Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Chelsea ta amince ta dauki Morata
 2. Aguero zai ci gaba da wasa a Ettihad
 3. Arsenal na neman Karim Benzema
 4. Conte ne koci mafi tsada a tarihin Chelsea
 5. Ross Barkley na son komawa Tottenham
 6. Shugaban Barcelona ya ce babu inda Neymar zai je
 7. Leicester na sahun gaba wurin neman Kelechi Iheanacho

Rahoto kai-tsaye

Daga Naziru Mikailu da Mohammed Abdu

time_stated_uk

Nan muka kawo karshen shirin

Da fatan za ku tara a shirinmu na gobe domin kawo muku wasu labaran wasanni.

Wasannin mako 30 a gasar Firimiyar Nigeria

Wasan Enugu Rangers da MFM ruwan sama ne ya hana a ci gaba da fafatawar, an tsayar da gobe domin a karasa karawar.

Kai tsaye
LMCNPFL

Sakamakon damben gasar mota

Bahagon Sanin Kurna ya kai wasan daf da karshe a gasar damben mota a ranar Laraba a filin wasa na Ado Bayero Square da ke birnin Kanon Nigeria.

Bahagon Sanin Kurna daga Arewa ya buge Bare-bare daga Kudu.

Shi kuwa Dan Ali Shagon Bata isarka daga Kudu ya kai zagayen gaba bayan da ya sasanta da shi da Sanin Shagon Kwarkwada shi ma dan damben Kudu.

Sauran wadanda suka kai wasan daf da karshe sun hada da Ali Kanin Bello daga Arewa da Abdurrazak Ebola.

Kai tsaye
BBC

Wasan damben gargajiya da aka yi a baya can

Sakamakon gasar Firimiyar Nigeria

Wasannin mako na 30

 • Wikki 1-0 ABS
 • Katsina 1-0 Pillars
 • Remo Stars 1-1 3SC
 • Enyimba 2-1 Lobi
 • Plateau Utd 1-0 FCIU
 • Gombe Utd 0-0 Tornadoes
 • Abia Warriors 0-0 Akwa
 • Nasarawa 2-1 El-Kanemi
 • Rivers Utd 0-1 Sunshine Stars

'Yan wasan da aka haifa ranar 19 ga Yuli

Matt Miazga shekara 22

Neto shekara 28

Kevin Großkreutz shekara 29

Nene shekara 36

Josue shekara 38

Ebbe Sand shekara 45

Bolt zai yi ritaya bayan tseren Landan

Usain Bolt ya ce zai fafata a tseren mita 100 da kuma ta 'yan wasa hudu a gasar da birnin Landan zai karbi bakuncin duniya a Agusta.

Bolt din wanda ya lashe lambar zinare takwas a Olympic ya ce da zarar ya kammala wasa a tseren Landan din zai yi ritaya.

Za a fara tseren mita 100 a ranar 5 ga watan Agusta, sannan a yi ta 'yan wasa hudu a ranar ta Asabar daga na Bolt ya rataye takalmansa.

Kai tsaye
Getty Images

Barcelona ta je Amurka da 'yan wasa 26

Sabon kociyan Barcelona, Ernesto Valverde ya bayyana 'yan wasa 26 da ya tafi da su Amurka a ranar Laraba, domin buga atisayen tunkarar kakar bana.

Barcelona za ta buga gasar International Champions Cup, inda za ta kara da Juventus ranar 22 da watan Yuli da Manchester United 26 ga watan da kuma Real Madrid a ranar 29 ga watan na Yuli.

Ga jerin 'yan wasan Barca da ta je da su Amurkan: Pique da Rakitic da Sergio da Denis Suarez da Arda da Iniesta da Suarez da Messi da Neymar Jr. da Cillessen da Mascherano da Paco Alcacer da Jordi Alba da Digne da S. Roberto da Aleix Vidal da Umtiti da Semedo da Marlon da Douglas da Samper da Vermaelen da Munir da Ortola da Jokin da Ezkieta da kuma Alena.

Kai tsaye
Getty Images

Juankar ya koma Malaga zuwa 2021

Juankar ya zama dan kwallon Malaga, bayan da ya buga mata wasa aro kakar wasa biyu.

Dan kwallon ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara hudu.

Kai tsaye
Malaga FC

Takaitattun labarin wasanni

Wanda muka gabatar a ranar Talata

Takaitattun labarin wasanni na Talata 18072017

Arsenal ta ci Munich a fenariti

Arsenal 1-1 Bayern Munich

Arsenal ta doke Munich 3-2 a bugun fenariti

Arsenal ta farke kwallon da Munich ta ci

Arsenal 1-1 Bayern Munich

Kai tsaye
Reuters

Ana tauye hakkin kwararrun 'yan kwallon Afirka

Ana tauye hakkin wasu 'yan kwallon Afirka

A rana irin ta 19 ga Yuli..........

A rana irin ta 19 ga watan Yulin bara Liverpool ta amince ta dauki Christian Benteke daga Aston Villa kan kudi fan miliyan 32.5.

Kai tsaye
Getty Images

Watakila Giroud ya koma Everton

Everton na son sayen dan kwallon Arsenal, Olivier Giroud bayan da Borrusia Dortmund ta ce ba za ta sayar da Pierre-Emerick Aubameyang in ji Daily Telegraph.

Kai tsaye
Getty Images

Damben gasar mota ta Kano

Zubar ruwan sama ne ya hana ci gaba da damben gasar cin mota a ranar Talata tsakanin Bahagon Sanin Kurna daga Arewa da Bare-Bare daga Kudu da fafatawa tsakanin Ali Shagon Bata isarka daga Kudu da Sani Shagon Kwarkwada daga Kudu a gumurzun wasan daf da na kusa da na karshe.

Muhukuntan gasar sun tsayar da ranar Laraba da yammaci domin ci gaba da wasannin a filin wasa na Ado Bayero Square da ke Kanon Nigeria.

Kai tsaye
BBC

Arsenal ta sauya Kolasinic

Arsenal 0-1 Bayern Munich

Arsenal ta sauya dan sabon dan wasan da ta dauka a bana Saed Kolasinic.

Gasar Firimiyar Nigeria mako na 30

Alkalan wasan Wikki da ABS

Alkali: Imam M. Umar

Mataimaki na daya: Shehu Saidu

Mataimaki na biyu: Ibrahim Yusuf

Mai jiran kar-ta-kwana: Musa I. Daura

Kai tsaye
gett

Benteke zai buga wa Palace wasa

Liverpool v Crystal Palace

Crystal Palace za ta fara wasa da Christian Benteke a karawa da za ta yi da tsohuwar kungiyarsa Liverpool a Hong Kong.

Muhawarar da kuke yi a BBC Hausa Facebook

Sa'idu Gagiyo Katamma Ni Magoyin Bayan Manchester United ne kuma ina yi wa kungiyar fatan alkairi, ina bukatar kungiyar ta saya mana 'yan wasan tsakiya mai tare kwallon.

Lehmann yana zaune a kan bencin Arsenal

Arsenal 0-1 Bayern Munich

Tsohon kyaftin din Arsenal wanda ya tsare mata raga Jens Lehman na zaune kusa da Arsene Wenger a wasan sada zumunta da Munich a Shanghai.

Kai tsaye
Getty Images

Wasan mako na 30 a Firimiyar Nigeria

Za a buga fafatawa 10 a wasannin mako na 30 a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria a ranar Laraba.

Kai tsaye
LMCNPFL

Za a gwada lafiyar Roberson a Liverpool

Kungiyar Liverpool za ta gwada lafiyar mai tsaron bayan Hull City, Andrew Robertson a ranar Alhamis domin shirin daukarsa kan kudi fan miliyan takwas in ji The Times.

Kai tsaye
Getty Images

Liverpool vs Crystal Palace

Liverpool za ta kara da Crystal Palace a wasan sada zumunta, kuma sabon dan kwallon da ta dauka Mohamed Salah zai buga mata karawar da Daniel Sturridge and Roberto Firmino.

Liverpool: Mignolet, Alexander-Arnold, Matip, Gomez, Moreno, Henderson, Lallana, Woodburn, Salah, Firmino, Sturridge.

Munich ta ci Arsenal

Arsenal 0-1 Bayern Munich

Munich ta ci Arsenal a bugun fenariti

Kai tsaye
Getty Images

James ya fara yi wa Munich wasa

Arsenal 0-0 Bayern Munich

Dan wasan da Bayern Munich ta dauka aro daga Real Madrid, James Rodriguez ya fara buga wa kungiyar tamaula a wasan sada zumunta da Arsenal.

Ga wasu 'yan wasan Munich Mats Hummels, Franck Ribery, Robert Lewandowski, Rafinha, Thomas Muller da David Alaba.

Suna buga wasan ne a Shanghai.

Fraizer Campbell ya sake komawa Hull City

Fraizer Campbell ya sake komawa Hull City kan jarjejeniyar shekara biyu bayan da Crystal Palace ta sallame shi.

Campbell, mai shekara 29, a baya ya taba taka-leda a kulob din a matsayin aro a kakar 2007-08.

Ya kuma zira kwallo 15, inda ya taimakawa Hull ta koma gasar Firimiya.

Sai dai ya ci kwallo daya kacal a wasa 13 da ya buga a Palace kafin kwantiraginsa ta kare a ranar 30 ga watan Juni.

Fraizer Campbell
Getty Images

Wa Real Madrid ta ke nema?

Har yanzu dai Real Madrid ba ta dauki wani dan wasa mai tsada sosai ba tun bayan bude kasuwar musayar 'yan kwallo ta Turai.

Sai dai an ta rade-radin cewa Madrid din na zawarcin dan wasan Monaco Kylian Mbappe da Pierre-Emerick Aubameyang na Borussia Dortmund.

Amma dai har yanzu babu wani labari game da wannan batu.

Kylian Mbappe
Getty Images

'Sai an biya ni fan 150,000 zan koma Tottenham'

Jaridar Daily Mirror da ake bugawa a Birtaniya ta ce dan wasan tsakiya na Everton Ross Barkley na bukatar albashin fan 150,000 a duk mako kafin ya koma Tottenham.

Sai dai kuma ta kara da cewa ita ma Everton na bukatar fam miliyan 50m kan dan kwallon na Ingila mai shekara 23.

Ross Barkley
Getty Images

Conte ne koci mafi tsada a tarihin Chelsea

Antonio Conte
BBC

Antonio Conte ya zama kociyan da aka fi biya a tarihin Chelsea.

Sabuwar yarjejeniyar shekara biyu da kociyan mai shekara 47 ya yi da kungiyar ta sa za a rinka biyansa fam miliyan 9.5 a ko wacce shekara.

A kakar da ta gabata ne kocin, dan Italiya, ya jagoranci kulob din ya lashe gasar Firimiya a shekararsa ta farko.

Sai dai har yanzu Jose Mourinho da Pep Guardiola na gabansa wurin daukar albashi.

An yi watsi da tayin Liverpool kan Kaita

Naby Kaita
Getty Images

An ki tayin da fam miliyan 66 da Liverpool ta yi kan Naby Kaita na kungiyar RB Leipzig da ke Jamus.

Kungiyar ta ce dan wasan ba na sayarwa ba ne.

Leicester City ta sayi golan Hull Eldin Jakupovic

Leicester City ta sayi mai tsaron gida daga Hull City, Eldin Jakupovic, kan yarjejeniyar shekara uku ba tare da bayyana kudin cinikin ba.

Dan wasan mai shekara 32 ya koma Hull City ne a shekarar 2012 kuma ya buga wasanni 22 a kakar bara lokacin da suka koma gasa ta kasa da Firimiya wato Championship.

Eldin zai fuskanci kalubale a Leicester daga mai tsaron gida na daya a kungiyar, Kasper Schmeichel, mai shekara 30.

Eldin Jakupovic
Getty Images

Newcastle da Crystal Palace 'ka iya taya Adrian'

Rahotanni a Ingila na cewa Newcastle da Crystal Palace na shirin taya golan West Ham Adrian, mai shekara 30, bayan da kulob dinsa ya sayi golan Ingila Joe Hart, a cewar jaridar Daily Mirror.

A jiya ne mai tsaron gidan na Manchester City, Hart, ya tafi West Ham a matsayin aro na shekara daya.

Golan West Ham Adrian
Arfa Griffiths

Alexis Sanchez ba na sayarwa ba ne - Wenger

Har ila yau kafar yada labarai ta Sky Sport ta rawaito kocin Aresenal Arsene Wenger yana cewa Alexis Sanchez, mai shekara 28, wanda Manchester City ke nema ba na sayarwa ba ne.

Ana dai rade-radin cewa dan kwallon na Chile na son barin Arsenal domin ya buga gasar zakarun Turai.

Alexis Sanchez
AFP

Arsenal za ta nemi Karim Benzema idan...

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal za ta yi kokarin sayen dan wasan gaba na Real Madrid Karim Benzema, idan har Alexis Sanchez ya barta a kakar bana, a cewar jaridar (Don Balon kamar yadda Daily Star ta rawaito).

A baya ma dai anyi rade-radin cewa Arsenal din za ta sayi dan wasan mai shekara 29.

Karim Benzema
Getty Images

Barkanmu da Hantsi

Jama'a barkanmu da sake saduwa a wannan shiri inda muke kawo muku wainar da ake tonawa a fagen wasanni, musamman ma hada-hadar cinikin 'yan kwallo a nahiyar Turai.