Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Gasar Premier wasannin mako na 11
 2. Wasannin La Liga, Bundesliga da Serie A
 3. Gasar kwallon tennis ta Faris
 4. Wasannin damben gargajiya
 5. Za ku iya bayar da gudunmawarku

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

Nan muka kawo karshen shirin

Sai ku sake tarawa a ranar Asabar

Man City 1-0 Middlesbrough

Sergio Aguero

Hertha ta koma matsayi na uku a teburin Bundesliga

Hertha 3 da Borussia Monchengladbach 0

Tsohon dan wasan Chelsea, Salomon Kalou, ya ci kwallaye uku a karawar da Hertha Berling ta doke Borussia Monchengladbach da ci 3-0 a gasar Bundesliga da suka yi a ranar Asabar. 

Da wannan sakamakon Hertha ta koma mataki na uku a kan teburin gasar ta Jamus, bayan da ta yi wasanni 10.  

Bundesliga
Getty Images

An fitar da Konta daga gasar China

Elina Svitolina ta kai wasan karshe a gasar kwararru da ake yi Zhuhai ta China.

Svitolina ta samu nasarar doke Johanna Konta ne a ranar Asabar da ci 2-6 6-1 6-4.   

Tennis
Getty Images

Burnley 2-0 Crystal Palace

Johann Berg Gudmundsson

Bournemouth 1-0 Sunderland

Dan Gosling (a minti na11)

Labarai da dumi-dumiMurray ya dare mataki na daya a Tennis

Andy Murray ya hau mataki na daya a jerin wadanda suke kan gaba a iya kwallon tennis a duniya, bayan da Milos Raonic ya janye daga wasan da ya kamata su fafata a ranar Asabar sakamakon raunin da ya yi.

Murray ya karbi matakin ne a wajen Novak Djokovic.

Manchester City da Middlesbrough

'Yan wasan da za a fara buga tamaula da su

City 11: Bravo, Zabaleta, Stones, Kolarov, Clichy, Fernandinho, Gundogan, Silva, De Bruyne, Navas, Aguero

Masu jiran kar-ta-kwana: Caballero, Kompany, Maffeo, Garcia, Nolito, Iheanacho. Sane

EPL
BBC

Boro 11: Valdes, Barragan, Chambers, Gibson, Friend, Traore, De Roon, Clayton, Forshaw, Downing, Negredo 

Masu jiran kar-ta-kwana: Da Silva, Bernardo, Leadbitter, Fischer, Guzan, Stuani, Nugent

EPL
BBC

Sunan kofin League Cup na Ingila zai koma Carabao

Manchester City ce ta lashe kofin bara

Kofin League Cup na kawllon kafa na Ingila (EFL), zai samu sabon suna daga kaka mai zuwa ta 2017-18, inda za a rika kiransa kofin Carabao, a karkashin wata yarjejeniya da aka kulla ta daukar nauyin gasar.

Hukumar gasar cin kofin ta kulla yarjejeniyar tsawon shekara uku a kan fam miliyan 18 da kamfanin lemon gwangwani na kara kuzari na kasar Thailand.

League Cup
Getty Images

West Ham United da Stoke City

An kai jami'an tsaro da dama filin wasa na West Ham United. West Ham za ta kara da Stoke City a gasar Premier wasan mako na 11. Ana ta samun yamutsi a filin wasan West Ham, na baya-bayan ne shi ne wanda kungiyar ta ci Chelsea 2-1 a League. Bayan da aka tashi daga wasan aka yi yamutsi. 

EPL
Getty Images
EPL
Getty Images

Ibrahimovich na kanfar kwallaye

Bayan da Zlatan Ibrahimovich ya dunga cin kwallo a wasanni hudu da ya fara buga wa Manchester United a jere, yanzu yana fama da kanfar cin su a raga. 

Dan wasan ya ci kwallo daya tilo a wasanni 11 da ya yi wa United a yanzu. 

Ga wasannin da ya ci wa United kwallaye

 • Leicester 1 - 2 Man Utd ya ci daya 
 • Bournemouth 1 - 3 Man Utd ya ci daya 
 • Man Utd 2 - 0 Southampton ya ci biyu 
 • Man Utd 1 - 2 Man City ya ci daya 
 • Man Utd 1 - 0 Zorya ya ci daya  
Premier
Getty Images

Za a buga wasan karshe a Federation Cup na Nigeria

Ranar Lahadi a Legas, Nigeria

Za a buga wasan karshe na Federation Cup a wasan maza tsakanin IfeanyiUbah da Nasarawa United. 

A wasan mata kuwa Bayelsa Queens da Rivers Angel ne za su kece raini. 

Za a yi dukkan wasannin ne a ranar Lahadi da yammaci a jihar Legas a Nigeria.

Gudunmawarku a BBC Hausa Facebook

Musa Usman Dutsinma: Middelesbroug kada ku bamu kunya, mu 'yan adawa so muke Man City ta kwashi kashinta a hannu, up Arsenal

Mubarak Sani Kankia: A karawar da za a yi tsakanin Manchester City da Middlesbrough Allah ya sa a tashi babu ci. 

Sa'idu Gagiyo Katamma: Wasa tsakanin Manchester City da Midlesbrough dai ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.

Konta ta kai wasan daf da karshe a China

Johanna Konta ta kai wasan daf da karshe a gasar kwararru da ake yi a Zhuhai, China, bayan da ta doke Caroline Garcia da ci 6-2 da 6-2. 

Konta mai shekara 25 za ta fafata ne da Elina Svitolina. Daya wasa na biyu shi ne tsakanin Petra Kvitova da Zhang Shuai.         

Tennis
Rex Features

Sakamakon wasannin damben jihar Kano

Manyan wasanni hudu aka yi a ranar Juma'a

Ali Kanin Bello daga Arewa ya yi nasarar doke Garkuwan Mai Caji daga Kudu a turmin farko. 

Bahagon Bahagon Sanin Kurna daga Arewa ya buge Dan Ali Shagon Bata Isarka daga Kudu. 

Audu Bahago Guramada da Shagon Mai Caji daga Kudu aka yi canjaras.

Dogon Kyallu Guramada da Bahagon Isya Na Wukari suka tashi wasa babu kisa. 

Damben Gargajiya
Getty Images

Murray na daf da hawa mataki na daya a Tennis

 Da zarar Andy Murray ya ci wasa daya a gasar kwallon tennis ta kwararru da ake yi a Paris zai dare matsayi na daya a jerin wadanda suke kan gaba a iya wasan a duniya. 

Wanda yake mataki na daya Novak Djokovic ya sha kashi a hannun Marin Cilic da ci 6-4 7-6 (7-2) a wasan daf da na kusa da na karshe da suka yi a ranar Jumma'a. 

A kuma ranar ce Murray ya doke Tomas Berdych 7-6 (11-9) 7-5, zai kuma fafata da Milos Raonic a ranar Asabar a wasan daf da karshe da karfe 4:30 na yamma agogon Nigeria. 15:30  

Tennis
Getty Images

Wasu damben da aka yi a farkon watan Oktoba a Abuja

Damben gargajiya da aka yi a Dei-Dei da ke Abuja, Nigeria

Wasu damben gargajiya da aka yi a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria

Bundesliga wasannin mako na 10

 • Freiburg da VfL Wolfsburg          
 • Hamburger da Borussia Dortmund          
 • Bayer 04 Leverkusen da SV Darmstadt  
 • Bayern Munich da Hoffenheim
 • FC Ingolstadt 04 da FC Augsburg
 • Eintracht Frankfurt da FC Koln 

Sakamakon gasar damben mota ta Minna

Shagon Sama'ila daga Kudu ya kai wasan zagayen gaba, bayan da Dogon Gobiraje Guramada bai halarci filin wasa ba. 

Shagon Dirago daga Arewa ya samu nasara ne a kan Shagon Audu Gurumada, bayan da suka yi turmi uku babu kisa, aka yi kuri'a Shagon Audu ya yi nasara. 

Da yammacin Asabar za a raba jadawalin wasannin zagaye na biyu. Ana yin wasannin gasar damben da za a ci mota ta matasa a filin wasa na U.K Bello Art and Theater da ke Minna jihar Niger, Nigeria.    

Damben gargajiya
BBC

Gasar Serie A wasannin mako na 12

 • Torino da Cagliari Calcio
 • Napoli da Lazio 

An dakatar da Andrew daga buga wasanni 12

An dakatar da dan kwallon Rochdale, Calvin Andrew, daga buga wasannin 12, shi ne hukuncin da aka yanke wa dan wasa a gasar Ingila mafi tsawo. 

An samu Andew mai shekara 29, da laifin yi wa Peter Clarke na Oldham Gula a lokacin da suka fafata. 

An taba dakatar da Luis Suarez daga buga wasanni 10, bayan da aka same shi da laifin cizon Kirk Broadfoot na Rotherham.

Rochdale
Getty Images

Me ke faruwa da Manchester United ne?

Manchester United tana karo na biyu da ta kasa yin abin a zo a gani a gasar Premier, bayan buga wasanni 10 da maki 15.

Karon farko shi ne a kakar wasan 2014/15, bayan buga fafatawa 10 ta hada maki 13. A ranar Lahadi United za ta ziyarci Swansea a gasar Premier wasan mako na 11.

EPL
Getty Images

Gasar La Liga wasannin mako na 11

 • Granada da Deportivo La Coruna             
 • Real Sociedad da Atletico de Madrid      
 • Osasuna da Deportivo Alaves    
 • Las Palmas da SD Eibar

Toure ya bayar da kai bori ya hau

Manchester City da Middlesbrouhg

Dan wasan tsakiya na Manchester City Yaya Toure ya nemi gafarar kungiyar "saboda abubuwan da suka faru a baya".

Kocin City Pep Guardiola ya ce ba zai sanya Toure, mai shekara 33 a wasa ba, sai lokacin da wakilinsa Dimitri Seluk ya nemi gafara a kan sukar da ya yi masa saboda kin sanya dan kwallon a jerin 'yan wasan da ke buga gasar zakarun turai.

Wasa daya Toure ya buga wa City, baya cikin masu buga mata wasannin gasar cin kofin zakarun Turai.

Manchester City
AFP

Gasar Premier wasannin mako na 11

 • Manchester City da   Middlesbrough
 • West Ham United da  Stoke City FC     
 • Burnley FC  da  Crystal Palace FC             
 • Bournemouth FC  da  Sunderland        
 • Chelsea FC   da   Everton FC    

Sharhin gasar Premier

A shirinmu na sharhi da bayanai a gasar cin kofin Premier, za mu kawo muku daya daga cikin wasannin mako na 11 a karawar da za a yi tsakanin Manchester City da Middlesbrough. Za mu fara gabatar da shirin da karfe 3:30 na rana agogon Nigeria da Nijar. 

EPL
Getty Images

Barkanmu da saduwa a cikin shirin labaran wasanni kai tsaye