsaya
Getty Images

Dembele zai ci gaba da zama a Celtic

Brendan Rodgers ya ce Moussa Dembele yana jin dadin zama a Celtic, kuma kungiyar ba ta shirya sayar da shi ba.

Dembele ya ci kwallo 32 a wasa 39 da ya yi wa Celtic a kakar da ta kare tun lokacin da ya koma kungiyar daga Fulham kan fan 500,000.

Celtic za ta kara da Rosenborg a wasan cike gurbin gasar cin kofin Zakarun Tuari a Celtic Park a ranar Laraba.

Babu kulob din da ya taya dan kwallon mai shekara 21, duk da rade-radin cewar kungiyoyi 10 na son zawarcin Dembele.

Brendan Rodgers

An ci kwallo 308 a Firimiyar Nigeria

Bayan da aka yi wasa 308 a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria, an ci kwallo 611 bayan da aka kammala wasannin mako na 31 a ranar Lahadi.

Kuma kwallo 472 aka ci a gida yayin da aka zazzaga 139 a waje, kuma saura wasa 72 a kare gasar da ake yi.

Kai tsaye
Getty Images

Robert Kubica zai yi tseren gwaji

Robert Kubica zai yi wa kamfanin Renault tseren mota a matsayin gwaji a karon farko a Hungary a ranar 2 ga watan Agusta.

Rabon da dan wasan mai shekara 32 ya tuka mota a Formula 1 tun hatsarin da ya yi a 2011, inda jikinsa ya shanye in banda hannunsa na hagu da ya dunga aiki.

Kai tsaye
Getty Images

Greg Rutherford ba zai yi Burtaniya wasa ba

Zakaran tsallen badaken duniya Greg Rutherford ya janye daga shiga gasar wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya da za a yi a Landan, sakamakon raunin da ya yi.

Dan wasan Burtaniya wanda ya ci lambar zinare a gasar Olympic da aka yi a Landan a 2015 da kambun duniya da ya lashe a 2015 ya ce ya yi bakinciki da ba zai shiga wasannin ba.

Haka shima Richard Kilty wanda aka zaba ya yi wa Burtaniya tseren mita 400 ta 'yan wasa hudu ba zai shiga gumurzun ba, sakamakon karya tsaya da ya yi a lokacin atisaye.

Burtaniya ta kara Shara Proctor da Jazmin Sawyers da Lennie Waite da Marc Scott da kuma Jess Turner cikin tawagarta.

Kai tsaye
Getty Images

Conte ya yi wa Fabregas alkawari

Kocin Chelsea, Antonio Conte ya yi wa Cesc Fabregas alkalin zai dinga saka shi a wasa akai-akai don haka ya bukaci dan kwallon ya ci gaba da zama a Stamford Bridge in ji Everning Standard.

Kai tsaye
Getty Images

Wasu damben da aka yi a gidan Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria

Maradona ya goyi a samar da na'ura da za ta taimakawa Alkalan wasa

Diego Maradona ya goyi da bayan a kirkiro kimiyar da za ta taimakawa alkalan wasa wajen tantance idan kwallo ya shiga raga ko akasin hakan. Maradona ya ci Ingila da hannu a gasar cin kofin duniya wasan daf da na kusa da na karshe inda Argentina ta lashe karawar da ci 2-1. Haka kuma a fafatawar ce Maradona ya yi wata bajinta inda ya yanke masu tsaron bayan Ingila biyar a karawar da Ingila.

Kai tsaye
Getty Images

Leicester City ta dauki Eldin Jakupovic

Leicester City ta dauki mai tsaron raga Eldin Jakupovic daga Hull City kan yarjejeniyar shekara uku in ji Marca.

Dan kwallon shi ne na uku da Leicester ta dauka a bana bayan Harry Maguire da kuma Vicente Iborra.

Jota ya koma Wolves da taka-leda

Wolves ta dauki aron matashin dan wasan tawagar kwallon kafa ta Portugal, Diogo Jota daga Atletico Madrid.

Dan wasan mai shekara 20 ya buga wa Porto wasanni aro a bara, inda ya yi wasa karkashin kocin Wolves Nuno Espirito Santo. Jota ya fara buga kwallo a Pacos Ferraira daga nan ya koma Atletico kan yarjejeniyar shekara biyar a bara.

Kai tsaye
Getty Images

Palace ta dauki Riedewald

Crystal Palace ta dauki dan kwallon Netherlands mai tsaron baya Jairo Riedewald daga Ayax kan yarjejeniyarshekara biyar.

Riedewald, mai shekara 20, a baya ya buga kwallo karkashin sabon kocin Palace Frank de Boer, wanda ya fara saka shi a wasa a 2013.

Dan kwallon ya yi wasa 93 kuma yana daga 'yan wasan da suka ci kofin gasar Netherland a 2014.

Kai tsaye
Getty Images

Liverpool ta ce Palace ta biya kudin Sakho

Daily Mirror ta wallafa cewar Liverpool ta shaidawa Crystal Palace cewar ko dai ta biya kudin Mamadou Sakho fan miliyan 30, idan ba haka ba, ba za ta amince ta sake bata shi aro ba.

Kai tsaye
Getty Images

United za ta iya daukar Reanato

Independent ta wallafa cewar Manchester United za ta iya daukar Renato Sanchez na Bayern Munich in ji koci Carlo Ancelotti, wanda ya bayar da hasken cewar ba zai bar Arturo Vidal ya bar buga gasar Bundesliga ba.

Leicester ta yi wa Mahrez farashi

Roma ta tanadi fan miliyan 30 da wasu karin kudin tsarabe-tsarabe daukar Riyad Mahrez dan kwallon tawagar Algeria, sai dai Leicester City ta ce sai dai a biyata fan miliyan 50 in ji Daily Mail.

Tun a cikin watan Mayu Mahrez ke son barin Leicester City

Kai tsaye
Getty Images

Takaitattun Labarin Wasanni na safiyar Talata

Madrid za ta dauki Mbappe a bana

Real Madrid za ta sayi Kylian Mbappe kan kudi Yuro miliyan 180 daga Monaco domin ya buga mata tamaula a Santiago Bernabeu a bana in ji jaridar Marca.

A labarin da ta wallafa ta ce wannan kudin da Madrid za ta biya Monaco zai haura wanda Manchester United ta sayi Paul Pogba daga Juventus a 2016.

Kai tsaye
Getty Images

Swansea ta yi watsi da tayin Everton na sayen Sigurdsson

Swansea ta yi watsi da tayin fan miliyan 50 da Everton ta yi domin sayen dan wasan Iceland Gylfi Sigurdsson.

Swansea na bukatar fan miliyan 50 ne kan dan kwallon mai shekara 27.

Sigurdsson bai bi kulob din zuwa Amurka ba, kuma yana ci gaba da atisayi ne da tawagar 'yan kasa da shekara 23 ta kulob din.

Tayin na ranar Litinin shi ne na farko da Everton ta yi kan dan wasan na tsakiya, sai dai ita ma Leicester City ta yi yunkurin sayensa tun farko.

Gylfi Sigurdsson
Getty Images

Man United 'za ta iya daukar' Sanches

Manchester United za ta iya daukar dan wasan Bayern Munich da kuma Portugal Renato Sanches, mai shekara 19, kamar yadda kocin kulob din Carlo Ancelotti ya ce.

Sai dai ya nace cewa dan kwallon Chile Arturo Vidal, mai shekara 30, ba zai bar kulob din, a cewar jaridar Independent.

Renato Sanches
Getty Images

West Ham ta sayi Javier Hernandez

West Ham ta kammala sayen tsohon dan wasan Manchester United Javier Hernandez daga Bayer Leverkusen kan kudi fan miliyan 16.

Dan kwallon na kasar Mexico ya sanya hannu kan kwantiragin shekara uku.

A watan Mayu, Hernandez - wanda aka fi sani da Chicharito, ya zamo dan kwallon da ya fi zira wa kasarsa kwallo.

Ya ci kwallo 39 a wasa 76 da ya buga a kulob din na gasar Bundesliga.

Javier Hernandez
Getty Images

An tsawaita hukuncin dakatar da Eric Bailly

Dan kwallon Manchester United, Eric Bailly ba zai bugawa kungiyar wasa uku ba, sakamakon jan kati da aka yi masa a karawa da Celta Vigo a gasar Europa League.

An kori dan kwallon ne mai shekara 23 a wasan daf da karshe a ranar 11 ga watan Mayu, inda hakan ya sa bai buga karawar karshe da United ta ci Ajax 2-0 ba.

Yanzu kuma hukumar kwallon kafa ta Turai ta tsawaita hukuncin dakatarwar zuwa wasa biyar, karin kwana biyu kan ukun da ta fara yi masa.

Bailly ba zai bugawa United karawar da za ta yi da Real Madrid a ranar 8 ga watan Agusta da wasan farko na gasar cin kofin Zakarun Turai ba.

Eric Bailly
AFP

Chelsea 'za ta kashe makudan kudade'

Jaridar Daily Mirror ta rawaito cewa za a bai wa kocin Chelsea Antonio Conte karin fan miliyan 150 domin sayen 'yan wasa.

Kuma ana sa ran dan wasan baya na Southampton Virgil van Dijk da na Juventus Alex Sandro, su ne a sahun gaba a jerin wadanda zai nema.

Hakan na nufin kudin da Chelsea za ta kashe za su iya haura fan miliyan 218 din da Manchester City ta kashe kawo yanzu.

Alex Sandro
AFP

Sanchez 'zai rage albashinsa' don ya koma Man City

Alexis Sanchez
AFP

Rahotanni daga Ingila sun ambato wata majiya na cewa dan wasan Arsenal Alexis Sanchez zai yarda a rage masa albashi domin ya koma Manchester City da murza-leda a bana.

Dan kwallon mai shekara 28 dan kasar Chile na son ya koma City a maimakon Bayern Munich, Paris St-Germain ko Juventus, a cewra jaridar Independent.

Ya kamata Martial ya jajirce – Mourinho

Kocin Manchester United, Jose Mourinho ya bukaci Anthony Martial ya zama yana kan ganiyarsa a koda yaushe.

An alakanta cewar Martial zai koma Inter Milan da taka-leda kan cinikin da zai bai wa Ivan Perisic damar barin buga gasar Italiya.

Martial shi ne ya bai wa Jesse Lingard kwallon da aka ci Real Madrid a wasan da suka tashi kunnen doki 1-1 a Santa Clara, inda United ta yi nasara a bugun fenariti.

Har yanzu United ba ta mori matashin dan wasan da ta dauko daga Monaco a 2015 kan kudi fan miliyan 36 ba.

Anthony Martial
Getty Images

Lukakau na son kafa tarihi a Man United

Romelu Lukaku
Getty Images

Romelu Lukaku ya ce yana kafa sabon tarihi na kashin kansa a Manchester United.

Dan kwallon na kasar Belgium mai shekara 24, ya koma United ne kan kudi fan miliyan 75 bayan ya zura kwallo 25 a gasar Firimiya a Everton a kakar da ta gabata.

Lukaku, wanda shi ne dan wasan kasar waje na farko da ya zura kwallo 80 a Firimiya kafin ya cika shekara 24, ya ce: "ba zan iya cewa burina ya cika ba tukunna.

"Akwai sauran aiki a gabanmu, kuma in farin ciki da hakan, domin yana nufin cewa zan kara gogewa fiye da yadda na ke."

Barkanmu da Hantsi

Jama'a barkanmu da sake saduwa a filin na yau inda za mu ci gaba da kawo muku bayanai kan wainar da ake tonawa a fagen wasanni.