Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Mourinho ya tsawaita kwantiraginsa da Man Utd
  2. Benitez da Conte da kuma Klopp za su yi taron manema labarai

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

'Dole Arsenal ta zarce tarihi'

Kungiyar Borussia Dortmund da ke gasar Bundesliga ta shaida wa Arsenal cewa sai ta zarce tarihin da ta kafa na sayen dan wasa kan kudi fam miliyan 52 kafin ta sayi Aubameyang, in ji Star.

Aubameyang
Getty Images
Aubameyang

Chelsea na neman Giroud?

Giroud
Getty Images

Jaridar The Mirror tana bayar da rahoton cewa neman dan wasan gaban da Chelsea ke yi ya kai ta kofar Arsenal, kuma za ta iya neman Olivier Giroud.

A baya dai an alakanta shi da tafiya Borussia Dortmund.

Coutinho ya fara taka wa Brca leda

Coutinho
Getty Images
Coutinho

Tsohon madugun 'yan wasan Liverpool, Philippe Coutinho, ya fara taka wa Barcelona leda yayin da kungiyar ta doke Espanyol a kan hanyarta ta zuwa matakin dab da na karshe a gasar kofin Spaniya a daren Alhamis.

Ya shiga wasan minti 22 da fara wasa kuma da ya taimaka a ci kwallo daya da ba don Pau Lopez ba.

Lionel Messi ya ci kwallon Barca ta 4,000 a Nou Camp a wannan nasarar.

Arsenal da Borussia sun kasa cimma matsaya

Aubameyang
Getty Images
Aubameyang

An kasa cimma matsaya tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da Borussia Dortmund game da cinikin dan kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 28, in ji Kicker.

PSG ta gindaya wa Neymar sharadi

Neymar
Getty Images
Neymar

Kungiyar kwallon kafa ta Paris St-Germain ta gindaya wa Neymar dan Brazil ,mai shekara 25, sharadin taka rawar gani a gasar zakarun Turai kafin kungiyar ta kyale shi ya koma Real Madrid, kamar yaddaGoal ta ambato shugaban kulob din na Faransa Nasser Al-Khelaifi yana cewa.