Takaitacce

 1. Coutinho ba zai bar Liverpool ba - Klopp
 2. United ta kammala sayen Matic
 3. An dakatar da Phil Jones buga wasa biyu
 4. Barcelona za ta yi karar PSG
 5. Ronaldo ya gurfana a gaban kuliya kan haraji
 6. Sanchez zai fara atisaye ranar Talata
 7. Madrid za ta yi wasa shida a watan Agusta
 8. Arsenal ta lashe Emirates Cup na bana
 9. Hamilton ya yi na hudu a tseren Hungarian Grand Prix

Rahoto kai-tsaye

time_stated_uk

Rudisha ba zai shiga gasar tseren Landan ba

Zakaran tseren mita 800, David Rudisha, ba zai buga gasar wasannin tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya ba, sakamakon raunin da ya yi.

Dan wasan na kasar Kenya mai shekara 28, ya ce a shafinsa na twitter ya yi matukar bakin-ciki da takaici, da ba zai halarci wasannin da za a fara daga 4 zuwa 13 ga watan Agusta a Landan ba.

A shekarar 2012 ne ya lashe lamabar zinare a gasar Olympiccs da aka yi a Landan, da kuma wacce aka yi a Rio din Brazil a shekarar da ta gabata.

Kai tsaye
Getty Images

Uganda ta nada masu horar da tamaula

Hukumar kwallon kafa ta Uganda (Fufa), ta nada Moses Basena da Fred Kajoba, a matsayin masu horor da tawagar kwallon kafar kasar a matsayin rikon kwarya.

Masu horarwar sun maye gurbin Milutin 'Micho' Sredojevic, wanda ya yi murabus tun kafin kwantiraginsa ya kare kan rashin biyansa albashi a ranar Asabar.

Hukumar ta tabbatar da cewa tsohon kocin dan kasar Serbia na bin ta bashin dala 54,000, kuma tace ta fara shirin biyansa.

Sredojevic shi ne wanda ya ja ragamar tawagar kwallon Uganda tun daga 2013, inda ya kai ta gasar kofin nahiyar Afirka karon farko tun bayan 1978.

Kai tsaye
BBC

Dambe tsakanin Nuran Dogon Sani da Shagon Abata Mai

Da suka dambata a Abuja, Nigeria a safiyar Lahadi

Man United ta kammala daukar Matic

Manchester United ta kammala daukar Nemanja Matic daga Chelsea kan kudi fan miliyan 40 kan yarjejeniyar shekara uku.

Matic mai shekara 28, shi ne na uku da United ta dauka a bana, bayan Victor Lindelof daga Benfica kan fam miliyan 31 da Romelu Lukaku kan fam miliyan 75 daga Everton.

Mourinho ya taba sayen Matic kan fan miliyan 21 daga Benfica a Janairun 2014 zuwa Chelsea.

Kai tsaye
Getty Images

An dakatar da Jones buga wasa biyu

An dakatar da dan wasan Manchester United, Phil Jones daga buga wasa biyu, bayan da aka sameshi da laifin fadawa jami'an hukumar Turai bakaken kalamu.

Hukumar kwallon kafa ta Turai ce ta samu dan wasan da laifin furta munana kalamai da kin bayar da hadin kai ga jami'an hukumar kula da gwajin shan abubuwa masu kara kuzari.

Haka kuma hukumar ta ci tarar Manchester United fam 8,900 da kuma Jones mai tsaron baya da zai biya fam 4,450.

Shi kuwa dan kwallon United, Daley Blind an tuhumeshi da laifin karya dokar kula da shan abubuwa masu kara kuzarin wasa, sai dai an ci tararsa fam 4.450 kawai.

Hukumar ta hukunta Jones da tuhumar Blind a wasan karshe da United ta ci kofin Europa bayan da ta doke Ajax.

Jones, ba zai buga Uefa Super Cup da Manchester United za ta kara da Real Madrid a ranar 8 ga watan Agusta ba. Haka kumaa ba zai buga wasan farko da United za ta yi a gasar cin kofin Zakarun Turai.

Kai tsaye
Getty Images

Fulham ta dauki Kamara

Kungiyar Fulham ta dauki Aboubakar Kamara daga Amiens ta Faransa kan yarjejeniyar shekara hudu.

Takaitatun Labaran wasanni

Takaitattun Labarin Wasanni daga Sashen Hausa na BBC

Ingila ta kai wasan daf da karshe

Tawagar kwallon kafa ta mata ta Ingila ta kai wasan daf da karshe a gasar cin kofin nahiyar Turai, bayan da ta ci Faransa daya mai ban haushi.

Jordie Taylor ce ta ci kwallon kuma na biyar da ta zura a raga a gasar, wanda ya bai wa Ingila nasarar cin Faransa a karon farko tun shekara 43.

Ingila za ta buga wasan daf da karshe da Netherlands a ranar Alhamis.

Kai tsaye
BBC

Mahrez zai koma Roma

Jaridar Corriere dello Sport ta ce an cimma yarjejeniya tsakanin Leicester City da Roma a kan daukar Riyad Mahrez, inda dan wasan tawagar kwallon Algeria zai je can domin a duba lafiyarsa.

Kai tsaye
Getty Images

Teburin gasar Firimiyar Nigeria bayan mako 32

Kai tsaye
LMCNPFL

Har yanzu Tottenham ba ta sayi dan kwallo ba

Kocin Tottenham, Mauricio Pochettino ya ce an bar su a baya wajen sayen 'yan kwallo domin tunkarar wasannin bana, amma yana kokari domin ya sayo 'yan kwallo in ji Evening Standard.

Kai tsaye
PA

Sakamakon Firimiyar Nigeria mako na 32

Kai tsaye
LMCNPFL

Everton ba za ta sallama Barkley ba

Jaridar Daily Mail

Jaridar Daily Mail ta ce Everton na shirin kin amincewa da tayin fan miliyan 35 da za ayi wa Barkley, duk da cewa kwantiraginsa zai kare kafin nan da wata 12.

Kai tsaye
BBC Sport

'Batun Sanchez ba zai shafi shirye-shiryenmu ba'

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce rashin sanin makomar Alexis Sanchez a kungiyar ba zai shafi shirin da yake na tunkarar wasannin bana ba.

A karshen kakar da za a fara a bana yarjejeniyar Sanchez dan kwallon tawagar Chile za ta kare a Gunners, kuma kungiyoyi da dama na zawarcin dan kwallon.

Kai tsaye
Empics

Barcelona za ta yi karar PSG

Barcelona na sa ran Neymar zai koma atisaye a ranar Laraba, amma a shirye take ta yi karar Paris St-Germain idan har ta biya Yuro miliyan 222 kudin ka'ida da ta saka ga duk kungiyar da ke son daukar dan wasan Brazil din.

Ana alakanta Neymar dan wasan Brazil mai shekara 25, da cewar zai koma buga gasar kwallon Faransa, kuma a ranar Talata ya kamata ya koma Spaniya daga China.

Rahotanni na cewa dan kwallon zai je Qatar a makonnan domin PSG ta duba lafiyarsa. A makon jiya shugaban kungiyar Barcelona, Josep Maria Bartomeu ya ce Neymar zai ci gaba da taka-leda a Camp Nou a bana.

Kai tsaye
Getty Images

Jesus zai sake komawa Sevilla

Rahotanni daga Spaniya na cewa Sevilla za ta sake dawo da Jesus Navas kungiyar daga Manchester City kan yarjejeniyar shekara uku da sharadin za a iya tsawaita zamansa zuwa shekara daya kuma, amma idan ya buga wasa akai-akai a 2019/20.

Kai tsaye
Getty Images

Watford za ta kara sayo 'yan kwallo

Hertfordshire Mercury ta ce kocin Watford, Marco Silva ya nuna bukatar a kara sayo 'yan wasa a kungiyar kafin a fara wasannin bana.

Coutinho zai maye gurbin Neymar

Jaridar Mundo Deportivo

Mundo Deportivo ta wallafa cewar dan wasan Liverpool Philippe Coutinho shi ne zai maye gurbin Neymar a Camp Nou idan ya koma PSG, kuma Barcelona na duba yadda za ta sayo Ousmane Dembele da kuma Kylian Mbappe.

Kai tsaye
Getty Images

Mcllroy ya sallami mai masa hidima

Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ce Rory Mcllroy ya sallami tsohon mai masa hidima a filin kwallon golf J.P. Fitzgerald, wanda suka yi aiki tare har ya ci manyan kofi hudu da kai wa kololuwar wasan golf a duniya a shekara tara da suka yi tare.

Kai tsaye
Getty Images

Ko Ross Barkley zai koma Tottenham?

Ross Barkley
AFP

Dole dan wasan tsakiyar Everton, Ross Barkley, ya rage kudin albashin da yake nema domin ya koma Tottenham, wadda ba ta da niyyar biyan albashin fan 120,000 a ko wane mako da ya yi watsi da shi a Everton, in ji jaridar Daily Mirrow.

Wasu rahotanni sun ce Everton na son ci gaba da rike dan kwallon duk da cewa wata 12 ne kawai ya rage a kwantiraginsa.

Ronaldo ya gurfana a gaban kuliya kan haraji

Da farko mun kawo muku rahota kan cewa Cristiano Ronaldo zai gurfana a gaban kotun kan zargin kaucewa biyan haraji.

A yanzu dai dan wasan na Real Madrid ya isa kotun.

Masu shigara da kara dai na zargin Ronaldo, wanda shi ne mai rike kanbun gwarzon dan kwallon duniya, da kin biyan harajin da ya kai dala miliyan 17.

Cristiano Ronaldo
Getty Images

Sai dai kuma dan kwallon ya yi watsi da wannan zargi.

Idan dai har aka samu dan wasan dan asalin kasar Portugal da laifi kan abin da ake tuhumarsa da shi to zai iya fuskantar zaman gidan kaso.

Ronaldo, mai shekara 32, shi ne na baya-bayan nan a jerin 'yan wasan da hukumomi a Spaniya ke tuhuma kan batun haraji.

Real Madrid za ta yi wasa shida a Agusta

Da zarar Real Madrid ta kammala wasannin atisayen tunkarar kakar bana da take yi a Amurka, za ta mayar da hankali wajen lashe kofi biyu da suke gabanta a Agusta.

Real za ta buga wasan sada zumunta da fitattun 'yan wasan da suke buga gasar Amurka a ranar Alhamis 3 ga watan Agusta, kuma shi ne na karshe da za ta yi sannan ta koma Spaniya.

Daga nan ne Real Madrid za ta kara da Manchester United a UEFA Super Cup a Macedonia a ranar Talata 8 ga watan Agusta.

Real Madrid
Getty Images

Kwanaki biyar tsakani Madrid za ta ziyarci Barcelona a wasan farko a gasar Spanish Super Cup, wanda ake karawa tsakanin Zakaran La Liga, Real da na Copa del Rey, Barca.

Barcelona za ta halarci Santiago Bernabeu a gumurzu na biyu a ranar 16 ga watan Agusta a gasar ta Spanish Super Cup.

Daga nan Real za ta fafata a wasan farko a gasar La Liga a ranar 20 ga watan Agusta da Deportivo La Coruna, sannan ta buga karawar mako na biyu a gida da Valencia a ranar 27 ga watan.

Barcelona 'za ta nemi Ozil'

Mesut Ozil
Getty Images

Barcelona za ta taya dan wasan Arsenal Mesut Ozil kan fan miliyan £53, idan suka kasa sayen dan kwallon Liverpool Philippe Coutinho, a cewar jaridar Don Balon, kamar yadda Express ta rawaito.

Kawo yanzu dai Ozil ko Arsenal ba su ce komai ba game da rahotannin.

Enyimba ta hada maki uku a kan Pillars

Kungiyar Enyimba ta ci Kano Pillars daya mai ban haushi a gasar Firimiyar Nigeria wasan mako na 32 da suka kara a yammacin Lahadi.

Enyimba ta ci kwallon ta hannun Mfon Udoh a bugun fenariti saura minti 19 a tashi daga fafatawar.

Ga sauran sakamakon wasannin mako na 32 da aka yi:

 • Katsina Utd 2-2 ABS FC
 • Remo Stars 0-1 MFM
 • Plateau Utd 2-0 3SC
 • Gombe Utd 0-0 Lobi
 • Abia Warriors 0-0 FCIU
 • Nasarawa Utd 1-0 Tornadoes
 • El-Kanemi 1-0 Akwa Utd
 • Wikki 2-1 Sunshine Stars
Enyimba da Kano Pillars
Other

Man United na daf da sayen Nemanja Matic

Manchester United ta kusa daukar dan kwallon tawagar Serbia mai wasan tsakiya, Nemanja Matic daga Chelsea mai rike da kofin Premier.

Matic mai shekara 28, shi ne dan kwallo na uku da zai koma United a bana, bayan da ta sayi mai tsaron baya Victor Lindelof daga Benfica da mai cin kwallo Romelu Lukaku daga Everton.

'Yan wasan da kocin United, Jose Mourinho ke bukata sune mai raba kwallo tun daga tsakiyar fili da gwanin taka-leda daga gefen fili.

Rahotanni na cewa United za ta sayi Matic daga Chelsea kan kudin da zai kai fan miliyan 50, kuma wannan ne karo na biyu da Mourinho ke daukar dan wasan.

Matic da Mourinho
Getty Images
Mourinho ya taba sayen Matic kan fan miliyan 21 daga Benfica a Janairun 2014 zuwa Chelsea.

Ronaldo zai gurfana a gaban kuliya kan haraji

Cristiano Ronaldo
AFP

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo zai bayyana a gaban kuliya nan gaba a birnin Madrid domin ya bayar da bahasi kan tuhumar sa da ake yi da zamba cikin aminci wajen biyan haraji.

Masu shigara da kara dai na zargin Ronaldo, wanda shi ne mai rike kanbun gwarzon dan kwallon duniya, da kin biyan harajin da ya kai dala miliyan 17.

Sai dai kuma dan kwallon ya yi watsi da wannan zargi.

Idan dai har aka samu dan wasan dan asalin kasar Portugal da laifi kan abin da ake tuhumarsa da shi to zai iya fuskantar zaman gidan kaso.

Ronaldo, mai shekara 32, shi ne na baya-bayan nan a jerin 'yan wasan da hukumomi a Spaniya ke tuhuma kan batun haraji.

Barkanmu da Hantsi

Jama'a barkanmu da sake saduwa da ku a yau Litinin, inda kamar kullum muke kawo muku irin wainar da ake tonawa a fagen wasanni, musamman a fannin hada-hadar 'yan kwallon Turai.