Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Liverpool ta ki sallama Countinho ga Barca
  2. AC Milan na son sayen Ibrahimovic
  3. Liverpool na neman 'sabon Ronaldo'
  4. Mourinho na neman karin dan wasa
  5. Ranar Juma'a za a fara gasar Premier
  6. Yaya Everton take ciki?

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

Sai mako mai zuwa

Abun da ya samu kenan a labaran wasanni kai tsaye na wannan makon. Sai kuma mako mai zuwa in mai duka ya kaimu.

Crystal Palace ta dau aron dan wasan Man Utd

Crystal Palace ta dauki aron mai tsaro bayan Manchester United Timothy Fosu-Mensah na tsawon kaka daya.

Da wasan da ya koma United a lokacin yana dan shekara 16 ya rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya a Old Trafford a watan Oktoba wadda za ta kai shekarar 2020.

Timothy
Getty Images

Arsenal na shirin tinkarar Leicester City

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta dukufa tana shirin tinkarar Leicester City a wasan farko na gasar Firimiyar kakar 2017-2018 da za su fafata ranar Juma'a.

Wani hoton da ta wallafa a shafinta na Twitter ya nuna 'yan wasa Arsenal biyu suna atisaye.

Sakon dai yana dauke da alamar karfin guiwa.

View more on twitter

Najeriya ta yi sama a teburin FIFA

Hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta fitar da sabon jerin sunayen kasashen da suke gwanayen kwallon kafa a duniya inda Najeriya ta haura daga mataki na 37 da take a da zuwa na 38.

A cikin jerin kasashen Brazil ta koma kasa ta daya da ta fi iya taka leda a duniya yayin da Jamus ta koma ta biyu, ita kuma Ajantina ta koma ta uku.

A Afirka kuma Masar ce ta daya yayin da Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo ta zo ta biyu, ita kuma Senegal ta zo ta uku.

Kazalika Tunisiya ta zo ta hudu, Kamaru ta zo ta biyar , Najeriya kuma ta zo ta shida a nahiyar Afirka.

Super Eagles
Getty Images

Marseille ta dauki Amavi

Marseille ta dauki dan wasan Aston Villa Jordan Amavi a matsayin aro na tsawon shekara daya.

Suna kuma da damar sayen dan kwallon mai shekara 23 din-din-din.

Amavi ya koma Villa ne daga Nice shekara biyu da ta wuce kan fan miliyan 13.

Tsohon dan wasan baya na Manchester United da Juventus Patrice Evra, mai shekara 36, shi ne ke buga wa Marseille lamba uku, inda Amavi ke buga tasa ledar.

Dortmund ta yi watsi da bukatar Barca kan Dembele

Borussia Dortmund ta yi watsi da bukatar Barcelona ta sayen dan wasan kungiyar mai shekara 20 Ousmane Dembele.

"Borussia Dortmund ta tattauna da FC Barcelona kan yunkurin sayen Ousmane Dembele," a cewar sanarwar da kulob din ya fitar.

Ta kara da cewa tayin da Barcelona ta yi bai dace da daraja da kwarewar dan kwallon ba.

Ousmane Dembele
Getty Images

Cike gurbin Lukaku zai yi wuya - Koeman

Kociyan Everton, Ronald Koeman, ya ce abu ne mai wuya kulob dinsa ya iya cika gurbin da Romelu Lukaku ya bari.

Lukaku dai ya koma Manchester United daga Everton.

Koeman ya ce: "A bu ne mai wuya maye gurbin Romelu Lukaku, ban ce ba zai yiwu ba, amman kwallo 25 na da yawa, kuma dole ne mu nemi wasu hanyoyi da kuma himmar aiki daga sauran 'yan wasan kuma muna son mu shigo da wasu 'yan wasan."

Romelu Lukaku
Getty Images
Lukaku ne dan wasan da yafi cin kwallo cikin 'yan Everton a kakar bara

Watford na shirin fafatawa da Liverpool

Watford
Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Watford na shirin fafatawa da Liverpool a wasansu na farko a gasar Firimiya ta bana.

A bayanin da ya yi wa manema labarai ranar Alhamis, kociyan Watford, Marco Silva ya ce: "Muna aiki tukuru a shirye-shiryenmu kuma ina ganin mun shirya.

Za mu fara da karawa da wata kungiyar da ta iya taka-leda, kuma haka ne yafi kyau mu fara. Gwaji na farko ne kawai, muna bukatar karawa da kowa.

Da yake magana akan Andre Gray, dan wasan gaban Burnley da ya saya akan kudi fam miliyan 18.5, Silva ya ce:

"Dan wasa mai kyau ne, na san wani dan wasa ne da ya so ya zo Watford, yana son ya ci gaba ya kuma yi fafatukar samun wuri a kungiyar. Mun yi nazari kan wuraren da muke bukatar sabbin 'yan wasa, daban yake da sauran 'yan wasan gabanmu. Kasuwar tana da wuyar sha'ani a wannan kakar."

Marco Silva

Muna dab da sayen Sigurdsson - Everton

Bayan kociyan Swansea, Paul Clement ya ce yana tsammanin Gylfi Sigurdsson ya koma Everton, kociyan Toffees (Everton), Ronald Koeman ya ce an kusa cimma yarjejeniya kan dan wasan.

Koeman ya ce: "Har yanzu yarjejeniyar ta yi kusa, wannan bai sauya ba, Na ji rade-radin cewar tattaunawar ta tsaya, amman har yanzu muna tattaunawa da Swansea."

Sigurdsson
Getty Images

Cooper ya tsawaita zamansa a Leeds

Dan wasan baya na Leeds United Liam Cooper ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar shekara hudu tare da kungiyar.

Dan kwallon mai shekara 25 ya buga wasa 80 tun lokacin da ya koma kulob din daga Chesterfield a watan Agustan 2014.

Liam Cooper
Rex Features

Babu Sigurdsson a jerin 'yan wasan Swansea

Kocin Swansea City Paul Clement ya ce dan wasan tsakiya Gylfi Sigurdsson ba zai kasance a cikin jerin 'yan wasan da za su buga masa wasa a karawar da za su yi da Southampton ranar Asabar ba.

An rawaito cewa Sigurdsson na son komwa Everton, sai dai har yanzu ba su amince su biya fan miliyan 50 da aka sanya wa dan kwallon ba.

Gylfi Sigurdsson
Getty Images

Brighton za ta sayi Jose Izquierdo

Brighton ta shirya domin sayan dan wasa mafi tsada a tarihinta a karo na uku a wannan lokacin bazarar bayan ta cimma yarjejeniyar sayan dan wasan Colombia, Jose Izquierdo, daga kungiyar kwallon kafa ta Club Brugge.

Dan wasan gefen mai shekara 25 wanda zai koma kungiyar ta Firimiya a kan yarjejeniyar da aka ce ta kai kudi fam miliyan 13.5 zai kammala komawarsa bayan an gama msihi gwaje-gwaje..

Izquierdo ya ci kwallo 15 na gasar kwararru ta kasar Belgium a kakar bara.

Jose Izquierdo
Getty Images

AC Milan na neman Ibrahimovic

AC Milan na sa ran ci gaba da sayan 'yan wasan da suka yi ta yi a lokacinh bazara ta hanyar neman dan wasan gaban Manchester United, Zlatan Ibrahimovic, mai shekara 35, in jiCorriere dello Sport.

Ibrahimovic
Getty Images

Liverpool na son sayan 'sabon Ronaldo'

Liverpool tana kara matsa kaimi wajen sayan dan wasan Brazil, Luan, wanda aka yi wa lakabi da 'sabon Ronaldo' ta hanyar tura wakilanta su kalli dan shekara 24 din, in ji Daily Mirror

Reds ba ta dauki fiye da minti 35 ba kafin ta yi watsi da tayin fam miliyan 90 da Barcelona ta sake yi kan Phillipe Countinho mai shekara 25 ba, in ji jaridar Daily Express.

Liverpool
Getty Images

'Tottenham za ta kara 'yan wasa'

Yayin da Kyle Walker ya riga ya bar Tottenham zuwa Man City kuma ake maganar cewar Danny Rose yake cewar yana son kulob din ya kashe kudi, kociyan Totteham Mauricio Pochettino ya ce Tottenham za ta kara 'yan wasa cikin 'yan makonnin nan.

Pochettino ya tabbatar wa BBC cewar shi yana da yakinin cewar kungiyarsa za ta kara 'yan wasa cikin makonnin nan.

A wata hirarsa da jaridar Sun ranar Alhamis, Rose, wanda ya koma Spurs daga Leeds a shekarar 2007, ya ce zai so ya ga kulob din ya kara sanannun 'yan wasa biyu ko uku.

Pochettino
Getty Images

Mersaille ta kasa sayan Giroud

Arsenal za ta fara gasar Firimiya gobe da wasan gida da zakarun kakar 2015-16, Leicester City.

A da an alakanta dan wasan gaba na Gunners, Olivier Giroud, da komawa Marseille, amman da alama cewa kungiyar kwallon kafar ta Farasa ta hakura da sayan dan kwallon.

"Ba na tunanin yana son ya zo ," in ji kociyan kulob din Rudi Garcia a hrirarsa da L'Equipe.

Giroud
Getty Images

Amavi da Bacuna na dab da barin Aston Vila

Jordan Amavi da Leandro Bacuna na dab da barin Aston Villa, kamar yadda kociya Steve Bruce ya tabbatar.

Amavi, mai shekara 23, na dab da komawa Marseille yayin da daya daga cikin abokan gogayyar Villa ke sha'awar Bacuna, mai shekara 25.

Amavi
Getty Images

Arsenal na tsoron tafiyar Sanchez

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal na tsoron cewar dan wasan gaban Chile Alexis Sanchez, mai shekara 28, zai iya sabunta yunkurinsa na ficewa daga Emirates, in ji jaridar Daily Mirror

Sanchez
Getty Images

'Chelsea ta taya Chamberlain'

Chelsea ta taya dan wasan Arsenal Alex Oxlade-Chamberlain, mai shekara 23, kan kudi fam miliyan 35 duk da cewar kwantiragin dan wasan da Gunners saura shekara daya ta kare, in ji jaridar Daily Star.

Arsenal Alex Oxlade-Chamberlain
Getty Images

'PSG na dab da sayan Kylian Mbappe'

Paris St-Germain na dab da sayan dan wasan gaban Faransa da Monaco, Kylian Mabppe, mai shekara 18, kan kudi Fam miliyan 163, kuma ta riga ta cimma yarjejeniya da takwaransa, Fabinho, mai shekara 23, wanda zai iya buga baya da tsakiya, in ji Daily Record

Mbappe
Getty Images

Liverpool ta ki sayar wa Barca Coutinho

Liverpool ta yi watsi da tayin Fam miliyan 90 da Barcelona ta yi wa madugun 'yan wasan kwallon kafa na Brazil, Philippe Countinho.

Tayi na biyun da Barca ta yi wa dan wasan mai shekara 25, wanda aka ki amincewa da shi nan take na kunshe da biyan Fam miliyan 76.8 da farko sannan a kara Fam miliyan 13.5 daga baya.

Liverpool ta nanata cewar Coutinho - wanda ya koma wurinta daga Inter Milan kan kudi Fam miliyan 8.5 a shekarar 2013- ba na sayar wa ba ne.

Barcelona ta sayar da dan wasan gaba na Brazil, Neymar ga Paris St-Germain kan kudi Fam miliyan 200 mai cike da tarihi a makon jiya.

Coutinho, wanda ya ci kwallo 14 a kakar da ta wuce kuma ya yi jinyan wuyar kafa na mako shida ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekara biyar a watan Janairu. Kuma ita yarjejeniyar ba ta ba da zabin tafiya ba.

Coutinho
Getty Images

Rose na son Tottenham ta kara 'yan wasa

Danny Rose ya nemi Tottenham ta kara kashe kudi a kasuwar musayar 'yan wasa kan sanannun 'yan wasa, in ji Sun.

Tottenham
Getty Images

'Sai dai kuma Rose ba ya son barin Spurs'

Danny Rose ya ce ba shi da niyyar barin Spurs, amman shi zai yi tunanin akan ko wane tayi kai tsaye da wata kungiya ta yi masa, kuma ya i imanin cewar ya kamata a biya shi fiye da yadda ake biyanshi yanzu, in ji jaridar Sun.

Danny Rose
Getty Images

Wa Mourinho ke son saya?

Mourinho
Getty Images

Kociyan Manchester United, JoseMourinho yana son ya kara akalla dan wasa daya kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa, kuma dan wasan baya na gefen hagun Tottenham, Danny Rose, mai shekara 27, da kuma dan wasan gefen Inter Milan Ivan Perisic mai shekara 28 na cikin wadanda yake nema, in ji Manchester Evening News.

Barka da hantsi

Jama'a, barkanku da shigowa shafinmu da ke kawo muku irin wainar da ake toyawa a fagen wasan kwallon kafa a nahiyar a Turai a yau, ranar jajibirin soma gasar Firimiya.