Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. An bayyana 'yan takarar gwarzon BBC na bana
 2. Nigeria 3 da Algeria 1
 3. Afirka ta Kudu 2 da Senegal 1
 4. Gasar kwallon tennis
 5. Wasan damben gargajiya
 6. Gudunmawarku

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

Nan muka kawo karshen shirin.

Za ku iya kada kuri'ar ku

'Yan takarar dan kwallon BBC na Afirka a 2016 

 • Sadio Mane
 • Riyad Mahrez
 • Andre Ayew
 • Pierre-Emerick Aubameyang
 • Yaya Toure

An fara yin zabe, za ku iya yin naku ta nan  

Click here to make your choice.

Yaya Toure

Mai shekara 33 ya ci kyauta ta biyu ta gwarzon dan kwallon kafa ta Afirka a bara, ko zai iya lashe ta uku? 

Koda yake ya dan samu sabani da kociyan Manchester City, Pep Guardiola, amma yanzu ana ganin komai ya wuce tun da ya bayar da hakuri. 

AFOTY
AP

Ku zabe ni - Toure

Gwarzon dan kwallon kafa na BBC a bana

Dangarama Yaya Toure

Sau biyu Yaya Toure yana zama Gwarzon Kwallon Kafar Afirka na BBC, kuma sau hudu yana lashe makamanciyarta ta Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF).

Don haka ganin sunansa a jerin wadanda aka ware bana ba abin mamaki ba ne.

Ko da yake sau 23 kacal ya buga wasa a 2016, saka sunansa a cikin jerin ya nuna irin matsayinsa a fagen kwallon kafa a Afirka.

Kuma duk da cewa wasannin da ya buga ba su da yawa, tasirinsa ba ya misaltuwa.

A watan Fabrairu ya daga wa Manchester City Kofin Gasar League ta Ingila - inda ya fasa raga da wani bugun fanariti mai muhimmanci wanda ya ba su damar cin Liverpool a wasan karshe.

Ku karanta cikakken bayani kan rawar da Toure yake takawa

Pierre-Emerick Aubameyang

Mai shekara 27, yana taka rawar gani a Borussia Dortmund tun lokacin da ya koma can a shekarar 2013.

Ya kuma ci wa kungiyar kwallaye 25 a kakar wasan 2015/16.

AFOTY
Rex Features

Andre Ayew

 Andre Ayew, wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa da BBC ta karrama a 2011, ya koma murza leda ga West Hama daga Swansea City kan kudi fam miliyan 20.5.

AFOTY
Getty Images

Ku zabe ni - Aubameyang

Gwarzon kwalon Afirka na BC a bana

 Dodon Raga Pierre Emerick-Aubameyang

Tun da ya soma buga kwallo a Borussia Dortmund, dan wasan gaba Pierre Emerick-Aubameyang na ci gaba da burge masoya kwallo.

Dan takarar na Zakaran Kwallon Kafar Afirka na BBC na 2016 na da shekaru 27, kuma ya taso ne a kasar Faransa. 

Yana cikin wadanda kungiyar kwallon kafar AC Milan ke nema, amma kuma har yanzu bai buga masu kwallo ba, bayan da ya je Dion na Faransa a matsayin aro.

A wani wasan sada zumunta wanda shi ne wasanshi na farko a shekarar 2008, lokacin yana da shekaru 18, ya burge manyan 'yan wasan da ke cikin tawagarsa.

Karanta cikakken bayani kan rawar da Aubameyang ke takawa

Ku zabe ni Gwarzon kwallon Afrika - Ayew

Na BBC a bana

Gwanin rike kwallo Andre Ayew

Dan kwallon tawagar Ghana, Andrew Ayew ya nuna cewa shi ba mutum ba ne wanda gwiwarsa za ta yi sanyi a duk lokacin da ya samu kansa a cikin mawuyacin hali.

A watan Janairu an tilasta wa Ayew, mai shekara 26, buga kwallo ba a wurin da ya saba taka leda ba, lokacin da sabon kociyan Swansea, Francisco Guidolin, ya karbi aiki bayan da aka sallami Garry Monk, Amma ya bai wa marada kunya.

Kwarewarsa da kwazon da yake nunawa da kwallayen da yake ci, sun nuna karara irin burin da yake son cimmawa, kuma sun taimaka wajen hana Swansea rikitowa daga Gasar Premier.

Ayew ya ci kwallo biyu daga cikinukun da suka doke Liverpool, wanda daga karshe aka tabbatar da cewar Swansea za ta ci gaba da zama a Gasar Premier bara.

Saboda haka ba a yi mamaki ba da ya lashe kyautar bakon dan kwallon da ya fi taka rawar-gani a Swansea bara.

Kalli shirin kai tsaye

Za ku iya kallon shirin da ake gabatarwa kai tsaye domin bayyana sunayen 'yan takarar gwarzon kwallon Afirka na BBC na 2016.

View more on facebook

Mahrez ya taka rawar-gani

 • Ya lashe gasar Premier ta Ingila
 • Shi aka zaba dan wasan da ya fi kowa a gasar
 • Yana cikin 'yan wasa 30 da ke takarar Ballon d'Or na Fifa

Ko zai iya lashe gasar BBC ta bana?

Ku zabe ni gwarzon kwallon Afirka - Riyad Mahrez

Mahrez
Getty Images

Dan kwallon Algeria da Leicester City Riyad Mahrez ya taka rawar gani a kakar bana.

"Za ka iya tunanin cewa maganadisu ne a kafarsa idan yana murza leda."

Wadannan su ne kalaman da Madjid, abokin dan wasan da ke takarar zama Zakaran Kwallon Kafar Afirka na BBC na 2016, Riyad Mahrez, ya yi wajen bayyana irin gogewar dan wasan.

Madjid, wanda abokin Mahrez ne tun suna kanana, ya kara da cewa "A da mukan yi fada da juna domin kawai mu tabbatar Riyad ya buga wa bangarenmu wasa."

Ya tuna lokacin da suke buga kwallo tare suna yara a garin Beni Snous da ke arewa maso yammacin Algeria.

Karanta cikakken bayani kan rawar da Mahrez ke takawa

Kamaru da Zambia su tashi wasa 1-1

Wasan shiga gasar cin kofin duniya

WCQ
Getty Images

Sadio Mane

Sadio Mane ya koma Liverpool kan kudi fam miliyan 34 a matsayin dan wasan da ya fi tsada daga Afirka. Mai shekara 24 ya ci kwallaye shida a wasanni 11 da ya buga wa Liverpool a bana.

Afoy
Rex Features

Ku zabe ni Sadio Mane

Gwarzon dan kwallon BBC a bana

Kakar wasanni ta bana ta yi kyau sosai ga dan wasan tawagar Senegal, Sadio Mane.

Hazikin dan wasan na gaba zai iya taka leda a ko wanne bangare na filin wasa - a gefe, ko a baya, ko a gaba - sannan an wayi gari ya shiga sahun 'yan wasan Gasar Premier da suka fi barazana ga ragar abokan hamayya, kuma daya daga cikin 'yan wasan Afirka da suka fi kwazo.

Gudun dan wasan, da iya rike kwallo, da saurin tunani, su kan jefa tsoro a zukatan abokan hamayyarsa sun kuma dasa kaunarsa a zukatan 'yan kallo sun kuma jawo masa yabo daga masharhanta.

Yana da dabaru ba iyaka ga shi kuma kaifi daya a bakin raga, inda yake iya karbar kwallo ya kuma samar da dama ga abokan wasanshi.

Mady Toure, wanda ya kafa cibiyar koyar da kwallon kafa ta Academie Generation Foot inda Mane ya fara daukar darasin kwallo, ya yi amanna cewa dan wasan komai-da-ruwanka ne.

Za mu fara gabatar da 'yan takara

Gwarzon dan kwallon BBC na bana

Hasashen da kuke yi a BBC Hausa Facebook

Tahir Imam Mahmoud: Mane,Iwuobi, Ihenacho,Yaya Toure. da kuma Ahmad Musa.

undefinedundefinedSani S Rafi: Ba shakka 'yan wasan zasu iya hadawa da irin su RIYAD MAHAREZ, PERRE-EMRIC AUBAMEYANG, AHMED MUSA, YAYA TOURE da kuma MIKEL OBI.  

Nigeria 3 da Algeria 1

Nigeria 2 Algeria 1

Nigeria ta sauya dan kwallo

Ahmed Musa ya canji Alex Iwobi

Gwarzon dan kwallon kafa na BBC na bana

Abedi Pele ne ya fara lashe kyautar dan kwallon kafar da BBC ta karrama a shekarar 1992, yayin da Yaya Toure ya ci kyautar bara. 

Shin wanene zai lashe kyautar bana? 

Daf muke da sanar da sunayen fitattun 'yan kwallon Afirka guda biyar da za ku zabi guda daya da ya fi yin fice a bana.  

Aforty
BBC

Nigeria 2 da Algeria 1

Nabil Bentaleb ne ya ci kwallon 

WCQ
Super Sports

Kamaru 1 da Zambia 1

Wasan shiga gasar kofin duniya sun tashi daga kwallo

Nigeria 2-0 Algeria

Algeria ta samu dama! Bentaleb ne ya buga kwallo ta yi waje. 

Gwarzon dan kwallon kafa na BBC na bana

Za a bayyana sunayen fitattun 'yan wasa biyar na Afirka

Da yammacin Asabar ne za a bayyana biyar daga cikin 'yan takarar Zakaran Kwallon Afirka na BBC na 2016, kuma a soma kada kuri'a.

Za a sanar da sunayensu a wani shiri na musamman kuma kai tsaye a tashoshin BBC World TV (talabijin) da BBC World Service (rediyo), wanda za a fara da misalin karfe 6:00 na yamma agogon GMT.

Masoya kwallon kafar Afirka a duniya za su iya kada kuri'unsu a shafin BBC ta daga karfe 6:50 na yamma agogon GMT.

Nigeria 2 vs Algeria 0

Miukel Obi ne ya ci kwallo na biyu a minti na 41

Nigeria 1 vs Algeria 0

Victor Moses ne ya ci kwallo a minti na 24

Nigeria 0 vs Algeria 0

'Yan wasan Nigeria: Akpeyi; Omeruo, Balogun, Troost-Ekong, Echiejile; Mikel (c), Onazi; Moses, Iwobi, Etebo; Iheanacho

Wasan shiga kofin duniya, Afirka

Nigeria da Algeria karfe 5:00 agogon Nigeria

Algeria ce ta ziyarci Nigeria a wasan shiga gasar cin kofin duniya da za su fafata a Uyo ta jihar Akwa Ibom ta Nigeria. 

Nigeria da Algeria sun kara a manyan wasanni sau 16, inda kowacce ta ci karawa shida-shida, kuma ta yi rashin nasara sau shida suka buga canjaras sau hudu.

Nigeria ta zura kwallaye 22 a ragar Algeria ita kuwa ta ci guda 20.   

WCQ
Getty Images

Murray ya ce Djokovic zai dawo wasa da karfinsa

Andy Murray wanda yake mataki na daya a jerin wadanda suke kan gaba wajen buga kwallon tennis a duniya, ya ce yana sa ran Novak Djokovic zai dawo buga wasan da karfinsa. 

A ranar Litinin ne Murray ya karbe matsayi na daya a wajen Djokovic wanda ake hasashen zai yi kokarin karbar gurbinsa a gasar kwararru da za a yi a mako mai zuwa. 

Ga yadda aka raba rukunin wasannin: 

Rukunin John McEnroe

1. Andy Murray (Birtaniya) 

3. Stan Wawrinka (Switzerland) 

5. Kei Nishikori (Japan) 

7. Marin Cilic (Croatia) 

 Rukunin Ivan Lendl

 2. Novak Djokovic (Serbia) 

4. Milos Raonic (Canada) 

6. Gael Monfils (France) 

8. Dominic Thiem (Australia)  

Tennis
Getty Images

Ya kamata a bai wa Southgate horar da Ingila - Rooney

Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Ingila, Wayne Rooney, ya ce ya kamata a bai wa Gareth Southgate aikin jan ragamar Ingila zuwa lokaci mai tsawo.

Southgate ya jagoranci Ingila lashe wasanni biyu daga guda uku da ya yi, inda a ranar Lahadi ya samu nasarar doke Scotland a wasan shiga gasar cin kofin duniya da ci 3-0.

Hakan ne ya sa Ingila ta dare mataki na daya a kan teburin rukuni na shida, bayan da ta yi wasanni hudu.

A kuma ranar Talata ne kociyan zai ja ragamar Ingila a wasan sada zumunta da za ta yi da Spaniya.

Southgate ya karbi aikin rikon kwarya na horar da tawagar Ingila, bayan da hukumar kwallon kafar kasar da Sam Allardyce suka raba gari.

England
Getty Images

Wasannin shiga gasar cin kofin duniya

Nahiyar Turai

 • Croatia  da Iceland          
 • Austria  da Ireland           
 • Georgia da Moldova      
 • Turkey  da Kosovo          
 • Ukraine da Finland         
 • Wales da Serbia               
 • Albania da Israel              
 • Liechtenstein da Italy    
 • Spain da Macedonia

WCQ
Getty Images

Gwarzon dan kwallon kafa na BBC na bana

Za a bayyana sunayen fitattun 'yan wasa biyar

Da yammacin Asabar ne za a bayyana biyar daga cikin 'yan takarar Zakaran Kwallon Afirka na BBC na 2016, kuma a soma kada kuri'a.

Za a sanar da sunayensu a wani shiri na musamman kuma kai tsaye a tashoshin BBC World TV (talabijin) da BBC World Service (rediyo), wanda za a fara da misalin karfe 6:00 na yamma agogon GMT.

Masoya kwallon kafar Afirka a duniya za su iya kada kuri'unsu a shafin BBC ta daga karfe 6:50 na yamma agogon GMT.

Za kuma a rufe zabe ranar Litinin 28 ga watan Nuwamba da karfe 6:00 na yamma agogon GMT, sannan a bayyana wanda ya yi nasara a shirye-shiryen BBC Focus on Africa na rediyo da talabijin ranar Litinin 12 ga watan Disamba, da misalin karfe 5:35 na yamma agogon GMT.

Wadansu tsofaffin kwararrun 'yan kwallon kafar Afirka da masana kwallon kafa zasu halarci shiri na musamman ranar Asabar din.

Peter Okwoche ne zai gabatar da shirin, wanda zai hada da hira da wanda daya daga cikin wadanda suka lashe gasar a baya, da tattaunawa a kan 'yan takarar bana da kuma waiwaye a kan harkar wasannin kwallon kafa a Afirka a bana.

Za kuma ku samu damar kallon abubuwan da suka gudana a bayan fage a shafukan intanet na Facebook na BBC Africa da BBC Sport da kuma shafin Instagram.

Ku biyo mu a shafin intanet na BBC Hausa domin samun bayanai kai-tsaye a yayin kaddamar da shirin.

Shafin BBC Sport mai zai rika aikewa da sakwannin Twitter kai-tsaye a BBC Africa da BBC Sport.

Masu bibiyar mu a kafofin sadarwa na zamani ma za su iya kasancewa da shirin ta hanyar maudu'i #BBCAFOTY.

Wasannin shiga gasar kofin duniya

Nahiyar Afirka

 • Uganda da Congo           
 • Afirka ta Kudu da Senegal           
 • Kamaru da Zambia          
 • Nigeria  da Algeria           
 • Cape Verde da Burkina Faso      
 • Mali da Gabon 
 • Morocco da Ivory Coast 

Barkanmu da saduwa a cikin shirin labaran wasanni kai tsaye