Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Wenger ya bai wa 'yan Arsenal Hakuri
  2. Liverpool na neman Thomas Lemar
  3. Swansea za ta tayan dan wasan Man City
  4. Chelsea na da kwarin guiwar sayan Drinkwater
  5. Barca ta sayi Dembele
  6. Liverpool ta sayi Naby Keita

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

Sai gobe!

Jama'a, abun da ya samu kenan a jerin rahotannin wasannin da muke kawo muku kai-tsaye a wannan shafin a yau. Ku ci gaba da kasancewa da BBC Hausa.

Birminghan ta dauki aron dan Chelsea

Kungiyar kwallon kafa ta Birmingham City ta dauki aron dan wasan tsakiyar Chelsea, Jeremie Boga, na kaka daya.

Dan wasan dan asalin kasar Ivory Coast, ya shafe shekara biyu da ya wuce a Rennes da Granada a zaman aro.

Birmingham
Getty Images

Siem de Jong ya sake komawa Ajax daga Newcastle

Ajax ta sake sayan dan wasan tsakiyar kasar Netherlands, Siem de Jong, daga Newcastle kan kudin da rahotanni suka ce ya kaifam miliyan 4.

Dan wasan mai shekara 28 ya koma Magpies ne daga Ajax a shekarar 2014 kan kudin da ba a bayyana yawanshi ba a wata yarjejeniyar shekara shida, amman ya yi ta fama da raunuka, ciki har da ciwon huhu. Ya buga wasanni 26, yawancinsu a matsayin wanda ya canji wani dan wasa, amman ya buga wasa sau 23 a lokacin ya je wasan aro a PSV Eindhoven a kakar bara.

Ajax
Getty Images

An yi wa shugaban Barcelona ihu

Bikin gabatar da sabon dan kwallon da Barcelona ta saya, Ousmane Dembele ya ci karo da cikas, bayan da magoya bayan kungiyar suka yi ta rera wakokin neman shugabanta ya yi ritaya.

Dembele mai shekara 20, ya zama na biyu da aka saya mafi tsada a tarihin tamaula a duniya kan fam miliyan 135.5, bayan Neymar wanda ya koma Paris St Germain da murza-leda kan fam miliyan 200.

Bikin ya ci karo da cikas bayan da aka yi jinkirin sa'a biyu, sakamakon rashin samun takardun rijistar dan kwallon daga Dortmund.

A lokacin ne magoya bayan Barcelona 18,000 suka rinka busa usur da rera wakokin cewar Bartomeu ya yi ritaya.

Karanta cikakken labarin a nan

Shugaban kulob din Barcelona
Getty Images
A bana ne Real Madrid ta doke Barcelona 5-1 gida da waje a Spanish Super Cup

Messi ya ci kwallo sama da 350 a La Liga

Dan wasan Barcelona da tawagar kwallon kafa ta Argentina Lionel Messi ya ci kwallo sama da 350 a gasar La Liga.

Dan wasan ya ci 349 kafin ya kara biyu a karawar da Barcelona ta ci Deportivo Alaves 2-0 a ranar Asabar a wasan mako na biyu a gasar ta La Liga a ranar Asabar.

Messi ya zama na biyu da ya fi cin kwallaye da yawa a kungiya daya tsakanin manyan gasar kwallon kafa ta Turai, bayan Gerd Muller da ya ci wa Bayern Munich kwallo 365.

Cikin kwallo 351 da ya ci a La Liga, guda 274 da kafar hagu ya ci sannan ya zura 63 a raga da kafar dama, kuma 14 da kai ya ci su.

Messi ya ci Espanyol a kakar wasan 2007 da hannu, an kuma karbi kwallon a cikin wadanda ya ci da kai.

Messi
Getty Images

Las Palmas na neman dan wasan Chelsea

Kungiyar kwallon kafa ta Las Palmas da kungiyar Cagliari suna neman dan wasan gaban Chelsea, Loic Remy, mai shekara 30, in ji jaridar Daily Mail.

Loic Remy
Getty Images

Chelsea za ta sake taya Llorente

Chelsea za ta sabunta sha'awarta ta dan wasan gaban Swansea, Fernando Llorente, mai shekara 32, ta hanyar taya shi dai-dai lokacin da kungiyar take neman sayan akalla 'yan wasa uku kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa, in ji jaridar Independent.

Fernando Llorente
Getty Images

Conte na son Chelsea ta kara karfi

Kociyan Chelsea, Antonio Conte, ya ce Blues na bukatar kara 'yan wasa domin kara wa kulob din karfi.

Ya ce kungiyar na iya kokarinta na kara 'yan wasa.

Conte
Getty Images

Nawa kudin Mayweather a yanzu?

Bayan Floyd Mayweather ya doke Conor McGregor a damben boksin da suka yi karshen mako, kudin dan bamben ya kai akalla fam miliyan 450, in ji jaridar Mirror.

Mayweather
Instagram/ Mayweather

Borussia Dortmund ta sayi Yarmolenko

Borussia Dortmund ta sayi dan wasan gaban Dynamo Kiev dan asalin Ukraine, Andriy Yarmolenko kan kudin da ba a bayyana ba a wata yarjejeniyar shekara hudu.

An bayyana zuwan dan shekara 27 din ne wasu mintuna kafin Barcelona ta bayyana cewar tsayi dan wasan gaban Dortmund, Ousmane Dembele, a wata yarjejeniyar fam miliyan 135.5.

Yarmolenko
Getty Images

Liverpool ta sayi Naby Keita

Liverpool ta sayi dan wasan tsakiyar Leipzig, Naby Keita, kuma dan wasan zai fara taka wa Reds leda ne ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2018.

Keita na cikin 'yan wasan da kociya Jurgen Klopp yake nema.

Kudin yarjejeniyar sayan dan wasan ya fi fam miliyan 35 da Liverpool ta biya wajen sayan Andy Carroll daga Newcastle .

Naby Keita
Getty Images

PSG ta cimma yarjejeniyar aron Kylian Mabappe

Paris St-Germain ta cimma yarjejeniyar aron dan wasan gaban Monaco mai shekara 18, Kylian Mbappe, da zabin sayanshi kan kudi fam miliyan 166, in ji L'Equipe .

Nbappe
Getty Images

Barca ta sayi Dembele

Barcelona ta kammala sayan dan wasan gaban Borussia Dortmund, Ousmane Dembele, kan kudi fam miliyan 96.8, kuma za a iya kara kudin zuwa fam miliyan 135.5.

San wasan dan Faransa mai shekara 20 ya rattaba hannu kan yarjejejniyar shekara biyar a Nou Camp tare da jagoran kungiyar, Josep Maria Bartomeu ranar Litinin.

Yarjejeniyar ita ce ta biyu a tsada a fagen tamaula bayan wadda Neymar ya rattaba wa hannu kan kudi fam miliyan 200.

Dembele
Getty Images

'Mene ne amfanin zaman Sanchez a Arsenal?'

Tsohon dan wasan gaban Arsenal, Thierry Henry, ya nuna tababa game da daililin da ya sa dan wasan gaban Chile, Alexis Sanchez, zai ci gaba da zama a Gunners bayan Liverpool ta lallasa Arsenal din 4-0 . Dan wasan mai shekara 28 yana da sauran shekara daya a kwantiraginsa kuma an alakanta shi da komawa Manchester City, in ji Sky Sports.

Sanchez
Getty Images

Napoli na son mai tsaron gidan Liverpool

Kungiyar kwallon kafa ta Napoli na hakon mai tsaron gidan Liverpool,Simon Mignolet, mai shekara 29, in ji Gianluca Di Marzio.

Simon Mignolet,
Getty Images

West Brom ta taya dan wasan Fenerbache

West Brom ta yi wa Fenerbache tayin fam miliyan 10 kan dan wasanta mai shekara 28, Josef de Souza, da aka fi sani da Souza, tare da tambaya game da dan wasan bayan Bournemouth, yrone Mings, mai shekara 24, jaridar Daily Mail.

Josef de Souza
Getty Images

Mustafi na shirin barin Arsenal

Dan wasan bayan Arsenal, Shkodran Mustafi, yana shirin barin Gunners domin komawa Inter Milan shekara daya kacal bayan dan wasan na Jamus, mai shekara 25, ya koma Arsenal daga Valencia kan kudi fam miliyan 35, in ji ESPN.

Shkodran Mustafi
Getty Images

Zamalek ta yi sabon kociya

Kungiyar kwallon kafa ta Zamalek da ke Masar ta fitar da sanarwar cewar Montenegrin Nebojsa Jovovic ya rattaba ahannu kan yarjejeniyar shekara biyu a matsayin kociya.

Kociyana ya maye gurbin dan kasar Portugal, Augusto Inacio wanda ya bar kulob din a watan Ylulin bayan ya shafe kasa da wata hudu yana jagorancin kungiyar .

Nebojsa Jovovic
Getty Images
Nebojsa Jovovic ne ya jagoranci kungiuyar Al Faisaly ta Jordan zuwa wasan karshe na cin kofin larabawa a farkon watannan

'Liverpool za ta sayi Chamberlain'

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta tashi tsaye kan batun neman Oxlade-Chamberlain, wanda ake ganin ya fi son ya koma Chelsea, kamar yadda jaridar Sunday Mirror ta ruwaito.

Arsenal tana shirin sayen dan kwallon Real Madrid, Marco Asensio, a kan fam miliyan 75 gabanin rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan Turai ranar Alhamis, in ji jaridar Sunday Express.

Chamberlain
Getty Images

Kociyan West Ham na tsaka-mai-wuya

Kociyan West Ham United, Slaven Bilic, yana kokarin kare aikinshi bayan ya kasa samun maki ko daya a wasanni uku na farko da ya yi a gasar Firimiya, in ji jaridar Sun.

Slaven Bilic
Getty Images

Arsenal ta shiga babbar matsala - Keown

Tsohon dan wasan Arsenal, Martin Keown, ya nuna takaicinsa ga kayen da Arsena ta sha a hannun Liverpool 4-0.

Keown ya ce: "Arsenal ta kasa auna mai tsaron gida ko sau daya a yau. Wannan wani lamari ne da ba za a iya raya a zuciya ba. An sha ta kwallaye takwas. Muna batun cewar Slaven Bilic zai rasa aikinshi. An ci kungiyarsa (West Ham) kwallaye 10. Daga ita sai Arsenal."

Tsohon dan wasan ya ce shi ya kasa gane dalilin sayar da wasu 'yan wasan Arsenal da na barin wasu 'yan wasan a benci.

Martin Keown
Getty Images

Liverpool ka iya ba da aron Origi

Kociyan Liverpool,Jurgen Klopp, ya bar kofar iya ba da aron dan wasan gaban Belgium, Divock Origi, mai shekara 22, idan har kulob din zai iya kawo 'yan wasan kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa, in ji Liverpool Echo.

Klopp
Getty Images

Liverpool ta taya Thomas Lemar

Liverpool ta yi tambaya domin sayan dan wasan tsakiyar Monaco mai shekara 21, Thomas Lemar, kan kudi fam miliyan 55, in ji Daily Telegraph.

Thomas Lemar
Getty Images

Swansea za ta taya dan wasan Man City

Swansea City za ta taya dan wasan gaban da ta sayar wa Manchester City yayin da take kokarin sake sayan Wilfried Bony, in ji jaridar Daily Mail.

Wilfried Bony
Getty Images

West Brom ta yi watsi da tayin Evans

An yi watsi da tayin fam miliyan 23 da Leicester City ta yi wa dan wasan bayan na West Brom, Jonny Evans kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasan ranar Alhamis.

A baya dai an yi watsi da tayin fam miliyan 10 da Foxes ta yi wa tsohon dan wasan Manchester United, mai shekara 29.

Shi ya sa kungiyar ta sake taya dan wasan a karo na biyu.

West Brom ta ce kudin da aka taya dan wasan ya yi kasa da abun da take nema a kanshi.

Johnny Evans
Getty Images

Chelsea na da karfin guiwar sayan Drinkwater

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tana da kwarin guiwar iya sayan dan wasan tsakiyar Leicester City da aka yi imanin cewar ya kai kudi fam miliyan 30 kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa ranar Alhamis, in ji Daily Telegraph.

Drinkwater
Getty Images

Wenger na neman goyan baya

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger, ya yi kira ga magoya bayan kungiyarsa da su cigaba da mara mata baya.

Wenger ya yi kiran ne bayan ya bayyana kayen 40- da kulob dinshi ya sha a hannun Liverpool a matsayin wani gagarumin bala'i.

'Yan wasan Gunners sun kasa auna mai tsaron gidan Liverpool a wasan da ake ganin ba su tabuka komai ba.

"Idan wasu na ganin ni ne matsalar, toh, ina neman gafarasu na kasancewa matsalar," in ji Wenger a hirarsu da Sky Sports.

Wenger
Getty Images

Barka da hantsi!

Jama'a barkanku da sake shigowa shafinmu na labaran tamaula kai tsaye.