Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Buhari na ziyarar ne sama da shekara biyu bayan hawansa mulki
  2. Shugaban ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar ya yi
  3. Ya yaba wa yadda jama'ar jihar suka tarbe shi
  4. Wasu Kanawa sun soke shi da gazawa wurin yi musu ayyukan cigaba
  5. Zai kuma gana da malaman addini da 'yan kasuwa
  6. Kano ce ta fi kowacce jiha ba shi kuri'u a zaben 2015

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan, Yusuf Yakasai da Nasidi Adamu Yahya

time_stated_uk

A nan muka kawo karshen bayanan da muke kawo muku kai tsaye na ziyarar Shugaba Buhari a Kano.

Sai ku ci gaba da kasancewa da shafinmu na bbchausa.com don karanta karin wasu labarai.

Shugaba Buhari ya bar asibitin Giginyu

.
.

Tawagar Shugaba Buhari ta bar asibitin Giginyu bayan kaddajmar da wani asibiti da gwamnatin Kano ta gina.

Nan gaba kuma zai kaddamar da wani asibitin a titin Gidan Zoo.

Wakilinmu da ke can, Muhammad Abdu Tudunwada, ya ce tuni titin ya dinke da jama'a masu dakon karasowar shugaban.

Buhari ya nemi gwamnoni su yi koyi da Ganduje

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi sauran gwamnoni su yi koyi da gwamnan jihar Kano wurin gudanar da ayyukan ci gaban jihohinsu.

A wani takaitaccen jawabi da ya yi a wurin kaddamar da asibiti a ungunwar Giginyu da ke tsakiyar birnin, Shugaba Buhari ya ce irin wadannan ayyuka suna kawo sauyi sosai a rayuwar al'uma.

A nasa jawabin, Gwamna Ganduje ya yaba wa shugaban kasar bisa ziyarar da yake yi a jihar.

Asibitin yana cikin manyan ayyukan da Gwamna Ganduje ya aiwatar
BBC

Kalli ficewar ayarin Motocin Buhari..

Kalli ficewar ayarin motocin Buhari daga gidan gwamnatin Kano.

View more on twitter

Buhari zai gana da malaman addini

Ziyarar Shugaba Buhari a Kano
BBC

Wani na hannun damar Shugaba Muhammadu Buhari ya shaida wa BBC cewa shugaban zai gana da malaman addini a Kano domin yi musu godiya kan addu'o'in da suka rinka yi masa a lokacin da ba shi da lafiya.

Ba ya ga malaman addini, shugaban zai kuma gana da manyan 'yan kasuwa da sauran shugabannin al'umma a ziyarar kwana biyun da zai yi.

Shugaban dai ya shafe watanni yana jinya a kasar Ingila, abin da ya sa aka dinga shakku kan ko zai iya cigaba da mulkin kasar.

Jihar Kano na daya daga cikin wuraren da aka rinka shirya addu'o'i na musamman domin nema wa shugaban lafiya.

Buhari: An gafartawa fursunoni 500

Buhari: An gafartawa fursunoni

'Ba ma murna da zuwan Buhari'

Wasu mazauna birnin Kano sun shaida wa BBC cewa ba sa murna ko kadan da ziyarar da shugaban kasar Muhammadu Buhari ke yi a jihar.

Sun shaida wa wakilinmu Ibrahim Isa cewa ba su ga wani abin arziki da shugaban ya yi wa jihar ba a sama da shekara biyun da ya shafe yana mulki.

Sai dai magoya bayan shugaban sun ce inganta tsaro da habaka aikin noma na daga cikin ayyukan da ya yi kawo yanzu.

Jihar Kano ce ta fi kowacce jiha bai wa shugaban kuri'a a zaben da ya gabata.

Saurari rahoton Ibrahim Isa kan ziyarar ta Shugaba Buhari

Buhari 'ya ci taliyar karshe'

Wasu daga cikin ra'ayoyinku

Jama'a na cigaba da bayyana ra'ayoyinsu kan ziyarar aiki ta kwana biyu da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke yi a jihar Kano.

Ga wasu daga ciki da muka tsakuro daga shafinmu na BBC Hausa Facebook:

Muhammad Ishaq: Wallahi shi kansa Buhari ya san cewa jama'a sun chanja masa, ka ga wai shi ne ya zo Kano ba kowa sai wadanda aka ba kudi.

Muazzam Bello Malamee: Lallai Buhari ya ci taliyar karshe, sai karya a radio wai an yi cikar kwari... Yunwa duk ta cika wa mutane ciki. Wa zai fita tararsa?

Sadeeq Nabageh: Kanawa kar ku ba mu kunya, ku fito don Allah, gobe a ba da mamaki, a cika a batse, a nuna tumbin giwar.

Abdulrasheed Gabas Cin Adarawa: Muna yi wa Shugaba Buhari barka da zuwa Birnin Kano. Shugaba Buhari muna maka fatan alheri Allah ya sa a yi taro lafiya a kare lafiya.

Jama'a a Kano na tarbar Shugaba Muhammadu Buhari
BBC
Duk da cewa wasu Kanawa na sukar Gwamnatin Buhari, wasu sun fito domin tarbarsa

An tsaurara matakan tsaro

Ziyarar Shugaba Buhari a Kano
BBC

Bayanai daga birnin Kano da kewaye sun ce an tsaurara matakan tsaro domin ziyarar da Shugaba Buhari ke yi a jihar.

Dubban jama'a ne dai suka fito domin yi wa shugaban marhabin zuwa jihar, wacce ita ce ta fi kowacce bashi kuri'u a zaben shekara ta 2015.

Sai dai jama'a da dama sun dawo daga rakiyar gwamnatinsa suna masu cewa ya kasa aiwatar da alkawuran da ya dauka.

Wasu Kanawa a shafukan sada zumunta sun yi zargin cewa an tsaurara matakan tsaron ne domin ana hasashen cewa wasu masu adawa za su nuna rashin jin dadinsu kan ziyarar tasa.

.
.

Shugaba Buhari ya isa gidan yarin Kurmawa

Shugaba Buhari ya ziyarci gidan yarin Kurmawa domin gane wa idonsa yadda ake zama a gidajen yarin Najeriya, in ji mai taimaka masa kan kafofin sa da zumunta, Bashir Ahmad.

View more on twitter

Ra'ayi:

Aliyu Dahiru Aliyu ya ce "gaskiya dai ya cika abin kunya a ce wai mai gaskiya zai zo Kano amma duk an bi an tsorata don ka da a yi masa ihu! Yanzu a ce yadda ake son Mai gaskiya a Kano amma duk ya tsorata saboda shi ya san bai yi abin kirki a garin ba. Sarkin Kano da gwamnatin Kano da hukumar 'yan sanda da sauran jami'an tsaro duk sun hadu suna fadakarwa a kan zuwan mai gaskiya don ka da a yi masa bore! To idan mai gaskiya na tsoron shigowa Kano to ina ga sauran jihohi?!

Shi ma Sheriff Almuhajir mai yawan bayyana ra'ayinsa a shafin Facebook ya rubuta cewa: Da Buhari wani garin zai je ba Kano ba, da yanzu sun ishi mutane da korafin an yi mutuwa a Numan bai je ba. An yi walkiya.

Aliyu Dahiru Facebook
Aliyu Dahiru Facebook
Sheriff Almuhajir Facebook
Sheriff Almuhajir Facebook
Faceebook
Faceebook

'Na gamsu da tarbar da Kanawa suka yi min'

Shugaba Muhamamdu Buhari ya ce ya gamsu da tarbar da al'ummar Kano suka yi masa a lokacin da ya isa birnin domin fara ziyarar aiki ta kwana biyu a jihar.

"Duk da cewa ban yi tsammanin wani abu kasa da haka ba, amma na yi matukar mamakin yadda Kanawa suka tarbe ni a safiyar nan," kamar yadda wani jami'insa ya rawaito shi yana cewa a lokacin da ya ziyarci fadar sarkin Kanon.

View more on twitter

Mutane na dakon Shugaba Buhari..

Mutane na dakon Shugaba Buhari a titin gidan zoo inda zai bude asibitin yara.

Dakon Buhari
BBC

Kalli yadda Buhari ya sauka

Kalli yadda Buhari ya sauka

View more on twitter

Kalli jerin gwanon motocin Buhari

Wani mai amfani da shafin Twitter ya wallafa yadda mutane suka tarbi jerin gwanon motocin Buhari.

View more on twitter

Daga wajen fadar sarkin Kano

Magoya bayan Shuga Muhammadu Buhari daga wajen fadar sarkin Kano suna jira yayin da jami'an tsaro ke aikinsu.

Magoya bayan Buhari a waje
BBC

Ya isa fadar Sarkin Kano

Shugaba Muhammadu Buhari ya isa fadar sarkin kano domin kai ziyarar ban girma.

Buhari da Ganduje da Sarkin Kano a tsakiya
BBC
Buhari da Ganduje da Sarkin Kano a tsakiya

Magoya bayan APC

Wasu sanye da kaya kalar tutar APC na maraba da zuwan Buhari

Magoya bayan jam'iyyar shugaban

Magoya bayan jam'iyyar sun yi anko.

Anko
BBC

Sharhi

A karon farko cikin shekaru biyu Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya na ziyara a Kano. 'Yan siyasa a jihar sun jima suna korafi kan lokacin da shugaban ya shafe bai kai ziyara jihar ba, wacce take 'cibiyar siyasar sa'.

Kano ce ta bawa Buhari kuri'a mafi yawa a lokacin zaben shugaban kasa na 2015. To sai dai magoya bayan Buharin na cewa ba su damu da rashin ziyarar ba, tun da dai akwai kauna tsakaninsu da shugaban.

A bangare daya kuma wasu na ganin cewa Shugaba Buhari ya kai ziyarar ne a yanzu kasancewar lokacin zabe ya fara karatowa.

To amma wasu na hannun daman Buharin na cewa Shugaban ya jinkirta ziyarar ne har sai an samar da manyan ayyukan da zai kaddamar idan ya je ziyarar.

A ziyarar ta kwanaki biyu, Shugaba Buhari zai bude wasu manyan asibitoci biyu a birnin da gwamnatin Ganduje ta karasa.

To sai dai masu suka na cewa babu wani aikin gwamnatin tarayya da za a nuna a jihar a cikin shekaru biyu da Buhari ya hau mulki.

An dai tsarara matakan tsaro a jihar, inda aka jibge yan sanda 8,000 bayan ga jami'an tsaron farin kaya da sojoji da ke sintiri a birnin. Haka kuma akwai jirage masu saukar aungulu guda biyu da ke shawagi a birin.

Muhammadu Buhari Hospital
BBC

A karon farko

Buhari ya je Kanon ne a karon farko tun bayan da ya hau shugabancin kasar.

Buhari ya isa Kano

Da misalin karfe 10.30 na safe Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka a filin jhirgin sama na Malam Aminu Kano, inda gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da Sarki Muhammadu Sanusi na II suka tarbe shi,

Ku kasance tare da wannan shafin domin samun labarai da sharhi kan ziyarar da Shugaba Muhammadu Buhari yake a Kano.