Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. An bai wa Buhari lambar yabo ta 'boge'
  2. Yadda 'yan birni ke farfado da bukukuwan kauye
  3. Shin abin da ya faru a fim din Taqaddama ya faru da gaske?
  4. An ba da umarnin sake bude gidan rediyo a Nijar
  5. 'Ruwan kudi' a bikin 'yar gidan Dangote
  6. An jana'izar sojoji 11 a Kaduna
  7. An hana El-Rufai karbar bashin $350m

Rahoto kai-tsaye

Daga Nasidi Adamu Yahya

time_stated_uk

A nan muka zo karshen labarai da rahotannin da muke kawo muku kai-tsaye a wannan dandali. Da fatan kun ji dadin kasancewa tare da mu. Sai ku biyo mu a makon gobe inda za mu ci gaba da kawo muku wadannan labarai. Amma za ku iya ci gaba da bibiyar shafinmu na intanet da kuma shafukanmu na sada zumunta da muhawara domin samun labaran da suka shafi rayuwarku. Sunana Nasidi Adamu Yahaya nake yi muku fatan alheri.

An kashe fiye da mutum 60 a Zamfara

Mazauna wani kauye da ke jihar Zamfara a arewacin Najeriya sun ce barayin shanu sun kashe sama da mutum 60 a kwanaki biyu da suka wuce.

A cewarsu mutum 15 aka kashe a harin farko.

Sauran kuma an kashe su ne a wasu jerin hare-hare da barayin suka kai lokacin da ake jana'izar mutanen farko da suka hallaka, inda mutum uku kawai ne suka rayu.

A ziyarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya kai makon da ya gabata a jihar, ya umarci jami'an tsaro su kawo karshen miyagun laifuka da ake aikatawa a jihar.

Adadin mutane da suka mutu ya karu
ZAMFARA GOVERNMENT

Sanatocin Najeriya sun hana El-Rufai karbar bashin $350m

Majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da bukatar da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya gabatar mata ta cin bashin $350m daga Bankin Duniya.

'Yan majalisar sun dauki matakin ne bayan wani kwamiti da Sanata Shehu Sani ke jagoranta ya gabatar musu rahoto kan batun.

A shekarar da ta wuce ne gwamnatin jihar Kaduna ta mika bukatar neman bashin domin gudanar da ayyukan 'ci gaban kasa'

'Yan majalisarsun yi watsi da bukatar karbo bashin ne "saboda Kaduna ita ce jiha ta biyu da ta fi yawan bashin da ake bin ta".

Kaduna ce jiha ta biyu da ta fi karbar bashi, in ji sanatocin.
KADUNA STATE GOVERNMENT

An yi jana'izar sojoji 11 a Kaduna

An yi jana'izar sojojin nan 11 da aka hallaka a yankin Birnin gwari na jihar Kaduna a ranar Alhamis, wadanda aka kashe yayin da suke aikin kakkabe masu fashi da makami da sace-sacen shanu da jama'a a yankin a aikin nan na soji na rawar Mage wato Akpan Apatuma.

A ranar 20 ga watan nan ne dai aka halaka sojojin 11, ana kuma zaton 'yan ta'adda' magoya bayan Buharin Daji ne suka kai musu hari.

Ga rahoton wakilinmu Nurah Mohd Ringim daga Kaduna:

Rahoton Nura Ringim kan jana'izar sojoji a Kaduna
'Yan bindiga ne suka kashe sojojin
Getty Images

Abdel Fatah-al Sisi ya sake lashe zaben Masar

Kafafen watsa labaran Masar sun ce Abdel Fatah-al Sisi ya sake lashe zaben kasar a wani wa'adi na biyu, inda zuwa yanzu ya samu sama da kashi 90 na kuri'un da aka kada.

Tun kafin wannan zabe aka yanke hukuncin Al-sisi zai samu nasara la'akari da cewa mutum guda da ke kalubalantarsa ba wani sananne ba ne.

Abin da da aka fi mayar da hankali akai shi ne yawan mutanen da suka fito jefa kuri'a.

Mahukuntan kasar sun yi amfani da duk wata dabarar tabbatar da cewa mutane sun fita rumfunar zabe.

Kafafen watsa labaran kasar sun ce sama da mutum miliyan 23 cikin 60 da suka yi rajista sun jefa kuri'a a zaben da aka kammala jiya labara.

Wadanan alkaluma ba sune na karshe ba, sai dai sun yi kasa da adadin mutanen da suka kada kuri'a a zaben kasar na baya.

Da ma an yi tsammani shi ne zai lashe zaben
AFP

An rufe hanyoyin Lagos 'saboda Buhari'

Wadannan hotunan da aka dauka a wasu layukan unguwar Victoria Island da ke birnin Lagos ne lokacin ziyarar da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya kai ta kwana biyu.

An hana mutane bin hanyoyin lamarin da ya kawo cunkoso a wasu yankunan.

Masu amfani da shafukan sada zumunta a jihar na korafi kan hakan.

An rufe hanyoyi a Lagos
AFP
An rufe hanyoyi a Lagos
AFP
An rufe hanyoyi a Lagos
AFP

Yadda 'yan birni ke farfado da bukukuwan kauye

A kullum jama'a suna fito da nau'ikan bukukuwan musamman a lokacin bikin aure.

Ranar Kauye ko 'Kauye Day' na daga irin bukukuwan da suke kara samun farin jini musamman wajen mata iyayen biki a wasu yankunan arewacin Najeriya.

Ga dai daya daga cikin irin wadannan shagulgula a cikin bidiyon da ke sama.

Yadda 'yan birne ke farfado da bukukuwan kauye

'Kudin da ake bai wa sanatoci ya sabawa doka'

Hukumar samar da kudin shiga da rarraba tattalin arzikin kasa ta Najeriya RMFA, ta ce yawan albashi da alawu-alawus din da ake bai wa ko wanne sanatan kasar duk wata a hukumance naira miliyan daya ne.

A wata sanarwa da hukumar ta aike wa manema labarai ta kara da cewa, naira miliyan 13.5 din da majalisar dokokin ke bai wa ko wanne sanata ta sabawa doka.

Sanata Shehu Sani ne ya fara fallasa wannan magana mako uku da suka gabata, kan yawan kudaden da ake ba su duk wata, al'amarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kasar.

Sanarwar ta ce, babu kumbiya-kumbiya a dokar albashi da alawus-alawus ta ma'aikatan gwamnati, don haka Majalisar Dokokin cewa kawai za ta iya bayanin yadda aka yi sanatoci ke karbar naira miliyan 13.5 duk wata.

albashin 'yan majalisa
BBC

An rufe asusun bankunan Switzerland saboda cin hanci a Najeriya

Ofishin Antoni Janar na Switzerland ya rufe wasu asusun bankunan kasar saboda samunsu da alaka da batun cin hanci da rashawa a Najeriya.

Ana sa ran za a yi shari'ar wasu manyan jami'an kamfanonin man Shell da Eni a birnin Milan na kasar Italiya a watan Mayu.

Hukumomin Switzerland sun kwace wasu kadarori sannan suka bayar da bayanai ga hukumomin Italiya bayan babban mai shigar da kara na Milan ya bukaci hakan, in ji ofishin Antoni Janar na Switzerland.

Kotunan Najeriya da Italiya sun zargi jami'an kamfanonin da laifin bayar da cin hanci domin su samu lasisin rijiyyoyin mai a Najeriya.

Kotunan Najeriya da Italiya sun zargi jami'an kamfanonin
PA

An kai harin kan mayakan Chadi

Rundunar sojin fitaccen dan kasar Libyar nan Khalifa Haftar ta ce jiragen yakinta sun kai hari kan 'yan tawayen Chadi a hamadar da ke kudancin kasar a karshen mako.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce harin ya nufi wuraren binciken ababen hawa da ke da nisan kilomita 400 daga Sebha, da kuma yankunan da ke lardin Terbu, in ji wani jami'i da ke aiki da rundunar da ake kira Libyan National Army (LNA), wacce Haftar ke jagoranta.

Jami'in ya kara da cewa "an kai harin ne domin tabbatar da tsaro a kudancin kasar."

Wata kungiyar masu dauke da makamai ta Chadi, the Military Command Council for the Salvation of the Republic (CCMSR), ta ce jiragen Haftar sun kai mata hari.

Mai magana da yawun CCMSR da ke gudun hijira a kasashen waje, Kingabe Ogouzeimi de Tapol, ya ce babu wanda ya mutu sakamakon harin.

Harin bai kashe kowa ba
Getty Images

An yi 'ruwan kudi' a auren 'yar gidan Dangote

Da alama babu abin da ba a yi ba lokacin auren 'yar gidan Alhaji Aliko Dangote, mutumin da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, a karshen makon jiya.

Fitaccen attajirin nan mai kamfanin Microsoft Bill Gates da shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo na cikin manyan bakin da suka halarci bikin Fatima Dangote da Jamil Abubakar, sannan fitaccne mawakin nan Davido ya rera waka lokacin bikin.

Jaridar Pulse Nigeria ta ruwaito cewa an bai wa kowanne mutum da ya halarci bikin kyautar agogon kece rani na Rolex.

Fitaccen mai tsara tufafin bikin nan Jeremiah Ogbodo, wanda aka fi sani da SwankyJerry, ya wallafa wani sako a shafin sada zumunta inda ya ce an yi masa babbar kyauta saboda tsara tufafin amarya da angon da ya yi - yana mai cewa kudin da aka ba shi sun "ishe ni na yi gogayya da takwarorina na Hollywood".

Sai dai bai bayyana takamaimai abin da aka ba shi ba, yana mai cewa "idan na fadi abin da aka biya ni mutane za su ce ina zuzutawa".

View more on instagram
Jamil couldn't take his eyes or hands off his bride, and I mean, it's not hard to see why. 😉 #famil2018
Jamil couldn't take his eyes or hands off his bride, and I mean, it's not hard to see why. 😉 #famil2018
Jamil couldn't take his eyes or hands off his bride, and I mean, it's not hard to see why. 😉 #famil2018
Jamil couldn't take his eyes or hands off his bride, and I mean, it's not hard to see why. 😉 #famil2018

Jamil couldn't take his eyes or hands off his bride, and I mean, it's not hard to see why. 😉 #famil2018

Kungiyar lauyoyin Lagos na zanga-zanga

Kungiyar lauyoyin Najeriya reshen jihar Lagos ta bayyana bijirewarta ga matakin da majalisar dokokin jihar ta dauka na amincewa da kudurin dokar mallakar kasa.

Kudurin dokar ya ba da dama ga gwamnati ta yi kari kan harajin da take karba daga masu gidaje da filaye a jihar.

Kungiyar lauyoyin tana amfani da ziyarar da shugaban kasar Muhammadu Buhari ke yi a jihar domin matsa lamba a janye dokar.

Kungiyar ta soki Gwamna Ambode
TWITTER/Ambode
Kungiyar ta soki Gwamna Ambode

Buhari yana ziyarar aiki a Lagos

Shugaban Najeriya ya tafi jihar Lagos da ke kudu maso yammacin kasar inda zai yi ziyarar kwana biyu.

Fadar shugaban kasar ta ce shugaban kasar zai kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta gudanar sannan ya halarci taron laccar da ake kira Bola Tinubu’s Colloquium

Sai dai masu amfani da shafukan sada zumunta suna sukar gwamnati kan yadda aka rufe manyan hanyoyin da mutane ke bi sakamakon zuwan shugaban kasar, kamar yadda wani fitaccen mai harshi a shafin Twitter, Joshua Japeth Omojuwa ya ce.

President @MBuhari arrives Lagos State for a 2-day official visit. In Lagos he will commission some projects and at… twitter.com/i/web/status/9…

The President visiting any state shouldn’t be at the inconvenience of citizens. And were that to be so, it ought to… twitter.com/i/web/status/9…

Buhari zai kaddamar da ayyuka
Twitter/Ambode

An bayyana sunayen sanatocin da ke goyon bayan Buhari

An fitar da sunayen sanatocin da ke goyon bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a daidai lokacin da majalisar dattawan kasar ke muhawara domin kwace ikon da yake da shi na yin gyara a kan dokokin zabe na shekarar 2010.

Batun gyara dokokin zaben da zummar fara zaben 'yan majalisar dokoki sannan a kammala da zaben shugaban kasar ya raba kan 'yan majalisar. Shugaban ya ki amincewa da gyaran da 'yan majalisar suka yi wa dokar.

Jaridar DailyTrust ta ruwaito cewa bangaren da tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu ke jagoranta na goyon bayan matsayin shugaban kasar, yayin da bangare daya ke goyon bayan matakin da shugabancin majalisar karkashin Sanata Bukola Saraki ya dauka. Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa masu goyon bayan Shugaba Buhari sun kai 42.

Cikinsu har da Ali Ndume, Ahmad Lawan, Jibrin Barau, Ovie Oma- Agege, Abdullahi Adamu, Abu Ibrahim and Tayo Alasoadura.

Gyaran dokar zaben ya jawo ce-ce-ku-ce
Nigeria Senate Facebook

An kama 'mayakan Boko Haram'

Rudunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kama wasu mayakan kungiyar Boko Haram uku a maboyarsu da ke Ngurore.

Sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na twiter ta ce ranar 28 ga watan Maris rundunar LAFIYA DOLE ta kama Adam Yagga, Musa Kamsulum da Abba Djidoum dukkansu 'yan kauyen Darajimal da ke karamar hukumar Bama da ke jihar Borno, bayan an tsegunta mata inda suka boye.

OPERATION LAFIA DOLE: TROOPS ARREST 3 BOKO HARAM TERRORISTS  bit.ly/2GTJ2yd

OPERATION LAFIA DOLE: TROOPS ARREST 3 BOKO HARAM TERRORISTS bit.ly/2GTJ2yd

Ba zan koma Real Madrid ba — Marcos Alonso

Marcos Alonso ya ce ba zai koma Real Madrid da taka-leda ba, idan an kammala kakar bana, zai ci gaba da zamansa a Chelsea.

Alonso mai tsaron baya ya koma Stamford Bridge daga Real Madrid a shekarar 2016.

Dan kwallon mai shekara 27, ya buga wa Spaniya wasan sada zumunta da ta shararawa Argentina kwallo a ranar Talata.

Wasu rahotanni ne ke cewa Alonso zai koma Santiago Bernabeu da murza-leda idan an kare kakar wasannin ta bana.

Alonso ya ce ya buga wa Real Madrid wasan farko a kakar 2009/10 karkashin koci Manuel Pellegrini, sannan ya samu damar buga gasar Premier, zai kuma ci gaba da zamansa a Stamford Bridge.

Marcos Alonso ya ce zai yi zamansa a Stamford Bridge
Getty Images

An ba da umarnin sake bude gidan rediyo a Nijar

Wata kotu a Jamhuriyar Nijar ta bai wa hukumomin kasar umarnin sake bude gidan rediyo da talabijin da suka rufe a karshen makon jiya.

An rufe gidan rediyo da talabijin din ne saboda ya yada "sakonni da ka iya tayar da husuma" lokacin da ake gudanar da zanga-zangar da ta rikide ta koma tarzoma.

Alkalin kotun ya ce bai dace ba da aka rufe gidan rediyon mai suna Labari radio and television station sanna ya ba da umarni a janye jami'an tsaron da aka jibge a kofar shiga gidan rediyon.

Alkali ya soki hukumomin Nijar
Getty Images
Alkali ya soki hukumomin Nijar

Shin abin da ya faru a fim din Taqaddama ya faru da gaske?

Sannu a hankali masu fina-finan Hausa sun fara daukar hanyar inganta irin fina-finan da suke yi ta hanyar kiran masana su kalli fim su bayar da shawarar yadda za a gyara kafin ya je ga masu kallo.

Alhaji Shehes shi ne ya shirya fim din, sannan Ali Gumzak ya bayar da umarni.

An kiyasta cewa an kashe kimanin Naira miliyan bakwai a fim din na Takaddama, sabanin yadda ake kashe abin da bai haura Naira miliyan biyu ba a sauran fina-finai.

Nazarin fim din takaddama

An bai wa Buhari lambar yabo ta 'boge'

Cibiyar The King Center, wacce ke adana tarihin fitaccen bakar fatar nan na Amurka, marigayi Martin Luther, ta nesanta kanta daga lambar yabon da aka bai wa Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya.

Ranar 26 ga watan Maris ne wasu da aka ce iyalin Martin Luther ne suka ziyarci fadar shugaban Najeriya tare da rakiyar mai ba shi shawara kan harkokin 'yan kasar mazauna kasashen waje, Abike Dabiri, inda suka ba shi lambar yabon da ake kira 1st Black History Month National Black Excellence and Exceptional African Leadership Award 2018, saboda jajircewarsa wurin mulki na gari.

Sai dai a wani sako da cibiyar ta wallafa a shafinta na Twitter ranar 28 ga watan Maris ta ce "ba cibiyar The King Center ce ta bai wa Shugaba Buhari lambar yabo ba, kuma ba 'ya'yan #MLK da #CorettaScottKing suka ba shi ba."

Fadar shugaban kasa ta shaida wa BBC cewa lambar yabon ba ta boge ba ce kamar yadda wasu ke zata. A cewarta, nan gaba kadan za ta fitar da sanarwa domin yin karin haske kan batun.

Wannan batu dai ya jawo zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta, inda wasu ke caccakar shugaban kasar "saboda bai wa kasar kunya a irin karairayin da take yi da zummar boye gazawarta wurin gudanar da mulki".

President @MBuhari today at the State House received Martin Luther King Jnr’s family. He was also conferred with th… twitter.com/i/web/status/9…

The award given to President Buhari of Nigeria was not given by The King Center, at the request of The King Center… twitter.com/i/web/status/9…

Masu bibiyar wannan shafi muna yi muku barka da sake saduwa a shirinmu na labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a kasashen Najeriya da Nijar da Ghana da Kamaru da Chadi. Sunana Nasidi Adamu Yahaya kuma ni ne zan gabatar muku da shirin.