Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Real Madrid ta gabatar da Ceballos ga magoya baya
  2. AC Milan ta dauki Bonucci
  3. City da Chelsea na son daukar Danilo
  4. Mourinho na son karin dan wasa daya kacal
  5. PSG ta son tattaunawa da Barca kan sayen Neymar
  6. Chelsea za ta yi murna da sayen Morata - Nevin
  7. Shin Jack Wilshere ya kai fam miliyan 20?

Rahoto kai-tsaye

Daga Naziru Mikailu, Abdulwasiu Hassan da Mohammed Abdu

time_stated_uk

Nan muka kawo karshen shirin

Tare da fatan za ku tara a shirinmu na ranar Lahadi.

Madrid ta gabatar da Ceballos

Real Madrid ta gabatar da Dani Ceballos a gaban magoya bayanta a filin wasanta a Santiago Bernabeu na ranar Alhamis. A ranar 14 ga watan Julin 2017 Madrid ta sayi dan wasan daga Real Betis kan yarjejeniyar shekara shida.

Kai tsaye
Getty Images

An tuntubi Mbappe ta bayan gida - Monaco

Monaco ta zargi wasu kungiyoyin nahiyar Turai da yin magana da dan wasanta Kylian Mbappe ta bayan gida.

Kai tsaye
Getty Images

CAF ta kara kasashen da suke buga kofin Afirka

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afirka ta kara kasashen da za su fafatawa a gasar cin kofin nahiyar zuwa 24 da za a fara a wasannin da Kamaru za ta karbi bakunci a 2019.

Tun farko hukumar tana gudanar da gasar da kasashe 16, sai dai kuma ba ta fayyace ko za ta gusar da wasannin daga watan Janairu zuwa Fabrairu daga gudanarwa zuwa Yuni da Yuli ba.

Kai tsaye
Getty Images

A rana irin ta yau United ta taya Van Persie

A rana ta 19 ga watan Yuli kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson ya tabbatar da cewar yana zawarcin Robin van Persie kyaftin din Arsenal.

Daga baya ne dan wasan ya koma United ya kuma taka rawa a kakar da kungiyar ta lashe Premier a 2012/13.

Kai tsaye
Getty Images

Werder Bremen na son aron Martial

Werder Bremen na son ta dauki aron dan kwallon Manchester United Anthony Martial.

Kai tsaye
Getty Images

Liverpool za ta sake taya Keita

Jaridar The Mirror ta shirya taya mai wasan tsakiya na RB Leipzig, Naby Keita kan kudi fan miliyan 70, tun farko anki sammala tayin fan miliyan 66 da kungiyar ta yi wa dan wasan tawagar kwallon kafa ta Guine mai shekara 22.

Kai tsaye
Getty Images

Wa zai taka rawa tsakanin Morata da Lukaku da Lacazette

Cikin manyan 'yan wasa uku da suke cin kwallo da aka saya a gasar Premier tsakanin Alvaro Morata da Alexandre Lacazette da kuma Romelu Lukaku wa zai fi taka rawar gani a bana?

Kai tsaye
Getty Images

Juventus ta sayi Sciglio

Juventus ta kammala daukar Mattia de Sciglio mai shekara 24 daga AC Milan kan kudi fan miliyan 10.64.

Kai tsaye
Getty Images

AC Milan ta dauki Bonucci

AC Milan ta dauki Leonardo Bonucci Kungiyar AC Milan ta dauki Leonardo Bonucci kan kudi da ake cewa ya kai fan miliyan 40 daga Juventus.

Dan kwallon mai shekara 30, ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara uku da Milan wadda ta kashe fan miliyan 160 wajen sayo 'yan wasa a bana.

Kai tsaye
EPA

Damben gasar cin mota wasan daf da karshe

Za a fitar da jadawalin wasan daf da karshe a gasar cin mota wadda ake yi a Kanon Nigeria da yammacin Alhamis.

'Yan wasan da suka kai wasannin daf da karshe sun hada da Ali Kanin Bello daga Arewa da Bahagon Sanin Kurna daga Arewa da Dan Ali Shagon Bata isarka daga Kudu da Abdurrazak Ebola daga Kudu

Za kuma a buga wasan karshe da matsayi na uku a ranar Asabar a filin wasa na Kano Pillars da ke Sabon Garin Kanon Nigeria.

Kai tsaye
Getty Images
Dan Aliyu da Shagon Mada

Yadda tebur yake bayan mako na 30 a Firimiyar Nigeria

Kai tsaye
LMCNPFL

West Ham na daf da daukar aron Hernandez

West Ham na daf da daukar aron Hernandez West Ham United ta kusa dauko aron dan kwallon Bayer Leverkusen, Javier Hernandez domin ya buga mata wasa.

West Ham tana da tabbacin son daukar tsohon dan kwallon Manchester United mai shekara 29, amma ba a fayyace kudin da za ta biya ba.

Kai tsaye
Getty Images

Takaitatun labarin wasanni na Laraba

Takaitattun Labarin Wasanni 19072017

United za ta taya Aurier

Manchester United na son daukar matashin dan wasa mai shekara 24 dan wasan Paris St-Germain mai tsaron baya Serge Aurier, bayan da tattaunawa da United ke yi kan sayen Fabinho na Monaco ta ci tura in ji Independent.

Yadda guragu ke buga kwallo

Sakamakon wasan mako na 30 a Firimiyar Nigeria

Kai tsaye
LMCNPFL

Manchester City na neman Danilo?

Danilo da Ronaldo
Getty Images

Jaridar Guardian ta Birtaniya ta ce Manchester City na son sayen dan wasan bayan Real Madrid Danilo, wanda dan kasar Brazil ne.

Kudin cinikin dan kwallon ka iya kai wa fan miliyan 26 da rabi.

Chelsea za ta yi murna da sayen Morata - Nevin

Tsohon dan wasan Chelsea Pat Nevin ya ce magoya bayan kulob din za su zuba ruwa a kasa su sha bayan da suka sayi Alvaro Morata.

Morata, mai shekara 24, zai tattauna kan yarjejeniyar da zai sa hannu sannan a gwada lafiyarsa a cinikin da zai kai fam miliyan 60.

Alvaro Morata
Getty Images

Neymar ba na sayarwa ba ne - Bartomeu

Jaridu da dama na rawaito cewa Paris St-Germain a shirye suke su tattauna da Barcelona kan sayen Neymar a farashin da ka iya kai wa fan miliyan 196.

Sai dai Shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu ya shaida wa BBC cewa dan kwallon na Brazil, mai shekara 25 ba na sayarwa ba ne.

Neymar
Getty Images

Shin Jack Wilshere ya kai fam miliyan 20?

Jaridar Daily Star ta Ingila ta ce Arsenal ta shaida wa West Ham cewa dole su biya fam miliyan 20 in har suna son su sayi dan wasan tsakiya, Jack Wilshere.

Dan shekara 25 wanda ya yi zaman aro a Bournemouth akakar da ta gabata, yana samun sauki daga karayar kafar da ya yi.

Jack Wilshere
Getty Images

West Ham na neman Javier Hernandez

Javier Hernandez
Getty Images

West Ham na fatan sayen tsohon dan wasan gaba na Machester United Javier Hernandez, mai shekara 29, daga Bayer Leverkusen, in ji kafar yada labarai ta Sky Sport.

Liverpool za ta biya 'fam miliyan 70' kan Kaita

Jaridar Daily Mirrow ta rawaito cewa Liverpool a shirye ta ke ta biya fan miliyan 70 da kulob din RB Leipzig ya nema domin sayen Naby Keita.

Tuni dai aka yi watsi da tayin fan miliyan 66 da ta yi wa dan kwallon na Guinea mai shekara 22.

Naby Keita
Getty Images

Chelsea na son fam miliyan 44 kan Costa

Jaridar Independent ta rawaito cewa Chelsea na ci gab bada jajircewa kan neman sayan Diego Costa da Atletico Madrid ke yi.

Chelsea ta dage sai an biya ta fam miliyan 44 kan dan kwallon mai shekara 28.

Tuni dai zakarun Firimiyar suka cimma yarjejeniyar sayan Alvaro Morata, mai shekara 24, daga Real Madrid.

Diego Costa
AFP

PSG ta son tattaunawa da Barca kan Neymar

Paris St-Germain ta shirya domin fara tattaunawa da Barcelona kan yarjejeniyar fam miliyan 196 don sayan Neymar, dan asalin Brazil mai shekara 25 wanda a yanzu yake taka-leda a Barca.

Barca dai ta nace cewa dan wasan ba na sayarwa ba ne.

Neymar
Getty Images

Dan wasa daya nake so - Mourinho

Kociyan Manchester United Jose Mourinho, ya ce bisa ga dukkan alamu dan wasa daya ne kawai zai iya saya kafin a rufe kasuwar hada-hadar 'yan wasa ta bana.

Dan asalin kasar Portugal din ya nun cewar kulob-kulob suna tsawwala kudade kan 'yan kwallo. Mourinho ya ce: " Ba mu shirya wa biyan irin kudin da kulo-kulob suke nema ba."

Kociyan, wanda ya riga ya sayi 'yan wasa biyu a wannan lokacin bayan ya nemi United ta sayi hudu, ya ce: "Na saba da ganin kulob-kulob suna biyan makudan kudade ga manyan 'yan wasa.

A yanzu kowa yana biyan makudan kudade ga 'yan wasa masu kyau."

Kociyan Manchester United Jose Mourinho
Getty Images

Barkanmu da Hantsi

Jama'a barkanmu da sake saduwa a wani sabon filin, inda muke kawo muku labarai kan wainar da ake tonawa a fagen wasanni.