Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Neymar na son ya koma PSG tare da Coutinho
  2. Sanchez zai fara atisaye a ranar Talata
  3. Labaran da jaridun Turai suka wallafa kan tamaula
  4. Mcllroy ya raba gari da mai yi masa hidima

Rahoto kai-tsaye

time_stated_uk

'Alex Sandro ba zai bar Juventus ba'

Daily Star cewa ta yi kocin Juventus Massimiliano Allegri ya shaidawa Chelsea cewar ba zai sayar mata da Alex Sandro ba.

Kai tsaye
Getty Images

Inter za ta yi zawarcin Sadio Mane

Daily Express ta wallafa cewar Inter Milan ta Italiya na son taya dan kwallon Liverpool, Sadio Mane mai shekara 25, wanda za ta taya kan fam miliyan 35.

Kai tsaye
BBC

Diego Costa na neman kungiya

Dan wasan Chelsea, Diego Costa ba zai yi atisaye da 'yan kwallon Chelsea ba domin tunkakar kakar da za a fara, bayan da yake ta neman klub din da zai koma da taka-leda in ji Marca.

Kai tsaye
PA

'Bolt zai zama abin koyi ga matasa'

Usain Bolt zai dace da aikin koci idan ya yi ritaya, in ji mai horar da tawagar Jamaica Glen Mills.

Bolt zakaran gasar Olympic wanda ya ci lambar zinare takwas, zai yi ritaya bayan gasar tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya da za a yi a Landan a watannan.

Mills ya ce Bolt zai zama abin koyi ga matasa a fagen wasa.

Kai tsaye
Reuters

'Klopp ba zai sayi dan wasa mai buga tsakiya ba'

Jaridar Independent ta ce tsohon dan kwallon Liverpool, Jamie Carragher ya ce Jurgen Klopp ba zai sake sayen dan wasa mai buga tsakiya ba a bana, duk da kin sayar masa da Naby Keita da RB Leipzig ta yi.

Kai tsaye
Getty Images

Coutinho zai ci gaba da zama a Liverpool

Kai tsaye
Talksport

Karen Bardsley ba za ta buga wa Ingila wasa ba

Mai tsaron ragar tawagar kwallon kafar mata ta Ingila, Karen Bardsley ba za ta karasa wasannin cin kofin nahiyar Turai ba, sakamakon raunin da ta yi.

Bardsley ta yi rauni ne a karawar da Ingila ta ci Faransa a wasan daf da na kusa da na karshe, kuma Siobhan Chamberlain ce ta canje ta a fafatawar.

Ingila za ta buga wasan daf da karshe da Netherlands a ranar Alhamis, tuni tsohuwar mai tsaron ragar Ingila, Rachel Brown-Finnis ta ce tana sa ran Chamberlain za ta taka rawar gani.

Kai tsaye
Getty Images

Paris za ta karbi gasar Olympic ta 2024

Mahukuntan birnin Los Angeles din Amurka, sun sanar da cewar an ba su izinin karbar bakuncin wasan Olympic na shekarar 2028.

Hakan kuma na nufin birnin Faris din Faransa ne zai fara karbar fafatawar da za a yi a 2024 kenan.

Kai tsaye
Getty Images

Autan Mai Turare a wakar da ya yi wa Horo

Sharapova ta doke Brady

Maria Sharapova ta doke Jennifer Brady da ci 6-1 4-6 da 6-0 a gasar Stanford West Classic, bayan jinya da ta yi.

Sharapova wadda ta dawo atisaye a cikin watan Afirilu, an hana ta wasa wata 15 sakamakon samunta da laifin shan abubuwa masu kara kuzari da aka yi.

Kai tsaye
Reuters

An ci tarar Nathan Redmond

An ci tarar dan kwallon Southampton, Nathan Redmond fan 1,000, bayan da aka sameshi da laifin gudun wuce sa a a cikin motarsa ta Range Rover wadda ta take fan 80,000 in ji Daily Mail.

Kai tsaye
Getty Images

Fernando zai koma Galatasaray

Dan wasan tawagar Brazil, Fernando na daf da komawa Galatasaray daga Manchester City.

Dan kwallon mai shekara 30 ya koma taka-leda a City daga Poto kan fam miliyan 12 a shekarar 2014.

Fernando ya buga wa City wasa 101, ciki har da 27 da ya murza-leda a kakar da ta kare, bai kuma halarci wasannin atisayen da kungiyar ta yi a Amurka a Yuli ba.

Kai tsaye
Getty Images

Takaitattun Labaran Wasanni

Jesus Navas ya koma Sevilla

Dan wasan tawagar kwallon kafar Spaniya, Jesus Navas ya sake koma Sevilla daga Manchester City, kan yarjejeniyar shekara hudu.

Kai tsaye
Getty Images

Jagaba wajen cin kwallo a gasar Firimiyar Nigeria

Bayan da aka buga mako na 32

Kai tsaye
LMCNPFL

Ter Stegen da Gomes sun koma atisaye

'Yan wasan Barcelona Ter Stegen da kuma Andre Gomes sun koma atisaye a kungiyar bayan da aka duba lafiyarsu.

📸  Ter Stegen and André Gomes have passed their medicals and returned to training ⚽️🏋️ 🔴🔵 #ForçaBarça
📸  Ter Stegen and André Gomes have passed their medicals and returned to training ⚽️🏋️ 🔴🔵 #ForçaBarça
📸  Ter Stegen and André Gomes have passed their medicals and returned to training ⚽️🏋️ 🔴🔵 #ForçaBarça
📸  Ter Stegen and André Gomes have passed their medicals and returned to training ⚽️🏋️ 🔴🔵 #ForçaBarça

📸 Ter Stegen and André Gomes have passed their medicals and returned to training ⚽️🏋️ 🔴🔵 #ForçaBarça

Yawan wasa kwallo bai shiga raga ba

Gasar Premier Nigeria bayan mako na 32

Kai tsaye
LMCNPFL

Fiorentina za ta dauki Emre Mor

Fiorentina za ta taya dan kwallon Borussia Dortmund, Emre Mor kan Yuro miliyan 10 in ji jaridar La Nazione, sai dai kuma Dortmund za ta bukaci kudin da aka taya dan kwallon.

Kai tsaye
Getty Images

An ci kwallo 626 a gasar Firimiyar Nigeria

Bayan da aka kammala wasannin mako na 32 a gasar Firimiyar Nigeria, a karshen mako an ci kwallo 626 a wasa 318 da aka fafata.

Kuma kwallo 482 kungiyoyin da suka buga wasa a gida suka ci, yayin da zura 144 a waje.

Plateau United ce ta daya a kan teburi da maki 58, sai Mountain Of Fire ta biyu da maki 55, Akwa tana ta uku da maki 51.

Kai tsaye
Getty Images

Monaco za ta maye gurbin Mbappe

Rahotanni na cewa Monaco na shirin maye gurbin Kylian Mbappe da dan kwallon Ajax Kasper Dolberg.

Real Madrid ce ke son daukar Mbappe dan wasan tawagar Faransa.

Kai tsaye
Getty Images

Ko Liverpool za ta kasa Arsenal kan Lemar?

Liverpool na sha'awar sayan dan wasan tsakiyar Monaco Thomas Lemar wanda Arsenal ma take hako, in ji jaridar Le10Sport.

A baya dai Arsenal ce ake ganin za ta sayi dan kwallon mai shekara 21.

Thomas Lemar
Getty Images

Sancho ka iya barin Man City

Dan wasan Manchester City kuma daya daga cikin tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 17, Jadon Sancho ka iya barin kungiyar domin bai halarci atisaye ba a lokuta da dama, in ji jaridar Telegraph.

Red Bull Leipzig da Borussia Dortmund na Jamus na daga cikin masu neman dan kwallon.

Jadon Sancho
Getty Images

Van Dijk zai gana da kocin Southampton

Virgil van Dijk
Getty Images

Mai tsaron bayan Southampton, Virgil van Dijk, mai shekara 26, ya shirya domin tattaunawa da sabon kociya Mauricio Pellegrino a wannan makon a lokacin da Liverpool ta shirya domin kafa tarihi na sayan dan wasan kan kudi mafi tsada, in ji jaridar Echo.

Sanches ka iya 'maye gurbin Coutinho' a Liverpool

Kociyan Liverpool Jurgen Klopp zai iya taya dan wasan Bayern Munich din nan mai shekara 19 Renato Sanches idan har Philippe Coutinho, mai shekara 25, ya koma Barcelona, in ji Daily Mirrow.

Renato Sanches
Getty Images

Alex Sandro ba na sayarwa ba ne - Allegri

Kociyan Juventus, Massimiliano Allegri ya shaida wa Chelsea cewa kungiyarsa ba za ta sayar da dan wasan baya na gefen hagu, Alex Sandro, mai shekara 26, ba.

Jaridar Sport Mediaset ce ta rawaityo kocin ya bayyana hakan.

Kawo yanzu Chelsea ba ta ce komai ba gama da rahotannin.

Alex Sandro
Getty Images

Costa ba zai halarci atisayen Chelsea ba

Dan wasan gaban Chelsea, Diego Costa, mai shekara 28, ba zai halarci atisayen da kulob din zai yi ba ranar Talata yayin da yake neman inda zai koma, in ji jaridar Marca.

Ana hasashen dan kwallon zai koma kungiyarsa ta da, wato Atletico Madrid.

Diego Costa
Diego Costa Twitter
Diego Costa ya wallafa hotonsa yana shakatawa a wani wuri da ba a bayyana ba

Neymar na son ya koma PSG tare da Coutinho

Rahotanni daga Faransa na cewa dan wasan Barcelona Neymar na saon komawa Paris Saint-Germain tare da takwaransa na Brazil Philippe Coutinho na Liverpool.

Duk 'yan wasan biyu na daga cikin wadanda aka fi yin ce-ce-ku-ce akan yiwuwar sauya sheka daga kungiyoyinsu.

Sai dai duka Barcelona da Liverpool sun bayyana cewa 'yan wasan ba na siyarwa ba ne.

Neymar da Coutinho
Getty Images

Man United ta kammala sayen Matic

Manchester United ta kammala daukar Nemanja Matic daga Chelsea kan kudi fan miliyan 40 kan yarjejeniyar shekara uku.

Matic mai shekara 28, shi ne na uku da United ta dauka a bana, bayan mai tsaron baya Victor Lindelof daga Benfica kan fam miliyan 31 da mai cin kwallo Romelu Lukaku kan fam miliyan 75 daga Everton.

Mourinho ya taba sayen Matic kan fan miliyan 21 daga Benfica a Janairun 2014 zuwa Chelsea.

Manchester United za ta buga Uefa Super Cup a karawar da za ta yi da Real Madrid a ranar 8 ga watan Agusta.

Nemanja Matic
AFP

Barkanmu da Hantsi

Jama'a barkanmu da sake saduwa da ku a yau Litinin, inda kamar kullum muke kawo muku irin wainar da ake tonawa a fagen wasanni, musamman a fannin hada-hadar 'yan kwallon Turai.