Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Bojan da Allen sun ci Leicester
 2. An bai wa Vardy jan kati a karawa da Stoke City
 3. Negredo ya ci Swansea kwallaye biyu
 4. An jima West Brom da Man United
 5. Crystal Palace 0-1 Chelsea

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

Nan muka kawo karshen shirin.

West Brom da Manchester United

'Yan wasan da za su taka-leda

Premier
BBC Sport

Sakamakon wasannin gasar Premier mako na 17

 • Crystal Palace 0 Chelsea 1
 •  Middlesbrough 3 Swansea 0 
 •  Stoke 2 Leicester 2 
 •  Sunderland 1 Watford 0 
 •  West Ham 1 Hull 0

An yi watsi da shirin Fifa na kara kasashe a gasar kofin duniya

Hadakar manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai ta yi watsi da shirin shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, Gianni Infantino, na kara yawan kasashen gasar cin kofin duniya da za a yi a 2026, daga 32 zuwa 48.

Shugaban hadakar, ko kungiyar ta ECA, tsohon dan wasan Jamus Karl-Heinz Rummenigge, ya ce duk wani abu da za a yi a game da gasar kamata ya yi, a mayar da hankali kan wasan.

Amma ba siyasa ko kasuwanci ba, don haka bai kamata a kara yawan masu shiga gasar ba.

Kungiyar ta ce daman tuni yawan wasan da ake yi a shekara ya yi yawan da ba za a amince da shi ba.

A farkon watan nan ne shugaban na Fifa, ya gabatar da shawarar mayar da gasar ta duniya ta kunshi kasashe 48, da za a raba zuwa rukuni 16, kowanne da kasashe uku-uku.

A ranar 9 ga watan Janairu ne majalisar zartarwar Fifa, za ta tattauna kan shirin na Infantino.

Fifa
Getty Images

GOAL Middlesbrough 2-0 Swansea

Alvaro Negredo

GOAL Middlesbrough 1-0 Swansea

Alvaro Negredo

Nadal ya nada Moya cikin masu horar da shi Tennis

Rafael Nadal ya kara tsohon zakaran kwallon Tennis na gasar French Open, Carlos Moya, a cikin masu horar da shi kwallon tennis. 

Moya mai shekara 40, zai yi aikin horar da Nadal tare da Toni Nadal da Francis Roig.

Premier
Getty Images

Sakamakon damben gargajiya

Wasannin da aka yi a gidan damben gargajiya na Idris Bambarewa da ke Maraba 'Yanya a jihar Nasarawa, Nigeria a ranar Juma'a. 

 • Shagon Dijango daga Arewa ya buge Dan Kadiri Shagon Kato daga Kudu a turmi na biyu. 
 • Aljanin Arewa daga Arewa ya buge Shagon Dogon Jafaru daga Kudu a turmin farko. 
 • Autan Bahagon Sani daga Kudu da Dan Aliyu daga Arewa turmi daya suka taka raba su dare ya yi.
Damben gargajiya
BBC

An biya 'yan Super Falcons kudadensu — NFF

Hukumar ta NFF ta samu biyan bashin ne bayan da gwamnatin Nigeria ta ba ta Dala Miliyan daya da dubu dari da saba'in domin ta biya ladan lashe kofi da hakkokin Super Falcons.

A ranar Larabar da ta gabata ne 'yan wasan na Super Falcons, wadanda suka lashe kofin kwallon kafar nahiyar Afirka na mata a watan Disamba a Kamaru, suka yi zanga-zanga zuwa Majalisar Dokoki da fadar Shugaban kasa saboda rashin biyansu kudaden da ya kamata a ba su. 

A ranar Juma'a NFF ta ce ta bai wa 'yan Super Falcons kudin da suke bin ta bashi

An fara amfani da bidiyo a gasar Fifa

Kashima Antlers ta Japan ta zama ta farko da ta ci gajiyar tsarin amfani da hoton bidiyo a gasar, Fifa, inda ta samu bugun fanareti ta ci 3-0 a wasan kusa da na karshe na cin kofin duniya na kungiyoyi.

Alkalin wasa Viktor Kassai ya tsayar da wasan ne wanda ake yi a Japan, bayan da mataimakinsa mai lura da hoton bidiyon wasan ya ankarar da shi kan wani laifi da aka yi, inda ya bayar da fanareti bayan ya kalli bidiyon.

Kungiyar Kashima ta doke Atletico Nacional ta Colombia, wanda hakan ya sa ta zama kungiya ta farko daga Asia da ta yi nasarar zuwa wasan karshe na gasar.

A ranar Lahadi ne Zakarun na Asia za su kara a wasan karshe da Zakarun Turai Real Madrid ko Zakarun Amurka ta Arewa Club America.

Premier
Getty Images

West Ham United da Hull City

'Yan wasan da za su murza-leda

Premier
BBC Sport

Middlesbrough da Swansea

Alvaro Negredo

  Alvaro Negredo ya kasa ci wa Middlesbrough kwallo a karawa 13 daga cikin 15 da ya yi mata a bana.  

Premier
Getty Images

Middlesbrough da Swansea

'Yan kwallon da za su taka-leda

Premier
BBC Sport

Crystal Palace 1-0 Chelsea

Yadda ake murza wasan

Premier
BBC Sport

Riyad Mahrez

Riyad Mahrez ne ya lashe kyautar Gwarzon dan kwallon Afirka na BBC na 2016

Masoya kwallon kafa a fadin duniya ne suka zabi dan wasan tsakiyar na Algeria da Leicester a kan Pierre-Emerick Aubameyang da Andre Ayew da Sadio Mane da kuma Yaya Toure.  

Riyad Mahrez ya lashe kyautar Gwarzon Kwallon Afirka na BBC na 2016.

Crystal Palace 1-0 Chelsea

Fabregas ya shiga fili ya maye gurbin Willian

Crystal Palace 0-1 Chelsea

Premier
BBC Sport

GOAL Crystal Palace 0-1 Chelsea

Diego Costa

Real Madrid da Kashima Antlers

Dan kasar Zambia, Janny Sikazwe ne zai alkalanci wasan karshe tsakanin Real Madrid da Kashima Antlers a gasar cin kofin duniya ta zakarun nahiyoyi da za a yi a filin wasa da ke Yokohama. 

Wannan shi ne karon farko da Sikazwe dan kasar Zambia zai alkaanci wasan da Real Madrid za ta yi. 

Sai dai kuma a gasar cin kofin duniya ta zakarun nahiyoyin a baya, Sikazwe ya busa fafatawar da Kashima Antlers ta doke Auckland City da ci 2-1.

Fifa World Club Cup
Real Madrid

Crystal Palace da Chelsea

'Yan wasan da za su murza-leda

Premier
BBC Sport

Wadanda suka fi zura kwallaye a Premier

 1. Alexis Sánchez Arsenal 12
 2. Diego Costa Chelsea 12
 3. Sergio Agüero M. City 10
 4.  omelu. Lukaku Everton 9
 5. Zlatan Ibrahimovic M. Utd 9
 6. Eden Hazard Chelsea 8
 7. Jermain Defoe Sunderland 8
 8. Christian Benteke C. Palace 8
 9. Theo Walcott Arsenal 7
 10. Sadio Mané Liverpool 7
Premier
Getty Images

Teburin Premier bayan wasannin mako 16

Premier
BBC Sport

Gasar Premier kai tsaye a BBC Hausa a radiyo

A shirinmu na sharhi da bayanai a gasar cin kofin Premier kai tsaye da harshen Hausa. 

Wannan makon za mu kawo muku daya daga cikin wasannin sati na 17 a karawar da za a yi tsakanin Crystal Palace da Chelsea. 

Za mu fara gabatar da shirin da karfe 1:00 na rana agogon Nigeria da Niger. 

Za kuma ku iya bayar da gudun mawarku a lokacin da ake gabatar da shirin a dandalinmu na muhawara da sada zumunta a BBC Hausa Facebook da kuma gugul filas.

undefined

Premier
AP

Gasar Premier League wasannin mako na 17

 • Crystal Palace da  Chelsea         
 • Middlesbrough da Swansea City    
 • Sunderland  da Watford              
 • West Ham United da Hull City               
 • Stoke City da Leicester City    
 • West Bromwich Albion da Manchester United    
Premier
Getty Images

Barkanmu da saduwa a cikin shirin bayanai kan wasanni kai tsaye