Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Madrid ta bai wa Munich aron Rodriguez
  2. Benitez ya yi korafi kan yadda 'yan kwallo ke tsada
  3. Arsenal na fatan Sanchez zai ci gaba da zama a kungiyar

Rahoto kai-tsaye

time_stated_uk

Nan muka kawo karshen shirin za mu ci gaba a ranar Laraba

Mandanda ya sake komawa Marseille

Mai tsaron ragar tawagar Faransa Steve Mandanda ya sake koma kungiyarsa ta Marseille daga Crystal Palace kan yarjejeniyar shekara uku.

Mandanda mai shekara 32 ya buga wa Palace wasa tara a kakar da aka kammala tun komawarsa kungiyar a watan Yulin 2016.

Mai tsaron ragar ya buga wa Marseille wasa 443 a kaka tara da ya taka mata leda

Crystal Palace
Getty Images
Mandanda ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Faransa wasa 24

Manchester United na son taya Dier

Daily Mirror

Kocin Manchester United, Jose Mourinho na son mahukuntar kungiyar su taya dan kwallon Eric Dier na Tottenham in ji Daily Mirror.

United din tana son sayen Dier mai wasan tsakiya kan kudi fam miliyan 60.

Manchester United
Getty Images
Tottenham ce ta kare a mataki na biyu a kan teburin Premier da aka kammala

Watakila Tottenham ta dauki Iheanacho

The Sun

Tottenham za ta riga Leicester City daukar dan wasan Manchester City, Kelechi Iheanacho, inda take fatan musaya da mai tsaron bayanta Kyle Walker domin ya koma Ettihad da taka-leda.

Manchester City
Getty Images
Iheanacho baya buga wasanni akai-akai tun lokacin da Guardiola ya karbi jan ragamar kungiyar

Liverpool ta kammala daukar Solanke

Liverpool ta kammala daukar matashin dan wasan Chelsea, Dominic Solanke, bayan da yarjejeniyarsa da kungiyar ta kare.

Kotu ce za ta yanke kudin da Liverpool za ta sayi dan kwallon mai shekara 19, amma ana ta rade-radin cewar zai kai darajar fam miliyan uku.

Solanke ya ci wa tawagar Ingila ta matasa kwallo uku a gasar kofin duniya da ta lashe a Koria ta Arewa.

Liverpool
Getty Images
A karshen kakar da aka kammala ne yarjejeniyar Solanke ta kare da Chelsea

Rooney zai fara yi wa Everton wasa

Wayne Rooney zai fara buga wa Eveton tamaula a wasan sada zumunta da kungiyar za ta yi da Gor Mahia ta Kenya da za su fafata a Tanzaniya a ranar Alhamis.

Kociyan Everton, Ronald Koeman ya tabbatar da cewar duk 'yan wasan da ya je da su karawar za su buga minti 45 a wasan sada zumuntar.

Rooney ya koma Everton daga Manchester United shekara 13 da ya bar kungiyar da ya fara buga wa tamaula.

Evrton
Getty Images
Rooney ya koma United da murza-leda a 2004 kan kudi fam miliyan 27

Watakila Ulloa ya tsawaita zamansa a Leicester

Sky Sport

Duk da zawarcin da Betis da Getafe da Levante suke yi wa dan kwallon Leicester City, Leonardo Ulloa, Sky Sports ta ce dan wasan na daf da tsawaita zamansa a kungiyar da ke buga gasar Premier.

Watanni shida da suka wuce Ulloa ya bukaci izinin barin Leicester domin ya gwada sa arsa a wata kungiyar.

Tamaula
Getty Images
Ulloa ya bukaci ya bar Leicester City a baya sakamakon rashin buga wasa akai-akai

Hull City ta dauki aron Aina daga Chelsea

Kungiyar Hull City ta dauki aron dan kwallon Chelsea, Ola Aina.

Aina mai tsaron baya mai shekara 20 ya buga wa Chelsea wasa uku a gasar Premier a sauyin 'yan kwallo a kakar da ta kare da wasa daya a FA Cup, sannan aka fara wasa biyu da shi a Capital One Cup.

Aina shi ne dan wasan da Hull ta dauka tun lokacin da Leonid Slutsky ya karbi aikin horar da kungiyar a watan Yuni.

Chelsea
Getty Images
Aina zai buga wasa aro a kungiyar Hull City

Sevilla ta nemi a ba ta aron Amavi

Kungiyar Sevilla ta bukaci Aston Villa ta ba ta aron Jordan Amavi, domin ya buga mata wasa aro.

Tun farko Sevilla ta so ta sayi dan wasan kan kudi fam miliyan takwas, daga baya ta bukaci a ba ta shi aro.

Sai dai Villa na son ta sayar da dan kwallon ba wai ta bayar da shi aro ba.

Aston Villa
Getty Images
Aston Villa na fatan ta sayar da dan kwallonta Amavi da Sevilla

Mario Suarez zai koma China da taka-leda

Mario Suarez zai ci gaba da murza leda a gasar China.

Dan kwallon Spaniya mai wasan tsakiya zai koma Guizhou Hengfeng Zhicheng wadda Gregorio Manzano ke horarwa.

Dan wasan Watford ya koma Valencia ta wasa aro a 2016.

Cinikayyar 'yan kwallo
Getty Images
Suarez ya buga wa Watford wasa 15 a kakar da ta kare

Vallecano ta tsawaita zaman Dorado

Kulob din Rayo Vallecano ya sanar da cewar ya tsawaita yarjejeniyarsa da Chechu Dorado zuwa shekara daya.

Cinikayyar 'yan kwallo
Getty Images
Dorado zai ci gaba da wasa shekara daya a Vallecano

West Ham na son daukar Hart

West Ham United na sha'awar daukar mai tsaron bayan Manchester City, Joe hart. Hart ya buga wasa aro a Torino ta Italiya a kakar bara, amma yanzu ya koma City da taka-leda kungiyar da yake da yarjejeniya zuwa 2019.

Tun lokacin da Pep Guardiola ya karbi ragamar jan Manchester City, Hart ya zama baya buga wasa akai-akai.

Manchester City
Getty Images
Hart ya koma Manchester City a 2006

Rodriguez zai koma Munich da taka-leda aro

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta amince ta bai wa Bayern Munich aron James Rodriguez domin ya buga mata tamaula.

Munich din ta amince da Rodriguez ya taka mata leda tsawon shekara biyu da zarar ta gwada lafiyar dan kwallon.

Real Madrid
Getty Images
Rodriguez ya koma Real Madrid da murza-leda a 2014

Barkanmu da saduwa a cikin shirinmu na yau