Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Mece ce makomar Sanchez
  2. 'Ina son Chamberlain ya tsaya'

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

Man City za ta sallamar da Mangala in...

Manchester City za ta sallamar da dan Faransa Eliaquim Mangala, mai shekara 26, ga Inter Milan idan kungiyra kwallon kafa ta Italiyar ta yarda ta biya fam miliyan 24 kan dan tsohon dan wasan Porto, in ji jaridar Daily Express.

Eliaquim Mangala
Getty Images

Southampton na sha'awar dan Lazio

Southampton na sha'awar dan wasan Lazio kuma dan Netherlands, Wesley Hoedt, in ji Press Association.

Wesley Hoedt
Getty Images

Everton ta kusa kammala sayan Gylfi Sigurdsson

Kociyan Everton, Ronald Koeman, ya ce dan wasan tsakliyar Swansea, Gylfi Sigurdsson, ya kammala gwaje-gwajen lafiya kuma ya kusa kammala komawa Toffees kan kudi fam miliyan 45.

Gylfi Sigurdsson
Rex Features

Deportivo La coruna na neman Diego Costa

Deportivo La Coruna tana aiki kan wata yarjejeniya da Atletico Madrid domin Diego Costa, mai shekara 28, in ji La Voz de Galicia .

Diego Costa dai, yana tsaka mai wuya a Chelsea wadda ta gindaya masa wasu sharrudan da ta ce dole ya cika kafin ta sayar da shi.

Costa
Getty Images

An ki sayar wa Chelsea dan wasa

Juventus ta ki bikon da Chelsea ta yi kan dan wasanta na baya, Alex Sandro, mai shekara 26, jaridar Daily Mail.

Alex Sandro
Getty Images

Chelsea za ta sayi Rose?

Jaridar The Sun na cewaChelsea tana kokarin biyan fam miliyan 50 domin sayan dan wasan Tottenham Hotspur, Danny Rose, bayan dan wasan ya bata wa Spurs rai ta hanyar sukar manufofin musayar 'yan wasa da na albashin kungiyar kwallon kafar..

Kazalika,Spurs ta cimma yarjejeniya da dan wasan bayan Paris St-Germain , Serge Aurier wanda a da Manchester United take hako, in ji L'Equipe.

Chelsea Rose
Getty Images

Jese Rodriguez ya koma Stoke City

Tsohon dan wasan Real Madrid, Jese Rodriguez, ya koma Stoke City akan aro daga Paris St-Germain.

Jese Rodriguez
Getty Images

Sanchez na son fam 150,000 daga Chelsea

Goal ta ruwaito cewar dan wasan tsakiya Alex Oxlade-Chamberlain yana son a ba shi fam 150,000 a ko wane mako kafin ya koma taka leda a Chelsea daga Arsenal.

Chamberlain
Getty Images

Ba za a iya kwatanta Costa da Sanchez ba -Wenger

Ba yadda za a kwatanta halin da Alexis Sanchez ke ciki da halin da Diego Costa ya shiga a Chelsea in ji kociyan Gunners, Arsene Wenger.

Sanchez, mai shekara 28, yana cikin shekara ta karshe a kwantiraginsa a filin wasan Emirates, kuma har yanzu bai sabunta kwantiraginsa ba, yayin da Costa ya ce yana son barin Blues.

A baya dai Wenger, mai shekara 67, ya ce Sanchez "respects" ya mutunta hukuncin da ya yanke na ci gaba rike dan wasan gaban Chile a Arsenal a wannan kakar, duk da cewar an ba da rahoton cewar Manchester City da Paris St-Germain na nemansa.

Sanchez
Getty Images

Chelsea na neman dan wasan gaban Torino

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea na kokarin sayan dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Torino da ke Italiya, Andrea Belotti, domin ta maye gurbin Diego Costa .

Andrea Belotti
Getty Images

Joselu ya koma Newcastle

Newcastle United ta kammala sayandan wasan gaba Joselu daga Stoke City.

Joselu
Getty Images

Ina son Chmaberlain ya tsaya -Wenger

A wata hirar da ya yi da 'yan jarida, kociyan Arsenal, Arsene Wenger, ya ce yana son Oxlade-Chamberlain ya tsaya. Ga yadda hirar ta tafi:

Tambaya: Shin ka hakikance cewar Oxlade-Chamberlein zai kasance a nan har karshen kaka?

Wenger: E.

Question: Saboda me?

Wenger: Ina ganin kimarsa sosai, kuma yana cikin 'yna wasan da ke kan hanyarsu zuwa sama. A gani na ina son ya dade a nan. Na yi imanin cewar zai kasance dan wasan Ingila da kowa zai yi ta kallo nan da shekara biyu zuwa uku..

Wenger
Getty Images