Takaitacce

  1. Aubameyang zai ci gaba da wasa a Dortmund
  2. Neymar zai ci gaba da wasa a Barcelona
  3. shin Perisic zai koma United?
  4. PSG na neman Alexis Sanchez
  5. Aguero zai koma Chelsea?
  6. Ko PSG za ta iya sayen Neymar
  7. Lukaku ya ci kwallon farko a United
  8. Mata zai yi jinyar mako daya
  9. Daniel Sturridge ya shirya tsaf - Klopp

Rahoto kai-tsaye

Daga Naziru Mikailu da Mohammed Abdu

time_stated_uk

Nan muka kawo karshen shirin da fatan za ku tara a shirinmu na gobe

Leiva ya koma Lazio da wasa

Dan kwallon Liverpool, Lucas Leiva ya kammala komawa Lazio domin ya taka mata leda kan kudi fan miliyan biyar. Lucas mai shekara 30, shi ne dan wasan Liverpool da ya fi dadewa a kungiyar, wanda ya koma Anfield a 2007 daga Gremio ta Brazil. Dan kwallon ya buga wa Liverpool wasa 345, inda ya fafata a gasar Premier sau 247.

Kai tsaye
Getty Images

West Ham United ta kammala daukar Hart

Manchester City ta kammala bayar da Joe Hart aro ga kungiyar West Ham United.

A bara ne kocin City, Pep Guardiola ya cewa Hart zai iya komawa wata kungiyar, domin ba zai yi amfani da shi ba.

Mai tsaron ragar mai shekara 30, ya buga wasa aro a Torino a kakar da ta kare.

Kai tsaye
ge

Arnautovic ya koma West Ham United

West Ham United ta cimma yarjejeniyar daukar dan kwallon Stoke City Marko Arnautovic.

Tun farko Stoke City ta ki sallama tayin da West Ham ta yi wa dan wasan sau biyu, amma yanzu ta sayar mata da dan kwallon kan kudin da ake cewa ya kai fan miliyan 24.

Arnautovic mai shekara 28, ya koma Stoke City daga Werder Bremen kan yarjejeniyar shekara hudu, kuma saura kaka daya ta rage masa a Stoke din.

Dan wasan ya ci kwallo bakwai a wasa 35 da ya buga wa kungiyar a kakar da ta kare.

Kai tsaye
Getty Images

Aubameyang zai ci gaba da zama a Dortmund

Daraktan Borussia Dortmund, Micheal Zorc ya ce Pierre-Emerick Aubameyang zai ci gaba da murza-leda a kungiyar.

An yi ta alakanta Aubameyang mai shekara 28 da cewar zai koma gasar Premier da wasa ko Paris St-Germain ko kuma AC Milan a bana.

Zorc ya ce Dortmund ta yanke shawarar ci gaba da amfani da Aubameyang a wasanninta, kuma shi a wajensa an kammala rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan tamaula ta Turai.

A tsakar daren 31 ga watan Agusta za a rufe kasuwar cinikin 'yan wasan tamaula ta Jamus.

Kai tsaye
Getty Images

Muhawarar da kuke yi a BBC Hausa Facebook

Shuaibu Adam Bagwai Hahaha to Arsenal dabara dai daman bata kai rakumi inda ake so har sai an hada da akala. Gara ma kufitar da makudan kudade kusayi 'yan wasan da zasu fitar daku kunya, domin ance "sayen nagari mai da kudi gida".

Hashimu Waso cefane bane iya miya, 'yan Manchester United kuyi hattara akwai maza a gabanku up Chelsea.

Hassan Musa Hadejia DW Gaskiya ina jin dadin shirinku, kuma yana kawatardani 100% kuma ina sanar da 'yan Manchester United mun yi shirin bugawa da kowa.

Babu wanda ya taya Mahrez - Shakespeare

Mai horar da Leicester City, Craig Shakespeare, ya ce har yanzu bai samu wata kungiyar da ta taya Riyad Mahrez ba.

Sai dai kuma mai tsaron bayan Leicester City, Robrt Huth ba zai a fara gasar Premier da za a fara a cikin watan Agusta ba, sakamakon raunin da ya yi.

Kai tsaye
Getty Images

Trippier ya tsawaita zamansa a Tottenham

Mai tsaron bayan Tottenham, Kieran Trippier ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka-leda a kungiyar zuwa shekara biyar.

Dan wasan mai shekara 26 ya koma kungiyar da wasa daga Burnley kan kwantiragin shekara biyar.

Kai tsaye
Getty Images

Neymar zai ci gaba da wasa a Barcelona

Neymar zai ci gaba da taka-leda a Barcelona duk da rade-radin da ake cewar zai koma Paris St Germain a bana.

Mataimakin shugaban Barcelona Jordi Mestre ne ya tabbatar da cewar ba za su sayar da dan kwallon ba, zai kuma buga kakar wasan bana da za a fara a Spaniya.

Rahotanni a Spaniya sun ce PSG na son sayen Neymar mai shekara 25, bayan da kungiyar ta dauki abokin wasansa a tawagar kwallon Brazil, Dani Alves.

Neymar ya koma Barcelona a 2013, a kuma watan Oktoban 2016 ya tsawaita zamansa a Camp Nou kan yarjejeniyar shekara biyar.

Kai tsaye
Getty Images

Getafe ta dauki aron Bergara

Getafe ta sanar da daukar Markel Bergara daga Real Sociadad domin ya buga mata tamaula aro a kakar da za a fara a bana.

Kai tsaye
Getafe

Valencia zai ci gaba da yi wa United wasa a Amurka

Mai tsaron bayan Manchester United, Antonio Valencia zai buga wa kungiyar wasan atisayen tunkakar gasar bana da take yi a Amurka duk da jan katin da aka yi masa a karawa da Salt Lake a ranar Litinin.

A 2006 Paul Scholes da Wayne Rooney an hana su buga wa United wasa uku bayan da aka ba su jan kati a wasannin atisayen a Amsterdam.

Mahukunta ne suka sauya dokar, inda suka ce sai anyi wani babban laifi ne za a dakatar da dan kwallo daga buga wasa, girman laifin da ya aikata.

Kai tsaye
Getty Images

Gasar damben Mota: Za a ci gaba da wasa

Za a karasa wasan daf da na kusa da karshe a gasar damben cin mota a yammacin Talata a filin wasa na Ado Bayero Square da ke birnin Kanon Nigeria.

Za a fara dambatawa tsakanin Bahagon Sanin Kurna daga Arewa da Bare-Bare daga Kudu.

Sannan asa zare tsakanin Dan Ali Shagon Bata isarka daga Kudu da Sanin Shagon Kwarkwada daga Kudu.

Kai tsaye
Getty Images

Ramos da Marcelo sun ci kofi 15 a Madrid

Kyaftin din Real Madrid, Sergio Ramos da Marcelo sun lashe kofi 15 kowannensu a kungiyar.

'Yan wasan biyu sun ci kofin Zakarun Turai uku da na Zakarun nahiyoyi biyu da La Liga hudu da Copa del Rey biyu da Uefa Super Cup biyu da na Spanish Super cup biyu.

A kakar wasannin da aka kare Ramos da Marcelo suka lashe kofin La Liga da na Zakarun Turai.

Wasu 'yan kwallon Madrid biyu da suke biye a yawan cin kofi a kungiyar su ne Karim Benzema da Cristiano Ronaldo wadanda kowannensu ya lashe guda 12.

Kai tsaye
Getty Images

Wenger na son kara sayen 'yan kwallo

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce yana son ya kara sayen 'yan wasa kafin a fara kakar wasannin bana. Wenger ya ce a shirye yake ya kara karfin kungiyar, wanda tuni ya dauki Sead Kolasinac da kuma Alexandre Lacazette.

Kai tsaye
Getty Images

Ebola ya kai daf da karshe a damben mota

Abdurrazak Ebola ya kai wasan daf da karshe a gasar damben cin mota a yammacin Litinin a filin wasa na Ado Bayero Square da ke birnin Kano, Nigeria.

Ebola ya kai zagayen gaba ne bayan da ya doke Jirgi Bahago Guramada a turmin farko.

Kai tsaye
BBC

Ya ya batun komawar Perisic United ne?

Jose Mourinho ya ce bai san me yake faruwa ba kan batun daukar Ivan Perisic na Inter Milan zuwa Manchester United.

Ana alakanta cewar dan wasan tawagar Croatia zan koma Old Trafford da taka-leda kan kudi fan miliyan 48.

Mourinho ya ce bai da masaniya a lokacin da aka tambayeshi batun dan wasan, bayan da United ta ci Real Salt Late 2-1.

Kai tsaye
Getty Images

Damben mota: Ali Kanin Bello ya kai daf da karshe

Ali Kanin Bello ya kai wasan daf da karshe a gasar cin mota da ake yi a filin wasa na Ado Bayero Square da ke Kano Nigeria a yammacin Litinin.

Ali kanin bello dan damben Arewa ya yi nasarar buge Ali Shagon Saiwa daga Kudu a turmin farko.

Kai tsaye
BBC

Shin ina Michu yake?

Isah Sani Mai Arsenal Shin ina labarin dan wasan gabane swensea city wato michu? a wacce kugiya yake taka ledane yanzu?

Amsa: Michu ya yi ritaya daga buga tamaula.

Za a fara gasar kwallon golf a ranar Alhamis

An raba jadawalin wasan zagayen farko a gasar kwallon golf ta 'yan wasa bibiyu, inda Henrik Stenson da Jordan Spieth za suyi wasa tare sai Dustin Johnson da Rory McIlroy a rukunin farko.

Shi kuwa Sergio Garcia da Jason Day da Zach Johnson da Mark O'Meara da kuma Ryan Moore suna tare.

Kai tsaye
Getty Images

Ko za ku iya tuna dan wasa Michu?

Shekara hudu da ta wuce Michu ya ci wa Swansea City kwallo 18 a gasar Premier a kaka daya ya zama na biyar a jerin wadan da suka fi cin kwallo a gasar ta Ingila, sannan ya ya jefa kwallo a raga a 2013 a League Cup wanda Swansea ta lashe kuma kofi na farko da ta dauka.

Yanzu yana da shekara 31 ya kuma yi ritaya. Bayan da ya bar buga gasar Premier ya koma Napoli inda ya yi rauni a kafarsa daga nan ya koma Langreo da Real Oviedo a Spaniya, yanzu raunin ya hana shi murza-Leda.

Kai tsaye
Getty Images

Alaves ta duba lafiyar Wakaso

Kungiyar Deportivo Alaves ta sanar da daukar Wakaso ta kuma kammala duba lafiyarsa, inda za ta gabatar da shi a gaban magoya bayanta a yammacin Talata.

Kai tsaye
Deportivo Alaves
Alaves ta ce za ta gabatar da Wakaso a gaban 'yan jarida a yammacin Talata

Arsenal za ta sayi dan wasa mafi tsada

Jaridar Mirror ta ce watakila Arsenal ta sayi Lacazette kan kudi Yuro miliyan 60 a matsayin mafi tsada a tarihi a bana, ko kuma Thomas Lemar na Monaco kan kudi Yuro miliyan 90.

Kai tsaye
Getty Images
Lemar dan wasan Monaco da kungiyoyi da dama ke zawarci

Chelsea da Everton na zawarcin Benteke

Kociyan Crystal Palace, Frank de Boer yana da imanin cewar dan wasan gaba Christian Benteke, mai shekara 26, zai tsaya a kungiyar duk da rade-radin da ke alakanta shi da Chealsea da Everton, a cewar jaridar Evening Standard.

Benteke ya ci kwallo 15 a gasar Firimiya ta kakar 2016-17.

Christian Benteke
Getty Images

Za a musanya Matial da Ivan Perisic

Jaridar La Gazzetta dello Sport ta Italiya ta rawaito cewa dan wasan gaba na Manchester United Anthony Martial ka iya zama wanda za a yi amfani da shi a yarjejeniyar musaya ta sayen dan wasan gefe na Inter Milan, Ivan Perisic, mai shekara 28.

Martial wanda dan kasar Faransa ne, mai shekara 21, bai yi kokari sosai a kakar da ta gabata ba a United.

Anthony Martial
Getty Images

Szczesny ya isa Juventus

Mun kawo muku labarin cewa gola Arsenal Wojciech Szczesny, wanda ya shafe shekara biyu yana zaman aro a Roma, na shirin komawa Juventus a kan fan miliyan 10.

Itama Juventus ta wallafa labarin a shafinta na Twitter tare da hoton dan wasan yana sauka a filin jirgin sama.

Babu wanda ya taya Riyad Mahrez - Shakespeare

Kocin Leicester City Craig Shakespeare ya tabbatar da cewa kawo yanzu babu wanda ya nemi sayen dan wasan gefe na kungiyar Riyad Mahrez.

A watna Mayu ne dan kwallon na kasar Algeria ya ce yana san ya bar kungiyar.

Mahrez ya taka rawar gani a lokacin da Leicester ta lashe gasar Firimiya, kuma ya taimaka wa kungiyar kare matsayinta a kakar da ta gabata.

Riyad Mahrez
Getty Images

Ba za a fara Firimiya da Robert Huth ba

Mai yiwuwa ba za a fara kakar bana da dan wasan baya na Leicester City Robert Huth ba bayan da ya samu rauni a kafar sahunsa.

Ana sa ran dan wasan mai shekara 32 zai shafe mako shida zuwa takwas yana jinya, kuma bai bi tawagar kulob din zuwa Hong Kong ba domin atisaye.

"An yi masa tiyata kuma aikin ya yi kyau," a cewar kocin Leicester Craig Shakespeare.

Robert Huth
Getty Images

Szczesny na dab da komawa Juventus

Jaridar Tuttosport ta Italiya ta rawaito cewa Juventus na dab da kammala sayen golan Arsenal Wojciech Szczesny.

Dan wasan na Poland mai shekara 27, har yanzu yana hannun Arsenal a hukumance duk da cewa ya shafe shekara biyu bai taka musu leda ba, inda ya je Roma a matsayin aro.

Ana sa ran Arsenal za su samu kudi kusan fan miliyan 10.

Jaridar ta kuma rawaito cewa Juventus na shirin sayen dan wasan baya na Italiya Mattia De Sciglio, mai shekara 24, daga AC Milan, yayin da dan wasan Spaniya Alex Berenguer, zai koma Torino daga Osasuna.

Tuttosport
Tuttosport

Ko PSG za ta iya sayen Neymar?

Jaridar Sport ta Sapaniya ta bada labarin cewa Paris St-Germain na sha'awar sayen dan wasan gaba na Barcelona Neymar.

Akwai yarjejeniyar dala miliyan 222 a kwantiragin dan kwallo idan har yana so ya bar Barcelona. Sai dai jaridar ta ce PSG a sherye suke su biya wannan kudi.

Dan wasan da ya fi kowanne tsada a duniya a yanzu shi ne Paul Pogba wanda Manchester United ta saya daga Juventus kan fan 89.3.

Neymar
Getty Images

Juan Mata zai yi jinyar mako daya

Dan wasan tsakiya na Manchester United Juan Mata zai yi jinyar mako guda bayan da ya samu rauni a wasan sada zumuntar da United ta yi da Real Salt Lake.

Dan kwallon na Spaniya ya fita daga fili bayan da Sebastian Saucedo ya taka shi, abin da ya sa aka maye gurbinsa da Matteo Darmian a wasan.

"Mata ya samu rauni a kafar sawunsa amma ina fatan ba abu ne mai girma ba," kamar yadda kociya Jose Mourinho ya ce bayan kammala wasan.

Ya kara da cewa: "Watakil 'yan kwanaki, ko mako daya. Matsalar Darmian ba abar damuwa ba ce."

Juan Mata a kwance da kuma Ander Herrera
Getty Images

Daniel Sturridge ya shirya tsaf - Klopp

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce Daniel Sturridge na cikin koshin lafiya kuma ya shirya tsaf fiye da kowanne lokaci tun bayan zuwan kocin Liverpool.

Rauni ya sa wasa 46 kawai dan kwallon ya buga a gasar Lig a kaka uku da ta gabata.

"Yana cikin koshin lafiya sosai," a cewar Klopp, wanda ya karbi ragamar Liverpool a watan Oktoban 2015.

Daniel Sturridge
Getty Images

PSG na zawarcin Alexis Sanchez

Magoya bayan Arsenal ku kawar da fuskarku

Jaridar L'Equipe ta Faransa ta rawaito cewa Paris St-Germain na zawarcin Alexis Sanchez na Arsenal.

Jaridar ta ce dan wasan na Chile na saon barin Arsenal domin ya buga gasar cin kofin zakarun Turai, gasar da Arsenal ba za ta je ba saboda ta kare a mataki na biyar a bara.

L'Equipe ta kara da cewa kocin Arsenal Arsene Wenger ba ya son sayar da dan kwallon mai shekara 28 ga abokan hamayyarsa a gasar Firimiya.

Jaridar L'Equipe
Jaridar L'Equipe

Aguero zai koma Chelsea?

Jaridar Daily Mirror ta Birtaniya ta rawaito cewa Chelsea na yunkurin sayen dan wasan gaba na Manchester City Sergio Aguero kan kudi fan miliyan 60.

Daily Mirror
Daily Mirror

Lukaku ya ci kwallon farko a Man Utd

Romelu Lukaku ya ci kwallonsa ta farko a Manchester United a wani wasan sada zumunci inda kungiyar ta Jose Mourinho ta doke Real Salt Lake 2-1.

Dan asalin Beljium din mai shekara 24, wanda ya zo Manchester daga Everton kan Fam miliyan 75 ya ci kwallon da ya raba gardama a wasan minti bakwai kafin a je hutun rabin lokaci bayan Henrikh Mkhitaryan ya ramawa United kwallon da aka zira mata a minti 20.

Daga baya United ta rasa Juan Mata da ya ji cwo da kuma Antonio Valencia da aka ba wa jan kati.

Morinho ya ce: "[kwallon Lukaku] ya yi mashi kyau, amman ba wani abu ba ne mai muhimmi a gare ni."

Kociyan na Manchester ya kara da cewar: "Na gaya masa ina kaunar abin da yake yi. Yana taimakawa a sha kwallo. Yana ja. Yana rike kwallo da kyau. Ina kaunar duk abin da yake yi."

Romelu Lukaku
Getty Images
Romelu Lukaku ya koma United kan fam miliyan 75 daga Everton

Barkanmu da hantsi

Jama'a barkanmu da sake saduwa a wannan fili, inda muke kawo muku sharhi kan abubuwan da ke gudana a fagen wasanni, musamman hada-hadar cinikin 'yan kwallo.

Michu
Getty Images