Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Gasar cin kofin Afirka Gabon 2017
 2. Gasar Firimiyar Nigeria
 3. Swansea City da Arsenal
 4. Leicester City da Chelsea
 5. Wasannin kwallon tennis
 6. Damben gargajiya

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

Nan muka kawo karshen shirin.

Damben boksin: De Gale da Badou

Zakaran damben boksin ajin IBF super-middleweight James DeGale zai kara da zakaran kambun WBC Badou Jack a New York a ranar Lahadi.

Gasar Premier wasannin mako na 21
BBC

Wasu wasannin damben gargajiya da aka yi a Marabar Yanya

Dambe 11 aka yi a gidan damben gargajiya na Bambarewa da ke Marabar Yanya

Gasar Premier: West Ham da Crystal Palace

'Yan wasan da za su murza-leda

Gasar Premier wasannin mako na 21
BBC Sport

Gabon 2017: Wace kasa ce za ta lashe?

Ivory Coast - Ta fito da sabbin 'yan wasa. 

Ghana    -  Ana mata kirari da Jamusawan Afrika 

Aljeriya - Na da 'yan wasan Afirka da aka fi ji da su a 2016. 

Senegal - Ta ci duk wasanninta na samun cancanta.

Masar - Ta yi rawar gani a wasannin cancanta kuma tana da nasibi.

Zambia - Ta yi cikas ga burin wasu a 2012 inda ta lashe gasar

Gasar Premier wasannin mako na 21
BBC

An tashi wasa Tottenham 4-0 West Brom

03:20

Kwallo ukun da Harry Kane ya ci ta taimaka wa Tottenham lashe wasanta na shida jere a gasar Premier, kuma za su matsa zuwa matsayi na biyu a kan tebur. Komai ya yi kyau a zagayen arewacin Londo.

Sam Sunderland ne ya lashe Dakar Rally

Sam Sunderland ya zama dan Burtaniya na farko da ya lashe gasar tseren babura ta Dakar Rally wadda ya ci a ranar Asabar.

Dan wasan mai shekara 27 ya bai wa Matthias Walkner na Austria tazarar minti 32 a zangon karshen gasar a Argentina. 

An fara gasar bana ta 38 a Asuncion zuwa Paraguay da Boliviasannan aka kammalata a Argentina.

Gasar wasannin premier mako na 21
Rex Features

Gasar Premier: Swansea City da Arsenal

'Yan wasan da za su murza-leda

Gasar Premier wasannin mako na 21
bbc

GOAL Tottenham 4-0 West Brom

Harry Keine kwallo na uku da ya ci a karawar

Murray zai kara kaimi a wasanninsa na tennis

Andy Murray ya ce sai ya kara kaimi a wasaninsa idan har yana son ya ci gaba da zama a mataki na daya a jerin wadanda suke kan gaba a wasan kwallon tennis. 

Dan wasan mai shekara 29 zakaran gasar Wimbledon ya maye gurbin Novak Djokovic a shekarar da ta wuce.

Murray zai fafata a gasar Australian Open a mako mai zuwa.

Gasar Premier wasannin mako na 21
Getty Images

GOAL Tottenham 3-0 West Brom

Harry Kane

Gasar Firimiyar Nigeria wasannin farko

Karawar da za a yi a ranar Lahadi

Bayan Kano Pillars ta fafata da Ifeanyiubah a ranar Asabar ne ake sa ran buha wasanni tara a ranar Lahadi.

Gasar Premier wasannin mako na 21
LMCNPFL Twitter

Kano Pillars da Ifeanyiubah

Kano Pillars ce ta doke Ifeanyiubah 2-0 a wasan da suka yi a bara a Kano, inda Prince Aggreh da Suleman Usman ne suka ci mata kwallayen biyu. 

Gabon 2017: 'Yan wasan da za su taka rawar gani

Baya ga Aubameyang, kallo zai koma kan fitaccen Dan wasan kwallon BBC na bana wanda ke tashe kuma Dan kwalon shekara na CAF Riyad Mahrez da kuma Dan wasan Afirka mafi tsada Sadio Mane

'Yan wasa 23 ne daga gasar Premier Ingila za su je gasar cin kofin Afirka ta Gabon ciki har da dan wasan Manchester United na kasar Ivory Coast Eric Bailly, da dan wasan West Ham daga kasar Ghana Andre Ayew, da Islam Slimani dan Aljeriya da ke buga wa Leicester kwallo dan wasan  Crystal Palace da zai wakilci kasar Ivory Coast Wilfried Zaha.  

Gasar Premier wasannin mako na 21
BBC

Yau za a fara gasar Frimiyar Nigeria

Kano Pillars da Ifeanyiubah

Gasar Premier wasannin mako na 21
NPFL Twitter

Jadawalin gasar Copa del Rey

Wasannin daf da na kusa da na karshe

Real Madrid za ta fafata da Celta Vigo a wasan daf da na kusa da karshe a gasar Copa del Rey.

Madrid ta kai wannan matakin ne bayan da ta ci Sevilla 6-3 a wasanni biyu da suka yi, yayin da Celta ta ci Valencia 6-2.

Mai rike da kofin bara, Barcelona, za ta kece raini da Real Sociedad, ita kuwa Atletico Madrid za ta kara ne da Eibar.

Kungiyar Alcorcon wadda ita kadai ce ba ta buga wasannin La ligar Spaniya za ta yi gumurzu ne da Deportivo Alaves.

Barcelona ce a kan gaba wajen yawan lashe Copa del Rey, bayan da ta dauki 28, sai Athletic de Bilbao mai 23, Real Madrid kuwa 19 ne da ita da Atletico de Madrid mai guda 10 a tarihi.

Za a fara wasannin farko a gasar daf da na kusa da karshe a ranar 18 ga watan Janairu, sannan a yi karon batta a karo na biyu a ranar 25 ga watan Janairun 2017.

Ga jadawalin wasannin da za a yi:

 • Real Sociedad da Barcelona
 • Alcorcon da Alaves
 • Atletico Madrid da Eibar
 • Real Madrid da Celta
Gasar Premier wasannin mako na 21
Getty Images

Muhawarar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

Asheerou Asabib Nasara Wannan wasa fatan a yi draw sannan ina fatan Liverpool ta lallasa Manchester Utd da ci 2 - 1.

Mustapha Mohammed To! Gasar Premier in ta zo tsakiya ko masana wasanni ma sai dai a hankali. 

Saleh Muhammed Saleh Damare To! Mu dai za mu iya cewa fadan da babu ruwanka, dadin kallo ne da shi. Up Barcelona! 

Shuaibu Adam Bagwai Hahaha! Ta safe ta yaro, Tottenham 2 - 0 West Brom. A ci gaba da gashi suya sai ranar sallah. Up Liverpool!

Tottenham sun mamaye wasa

Yayin da West Brom suka iya taba kwallo sau 52 ana minti 33 da fara wasa, Tottenham sun taba kwallo fiye da sau 200.  

Gasar Premier wasannin mako na 21
BBC

Gabon 2017: Yau za a fara gasar cin kofin Afirka

Yau Asabar da karfe 5:00 agogon Nijeriya ne za a fara gasar cin kofin Afirka karo na 31, inda mai masaukin baki Gabon za ta buga wasan farko da Guinea-Bissau

Shekara sittin kenan tun bayan fara gasar cin kofin Afirka cikin 1957 a Sudan, inda kasa uku ta fafata kuma Masar ta dauki kofi.

Gasar a bana ta kunshi wasa 32 a tsawon kwana 23, inda kasa 16 - za su kara da juna cikin rukuni hudu. A ranar 5 ga watan Fabrairu ne za a buga wasan karshe, inda kasar za ta tafi da kofi wanda aka kere shi a kasar Italy da kuma tsabar kudi dala miliyan 4.

Gasar Premier wasannin mako na 21
BBC

GOAL Tottenham 2-0 West Brom

GOAL Tottenham 1-0 West Brom

Haryy Kane

'Na yi shekara 4 masu dadi a West Ham'

Yau, Sam Allardyce zai kara da daya daga cikin tsoffin kungiyoyin da ya rike, wato West Ham.

Allardyce ya ce bai cika son kallon baya ba, amma ya ji dadi zamansa a West Ham tsawon shekara hudu.

"Ina da kyakkyawan fata a wannan wasa, karon farko kenan da zan koma sabon filin wasan.Abin sha'awa ne kwarai amma dai sakamako shi ne muhimmin abin da na je nema."

Gasar Premier wasannin mako na 21
Getty Images

Tottenham ba ta fito wannan wasa da wasa ba

Gasar Premier wasannin mako na 21
BBC Sport

West Brom na neman cin wasa karo na uku a jere

Gasar Premier wasanni mako na 21
BBC Sport

Muhawarar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

Dan Hajiya A Yakasai Bahaushe dai ya ce ba a san ma ci tuwo ba, sai miya ta kare. Fatana a nan shi ne Allah ya sa west brom ta ci kamar 3-0 up arsenal up bacerlona.

Yaya Muhammad Madaki Hadejiia Ana dara ga dare ya yi. Hakika wannan karawa za ta yi armashi ganin yadda Tottenham suke kan ganiyarsu su kuma West brom za su fuskanci matsi a wannan wasan saboda haka sai sun dage.

undefinedSamaila Sparty Sankalawa A gaskiya ni dai ina fatan samun nasara ga West brom a kan Tottenham domin kulob dina na Arsenal ya kara matsawa.  

'Yan saman teburin gasar Premier

Bayan da aka buga wasannin mako na 20.

Gasar Premier wasannin mako na 21
BBC Sport

'Yan kasan teburin gasar Premier

Bayan da aka yi wasannin mako na 20

Gasar Premier wasannin mako na 21
BBC Sport

Konta ta lashe gasar Sydney International

Gwarzuwar 'yar kwallon Tennis ta Birtaniya Johanna Konta ta lashe gasar Sydney International ranar Juma'a inda ta yi nasara a kan Agnieszka Radwanska da ci 6-4 6-2 a kasar Australia.

Konta, wacce ita ce ta goma a duniya a fagen Tennis, ta doke takwararta 'yar kasar Poland a zagaye na uku.

Gasar premier wasannin mako na 21
Getty

Karawar da za mu kawo muku kai tsaye a BBC rediyo

A shirinmu na sharhi da bayanai a gasar cin kofin Premier kai tsaye da harshen Hausa. 

Wannan makon za mu kawo muku daya daga cikin wasannin sati na 36 ne a karawar da za a yi tsakanin Tottenham da West Brom. 

Za mu fara gabatar da shirin da karfe 1:30 agogon Nigeria da Niger. Za kuma ku iya ba da gudunmawarku a lokacin da ake gabatar da shirin a dandalinmu na muhawara da sada zumunta a BBC Hausa Facebook da kuma gugul filas.  

Premier wasannin mako na 21
Getty

Gasar Premier wasannin mako na 21

 • Tottenham Hotspur da West Bromwich Albion
 • Sunderland da Stoke City    
 • West Ham United da  Crystal Palace      
 • Watford da Middlesbrough   
 • Hull City da Bournemouth 
 • Burnley  da Southampton 
 • Swansea City da Arsenal        
 • Leicester City da Chelsea    

Barkanmu da shigo wa fagen labaran wasanni kai tsaye