Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. City ta dauki dan wasa na biyar a bana
  2. Man Utd ta doke Real Madrid a bugun fanareti
  3. Messi da Suarez sun shawo kan Neymar 'ya zauna a Barcelona'
  4. Roma na neman Riyad Mahrez
  5. Real Madrid ta ci ribar sayar da 'yan zaman benci

Rahoto kai-tsaye

time_stated_uk

Wakar Jafaru - Hussaini dan mai kotso

Damben gargajiya

Ya kamata Martial ya jajirce - Mourinho

Kocin Manchester United, Jose Mourinho ya bukaci Anthony Martial ya zama yana kan ganiyarsa a koda yaushe.

Latsa nan domin ci gaba da karanta labarin

Kai tsaye
Getty Images

Juventus na son taya Mangala

Kungiyar Juventus na son ta taya mai tsaron bayan Manchester City, Eliaquim Mangala, bayan da ta sayar da Leonardo Bonucci. An ce Juventus din na son taya dan kwallon kan fan miliyan 20.

An tsawaita hukuncin dakatar da Bailly

Dan kwallon Manchester United, Eric Bailly ba zai bugawa kungiyar wasa uku ba, sakamakon jan kati da aka yi masa a karawa da Celta Vigo a gasar Europa League.

Latsa nan domin ci gaba da karanta labarin

Kai tsaye
Reuters

Spieth zai kara daura damara

Jordan Spieth ya ce bai fuskanci kalubale wajen lashe gasar kwallon golf da aka kammala a Royal Birkdale ba, inda hakan ya sa ya kara cin kofi bayan na kwararru da na US Open.

Southampton ba ta je Amurka da Van Dijk ba

Kungiyar Southampton ba ta je Faransa wasan atisaye da Virgil Van Dijk ba, bayan da ta bar shi a gida.

Ana alakanta cewar kungiyoyi da yawa na zawarcin Van Dijk kan kudi mai tsoka.

Wasu rahotanni na cewa Liverpool ta daina batun son daukar dan kwallon wanda ta fara zawarci tun da aka bude kasuwar bana, inda a lokacin ake cewa Southampton za ta yi karar Liverpool kan ta tuntubi dan wasan ta bayan gida.

Latsa nan don karanta labarin

Kai tsaye
Getty Images

Za a yi wa Pedro fuskar roba

Kocin Chelsea Antonio Conte ya tabbatar da cewar mai buga masa wasan tsakiya Pedro ya yi rauni a lokacin da ya yi taho mu gama da mai tsaron ragar Arsenal, David Ospina, a wasan sada zumunta da suka yi a Beijing. Conte ya ce yana sa ran Pedro zai dawo atisaye nan da kwana 10 tare da fuskar roba da za a kera masa.

Kai tsaye
Getty Images

Mendy ne mai tsaron baya mafi tsada

Manchester City ta kashe sama da fan miliyan 200 wajen sayen kwallo a bana, bayan da Benjamin Mendy daga Monaco ya kammala komawa Ettihad a ranar Litinin. Dan wasan tawagar Faransa da City ta saya kan fan miliyan 52 ya zama mai tsaron baya da aka dauka mafi tsada a duniya a bana.

Kai tsaye
Getty Images

Takaitattun Labarin wasanni na safiyar Litinin

Takaitattun Labarin wasanni a safiyar Litinin 24072017

Boxing

An fara sayar da tikitin damben Mayweather da McGregor

Sauran kasa da wata daya a dambata tsakanin Floyd Mayweather da Conor McGregor a karawar da masu son dambe ke son gani a duniya.

An fara sayar da tikitin kallon dambatawar a Intanet a ranar Litinin da wasu wuraren a Las Vegas. Karawar da za a yi ta a cikin watan Agusta, za a kalli damben daga tsakanin dala 500 zuwa 10,000.

Haka kuma akwai tikitin dala 1,500 da 2,500 da 3,500 da 5,000 da kuma 7,500. An kuma takaita cewar tikiti biyu za a bai wa gidan da suke da yawa domin kallon karawar.

Kai tsaye
Getty Images

Teburin gasar Firimiya bayan mako na 31

Kai tsaye
LMCNPFL

Sakamakon mako na 31 a gasar Firimiyar Nigeria

Mountain of Fire ta ci Katsina United 3-2 a wasan mako na 31 da suka karasa a safiyar Lahadi.

Kai tsaye
LMCNPFL

Ko Wilshere zai koma Turkiya kuwa?

Daily Mail ta wallafa cewar kulob din Turkiya Antalyaspor na kokarin daukar dan wasan Arsenal, Jack Wilshere, sai dai shugaban kulob din ya ce Arsenal ta saka buri kan dan kwallon.

Kai tsaye
Getty Images

Inter za ta dauki Vidal

Inter na son taya Arturo Vidal kan kudi fan miliyan 50 in ji La Gazzetta, koda yake Bayern Munich ta ce ba ta shirya sayar da dan wasan ba.

Kai tsaye
Marca

Liverpool za ta sake taya Keita

Sky Sports ta ce Liverpool za ta sake taya dan kwallon RB Leipzig, Naby Keita tun farko anki sallama mata dan wasan kan tayin fan miliyan 70 da ta yi.

Kai tsaye
Getty Images

Koscielny zai ci gaba da wasa a Emirates

Zan ci gaba da zama daram a Arsenal - Koscielny

Ina da yarjejeniyar buga wa Arsenal tamaula shekara da yawa, kuma banga dalilin da zai sa na bar Gunners ba

Laurent Koscielny
Kai tsaye
Getty Images

Sanchez zai yi zamansa a Arsenal

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce Alexis Sanchez bai nemi ya bar kungiyar a bana ba, saboda haka yana sa ran zai ci gaba da wasanninsa a Emirtaes.

Kai tsaye
Getty Images

Southampton ta bar Van Dijk a gida

Southampton ba ta sanya sunan kyaftin dinta Virgil van Dijk a jerin 'yan wasan da za ta tafi da su atisayi Faransa a wannan makon ba.

Kocin kulob din Mauricio Pellegrino ya fada a makon da ya gabata cewa Van Dijk na yin atisayi shi kadai saboda dan kwallon ba shi da tabbas kan makomarsa kuma hankalinsa a rabe ya ke.

Virgil van Dijk
Getty Images

Man City ta kashe fan miliyan 201...

Kawo yanzu Manchester City ta kashe fan miliyan £201.5 kan sabbin 'yan wasa a bana

  • Kyle Walker (Tottenham) - £45m
  • Bernardo Silva (Monaco) - £43m
  • Ederson Moraes (Benfica) - £35m
  • Danilo (Real Madrid) - £26.5m
  • Benjamin Mendy (Monaco) - £52m
Benjamin Mendy
Getty Images
Benjamin Mendy ya bugo kwallo daga gefe (crossing) sau 57 a gasar zakarun Turai ta bara fiye da kowane dan wasa

Man City ta dauki Benjamin Mendy

Benjamin Mendy
Getty Images

Manchester City ta kammala sayen mai tsaron baya na Monaco, Benjamin Mendy kan kudi fan miliyan 52 kuma na biyar da ta dauka a bana.

Dan wasan mai shekara 23, wanda ya koma Monaco daga Marseille a bara ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar.

Mendy shi ne dan kwallo na biyar da City ta dauka a bana, wanda ta kashe fan miliyan 200 wajen sayo 'yan wasan

Za mu rike Neymar duk runtsi — Valverve

Kociyan Barcelona, Ernesto Valverde ya ce za su hana Neymar barin kungiyar a bana, bayan da dan wasan ya ci kwallo biyu a karawa da Juventus a wasan sada zumunta.

An ce Paris St-Germain za ta biya Yuro miliyan 222 kudin ka'ida da Barca ta ajiye idan wani kulob din na son daukar dan kwallo kafin yarjejeniyarsa ta kare a Camp Nou.

Sai dai kuma shugaban Barcelona, Josep Maria Bartomeu ya shaidawa sashen wasanni na BBC cewar ba za su sayar da Neymar mai shekara 25 ba.

Neymar
Getty Images

Babu inda Ronaldo zai je - Zidane

Jaridar Independent ta rawaito cewa kocin Real Madrid, Zinedine Zidane, ya hakikance cewar Cristiano Ronaldo zai ci gaba da taka-leda a kungiyar duk da rahotonnin da ake cewar zai bar Spaniya sakamakon zargin kin biyan haraji da ake yi masa.

Ronaldo ya musanta aikata kowanne irin laifi game da batun.

Cristiano Ronaldo
Getty Images

Thomas Sorensen ya yi ritaya daga kwallo

Thomas Sorensen ya yi ritaya.
AFP

Tsohon golan Sunderland da Aston Villa da kuma Stoke Thomas Sorensen ya yi ritaya.

Dan kwallon na kasar Denmark ya ajiye takalmansa ne yana da shekara 41.

Ya fada a shafinsa na Instagram:

"Ina alfahari da kuma bakin ciki a lokaci guda, cewa a yau na sanar da yin ritaya daga tamaula... Ina godiya da gudummawar da kuka ba ni."

Sorensen yana taka leda ne a Melbourne City tun shekara ta 2015 kuma yana da aniyar cigaba da zama a Australia.

Chelsea za ta matsa kaimi kan Alex Chamberlain

Alex Oxlade-Chamberlain da Conte da Guardiola
Getty Images

Chlesea za ta kara matsa kaimi wajen neman sayan dan wasan tsakiyar Arsenal mai shekara 23 Alex Oxlade-Chamberlain a wannan makon, amma za ta iya fuskantar kalubale dage Manchester City, acewar jaridar

Manchester Utd ta doke Real Madrid a bugun fanareti

Manchester United ta doke Real Madrid a bugun fanareti bayan sun tashi a wasan gabannin kakarsu da ci 1-1 a Santa Clara.

Anthony Martial ne ya bai wa Jesse Lingard damar fara ci wa United kwallo daga gefen hagu.

Casemiro ya daukar wa Real Madrid fansa a bugun fenareti bayan sabon mai tsaron bayan United, Victor Lindelof, ya kayar da Theo Hernandez.

A bugun fanaretin da aka yi na raba gardama bayan an tashi wasan kunnen doki, an barar da fanareti 7 daga cikin 10 inda United ta doke Real Madrid da ci 2-1.

Daren wasan bai yi wa Lindelof kyau ba, domin ya kara barar da fenareti bayan ya janyo fenaretin da ya sa Madrid ta rama kwallon da aka zira mata.

Wani labari mara dadi ga United kuma shi ne ficewar Ander Herrera wanda ya ji ciwo a kugu bayan ya buga wasan minti shida kacal.

Jesse Lingard
Getty Images
Jesse Lingard ya ci wa United kwallo na farko a wani wasan da za a sake maimaitawa a gasar European Super Cup ranar 8 ga watan Agusta

Real Madrid ta ci ribar sayar da 'yan zaman benci

Real Madrid na ci gaba da karfafa kungiyar wajen shigar da matasan 'yan kwallo, domin tunkarar kakar wasanni da za a fara a cikin watan Agustan nan.

Tuni Madrid din a kokarin da take na ganin ta taka rawar gani a fafatawar da za a fara, ta sayar da 'yan wasanta masu zaman benci kan kudi Yuro miliyan 110.

Real din ta sayar da Alvaro Morata da Danilo sannan ta bai wa Bayern Munich aron James Rodriguez domin ya buga mata tamaula shekara biyu, daga nan ta sayi dan wasan idan ya yi mata.

Chelsea ce ta sayi Morata kan kudi Yuro miliyan 80, wanda ya sa Real ta ci ribar Yuro miliyan 50 dan kwallon da ta dauka a Juventus kan Yuro miliyan 30.

Masu zaman benci da Real ta sayar a kakar bana
MARCA

Ita kuwa Manchester City ta sayi Danilo kan Yuro miliyan 30 kuma kudin da Madrid ta dauko dan wasan daga Porto.

Bayern Munich kuwa ta biya Madrid kudin daukar Rodriquez da zai buga mata wasanni aro, idan kuma ta ce za ta saye shi bayan shekara biyu, za ta biya Madrid Yuro miliyan 50.

Daga karshe Real ta sayarwa da Lyon matashin dan wasanta Mariano Diaz kan Yuro miliyan 10. Real ta ci ribar sayar da 'yan zaman benci.

Roma 'ta tattauna da Riyad Mahrez'

Riyad Mahrez
Getty Images

Rahotanni daga Italiya na cewa an yi tattaunawa tsakanin dan wasan gefe na Leicester City Riyad Mahrez da kuma AS Roma.

Sai dai har yanzu Leicester na nuna rashin amincewa da tayin fan miliyan 30 kan dan kwallon mai shekara 26.

PSG da Arsenal 'sun dakatar da tattaunawa kan Sanchez'

Jaridar Le Parisien ta Faransa ta rawaito cewa an dakatar da tattaunawa kan batun komawar Alexis Sanchez zuwa PSG daga Arsenal bayan an kasa cimma matsaya game da farashin dan kwallon.

Dan kwallon mai shekara 28 na son barin Arsenal kafin yarjejeniyarsa ta kare a badi.

Sanchez da Wenger
Getty Images

Messi da Suarez sun shawo kan Neymar?

Jaridar Sport ta wallafa bayanan da ta ce ta samu wadanda suka tabbatar mata da cewa dan kwallon Brazil Neymar, ya shaida wa abokan wasansa Lionel Messi da Luis Suarez cewa zai ci gaba da zama a Barcelona.

Ta kara da cewa 'yan wasan biyu ne suka shawo kan dan kwallon, mai shekara 25, ka da ya koma Paris St-Germain a kan kudi fam miliyan 200.

Neymar da Lionel Messi da Luis Suarez
Getty Images

Ko Coutinho zai bar Liverpool?

Philippe Coutinho
Getty Images

Daily Mirror ta rawaito cewar a shirye Barcelona take ta sayi Philippe Coutinho daga Liverpool kan kudi fan miliyan 80.

Ita kuwa Daily Mail cewa ta yi Barcelona ta hakikance cewar idan ta dauko Coutinho daga Liverpool zai taimaka Neymar wanda PSG ke zawarci ya ci gaba da zama a Camp Nou.

Barkanmu da hantsi

Jama'a barkanmu da sake saduwa a filin na yau inda za mu ci gaba da kawo muku bayanai kan wainar da ake tonawa a fagen wasanni.