Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Shin 'yan wasa nawa Chelsea ta dauka
 2. Barcelona ta ci Man United 1-0
 3. Liverpool ta tsuga kudi kan Coutinho
 4. City ta lallasa Real Madrid da ci 4-1

Rahoto kai-tsaye

time_stated_uk

Nan muka kawo karshem shirin

Da fatan za ku tara a ranar Ltinin domin jin wani sabon shirin labaran wasanni

Allardyce - Kudin da ake sayen 'yan wasa na sa matsi ga koci

Tsohon kocin tawagar kwallon kafa ta Ingila Sam Allardyce ya ce tsabagen kudin da ake sayen 'yan wasan tamaula na kara matsi ga mai horar da kwallon kafa.

Sama da fan miliyan 850 aka kashe wajen sayen 'yan kwallon da za su buga gasar Premier daga kasuwar da za ta daina ci a tsakar daren 31 ga watan Agusta.

Allardyce mai shekara 62 ya yi murabus daga horar da Crystal Palace a watan Mayu, inda ya ce kungiyoyi na dora buri kacokan ga koci.

Kai tsaye
Reuters

Har yanzu PSG na neman Neymar

L'Equipe ta ce Paris St Germain nada tabbacin za ta kammala daukar Neymar daga Barcelona kan kudi fan miliyan 198 nan da kwana 15.

Kai tsaye
Getty Images

Allardyce zai dawo horar da tamaula

Tsohon kocin tawagar kwallon kafar Ingila, Sam Allardyce ya shaidawa BBC cewar zai dawo horar da tamaula nan gaba.

Allardyce ya yi ritaya daga jan ragamar Crystal Palace bayan da ya haurar da kungiyar daga siratsi.

Kai tsaye
Getty Images

'Yan wasan da Chelsea ta dauka a bana

Wadan da ta dauka: Willy Caballero (Manchester City,) Rudiger (Roma kan Yuro miliyan), Bakoyoko (Monaco, Yuro miliyan 40), Morata (Real Madrid, fan miliyan 60)

Wadan da suka barta: Ake (Bournemouth, Yuro miliyan 23), Cuadradoundefined(Juventus, Yuro miliyan), Begovic (Bournemouth, Yuro miliyan 11.5), Bertrand Traore (Olympique Lyon, Yuro miliyan 10), Atsu (Newcastle, Yuro miliyan 7.5), Solanke (Liverpool, yarjejeniya ce ta kare), Terry (Aston Villa, yarjejeniya ce ta kare), Abraham (Swansea, aro), Aina (Hull, aro), Loftus-Cheek (Crystal Palace, aro), Chalobah (Watford, Yuro miliyan 5.7), Van Ginkel (PSV, aro), Zouma (Stoke, aro)

Kai tsaye
Getty Images

Har yanzu City na son daukar Mbappe

Daily Mail ta ce koci Pep Guardiola ya ce Manchester City tana da kudin da za ta kalubalanci Real Madrid kan daukar Kylian Mbappe na Monaco.

Kai tsaye
Getty Images

Za a ci gaba da Firimiyar Nigeria a ranar Lahadi

Wasan mako na 32

Kai tsaye
LMCNPFL

Barca za ta maye gurbin Neymar da Coutinho

Talksport ta ce Barcelona za ta dauki Philippe Coutinho daga Liverpool domin maye gurbin Neymar idan ya koma PSG.

Kai tsaye
Reuters

Golan Watford ya tsawaita zamansa

Mai tsaron ragar Watford, Heurelho Gomes ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyu a kungiyar.

Golan mai shekara 36 ya buga wa kungiyar wasa sama da 100 tun lokacin da ya koma kungiyar a 2014.

Real za ta bai wa United Bale

Jaridar Independence

Independence ta ce idan har Real Madrid ta dauki Kylian Mbappe daga Monaco, za ta sayarwa da Manchester United, Gareth Bale.

Kai tsaye
Getty Images

Dan Moyi mawakin damben gargajiya

Wakar da ya yi wa Shamsu Kanin Emi dan wasan Arewa

Football

Shugaban hukumar kwallon kafar Spaniya, Angel Maria Villar ya yi ritaya daga mukamin mataimakin shugabancin hukumar kwallon kafa ta Turai da na mataimakin Fifa.

A farkon watan nan jami'an tsaro suka damke Villar kan zargin almubazzaranci da rubuta takardun jabu.

Sai dai kuma ya karyata zargin da ake yi masa, amma ba zai sake jagoranci hukumomin ba.

Tottenham ba ta dauki dan wasa ba

Bayan da Tottenham ta yi ta biyu a gasar Premier da aka kare, har yanzu kungiyar ba ta dauki dan wasa ko daya ba.

Kungiyar za ta buga gasar cin kofin zakarun Turai da za a yi a bana.

Tottenham ta sayar da mai tsaron bayanta Kyle Walker ga Manchester City kan kudi fan miliyan 45.

Kai tsaye
AFP

Froome zai shiga tseren Vuelta

Chris Froome ya tabbatar da cewar zai fafata a tseren kekuna da za a yi a Vuelta ta Espana, bayan da ya ci Tour de France ta shekarar nan ta uku a jere ta hudu jumulla.

Kai tsaye
BBC Sport

Kalas ya tsawaita zamansa a Chelsea

Tomas Kalas ya tsawaita zamansa a Stamford Bridge zuwa shekara hudu, sai dai kuma Chelsea ta sake bayar da shi aro ga Fulham.

Tomas Kalas has signed a new four-year deal with Chelsea - and gone out on loan again 👉 bbc.in/2v0d3c9

Tomas Kalas has signed a new four-year deal with Chelsea - and gone out on loan again 👉 bbc.in/2v0d3c9

AC Milan na son daukar Costa

Kungiyar AC Milan na son ta sayi Diego Costa na Chelsea, kafin ta dauki Nikola Kalinic daga Fiorentina.

Sai dai Costa ya fi son ya koma Atletico Madrid.

Kai tsaye
Getty Images

Kun san 'yan wasan da Man City ta dauka?

Manchester City ta kashe sama da fam miliyan 200 a lokacin bazarar nan domin tunkarar kakar wasa ta bana.

'Yan wasan da City ta saya sun hada da:

 • Kyle Walker (fam miliyan 45)
 • Bernardo Silva (fam miliyan 43)
 • Ederson Moraes (fam miliyan 43)
 • Benjamin Mendy (fam miliyan 52)
 • Danilo (fam miliyan 26.5)
Kyle Walker
get

Za a raba jadawalin WAFU Cup 2017

Za a raba jadawalin gasar WAFU Cup ta bana a ranar Alhamis a otal din Labadi beach da ke Accra, Ghana.

Za a fara wasannin tsakanin 9 zuwa 24 ga watan Satumbar 2017 a filin wasa na Sekondi.

Ga kasashen da za su kara a gasar:

Benin

 • Burkina Faso
 • Cape Verde
 • Ivory Coast
 • Gambia
 • Ghana
 • Guinea
 • Guinea Bissau
 • Liberia
 • Mali
 • Mauritania
 • Niger
 • Nigeria
 • Senegal
 • Sierra Leone
 • Togo

Rooney zai buga wa Everton gasar Europa

Wayne Rooney ya ce a koda yaushe yana dokin buga wa Everton wasa a gasar Zakarun Turai ta Europa.

Everton za ta buga wasan cike gurbi da MFK Ruzomberok ta Slovakia a Goodison Park a yammacin Alhamis.

Rooney mai shekara 31, zai buga wa Everton karawar a karon farko tun bayan da ya bar kungiyar sama da shekara 13 ya koma Manchester United.

Ya koma United da taka-leda yana da shekara 18 kan kudi fan miliyan 27 a shekarar 2004.

Kai tsaye
EPA

Takaitattun Labarin Wasanni

Takaitattun Labaran Wasanni 27072017

Barcelona ta ci Manchester United 1-0

Barcelona ta ci Manchester United daya mai ban haushi a gasar International Champions Cup da suka fara a filin wasa na Levi da ke Amurka. Neymar ne ya ci kwallon.

Kai tsaye
Marca

Ko Bale zai koma Manchester United?

Yunkurin Real Madrid na sayan dan wasan gaba na Monaco, Kylian Mbappe, mai shekara 18 ka iya sa dan wasanta na gefe Gareth Bale, ya koma Manchester United, in ji jaridar Independent.

An dade ana hasashen dan wasan na Wales, mai shekara 28, na son komawa United, amma ya bayyana cewa a shirye yake ya ci gaba da zama a Madrid.

Gareth Bale
Getty Images

Swansea na neman Chris Wood na Leeds

Swansea City tana zawarcin dan wasan gaba na Leeds United, Chris Wood, amman tana fuskantar gogayya daga wasu kungiyoyin Firimiya biyu kan sayan dan wasan mai shekara 25, in ji jaridar Wales Online.

Yadda Man City ta lallasa Real Madrid

Manchester City ta lallasa Real Madrid da ci 4-1 a Los Angeles a wasan sada zumunci da suka buga domin shirin tunkarar kakar wasa ta bana.

Kociya n City Pep Guardiola ya ce Benjamin Mendy wanda ya saya kan kudi fam miliyan 52 ba zai taka leda na mako biyu ba bayan wasan na Amurka.

Mutun 93,000 ne suka kalli yadda City ta samu nasararta ta farko a wasannin shirin sabuwar kaka da kwallaye daga Nicolas Otamendi da Raheem Sterling da John Stones da kuma dan shekara 17, Brahim Diaz.

Man City da Real Madrid
Getty Images

A rashin Mendy, Danilo ya buga wasansa na farko a filin wasan Los Angeles Memorial Coliseum, inda mai shekara 26 din wanda dan asalin kasar Brazil ne ya buga baya ta gefen hagu.

Ya dai fuskanci tsohon kulob dinsa bayan Man City ta saye shi kan kudi fam miliyan 26.5.

PSG na da kwarin gwiwa kan sayen Neymar

Paris St-Germain na da karfin guiwar kammala yarjejeniyar Fam miliyan 198 na sayan Neymar daga Barcelona a cikin kwanaki 15 masu zuwa, in ji jaridar L'Equipe ta kasar Faransa.

Sai dai Barcelona ba ta so ta sayar da dan kwallon na Brazil.

Kuma wasu rahotanni sun ambato shi yana shaida wa abokan wasansa cewa zai ci gaba da zama a Barcelonar.

Neymar
Getty Images

Liverpool ta tsuga kudi kan Coutinho

Jaridar Daily Mirror ta rawaito cewa Liverpool ta sanya farashin fan miliyan 133 kan dan wasan gaba na Brazil Philippe Coutinho.

Barcelona ce rahotanni suka nuna tana neman dan kwallon mai shekara 25.

Sai dai Liverpool ta ce ba a shirye take ta sayar da shi ba.

Coutinho na cikin 'yan wasan da Liverpool ke ji da su.

Philippe Coutinho
Getty Images

Barkanmu da rana

Jama'a barkanmu da sake saduwa a wani sabon shirin, inda muke kawo muku wainar da ake tonawa a fagen wasanni, musamman musayar 'yan kwallo a nahiyar Turai.

Muna neman afuwa saboda rashin fara kawo muku wadannan labarai da wuri kamar yadda muka saba.

Wasu 'yan matsaloli suka sha kanmu.