Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Man City za ta so ta sa Arsenal ta sayar da Sanchez
  2. Chelsea ma na son jan Chamberlain
  3. Barcelona ta cimma matsaya kan Dembele
  4. Tottenham da Chelsea na neman dan wasan baya na Ajax Amsterdam

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

Sai gobe

Jama'a, abin da ya samu kenan a shafinmu na labaran wasanni kai tsaye. Sai kuma gobe in mai duka ya kai mu. A kasance da shafinmu na labaran wasanni kai tsaye daga karfe 10.30 agogon Najeriya da Nijar.

Crystal palace na son sayan dan mai tsaron gidan Roma

Crystal Palace tana son sayan mai tsaron gidan Roma, Lukasz Skorupski, mai shekara 26,

in ji jaridar Daily Mail.

Lukasz Skorupski
Getty Images

Matic ya ce zai dade a Man Utd

Dan wasan tsakiyar Manchester United, Namanja Matic, ya ce zai dade a kungiyra kwallon kafan da ke saman teburin gasar Firimiya.

Dan wasan da ya ci kyautar gwarzon dan wasa bayan United ta yi gagarumar nasara a wasanta na farko a gasar Firimiya, ya ce ya ji dadin yadda takwarorinsa na United suka karbe shi hannu bibbiyu.

Namanja Matic
Getty Images

Buffon da Messi da Ronaldo ka iya cin kyutar Uefa

An fitar da sunayen Gianluigi Buffon da Lionel Messi da kuma Cristiano Ronaldo a matsayin wadanda za su iya cin kyutar gwarzon dan wasan ta hukumar kwallon kafa ta Turai, Uefa.

Kociyoyi 80 da 'yan jarida 55 suka zabi 'yan wasan.

Messi da Ronaldo sun ci kyautar sau biyu -inda Ronaldo ya ci a kakar bara.

Za a mika kyautar ce a ranar 24 ga watan Agusta lokacin da da za a fitar da jadawalin gasar zakarun Turai.

Uefa
Getty Images

Newcastle za ta dakuki aron dan wasan Chelsea

Ana tsammanin Newcastle United, da aka sani da Magpies, za ta dauki aron dan wasan gefen Chelsea mai shekara 21 Kenedy ,amman kociyan Blues, Conte ya jinkirta yarjejeniyar saboda tsoron raguwar 'yan wasansa, in ji. Goal.

Kenedy
Getty Images

Rafael Benitez na ya kara 'yan wasa

Kociyan Newcastle United, Rafael Benitez, yana hakon karin 'yan wasa biyar kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa nan da mako biyu, in ji jaridar Telegraph.

Rafael Benitez
Getty Images

Stoke City na gab da shelar sayan Jese Rodriguez

Kungiyar kwallon kafa ta Stoke City na gab da shelar sayan dan wasan gaba na PSG mai shekara 24 Jese Rodriguez, in ji jaridar Telegraph.

Jesse Rodriguez
Getty Images

Dan wasan Leicester na dab da komawa Derby County

Dan wasan gefen Leicester City, Tom Lawrence, mai shekara 23, yana dab da komawa Derby County a wata yarjejeniyar da ta kai fam miliyan 7, in ji jaridar Daily Mail.

Tom
Getty Images

Carlos Tevez ya yi alkawarin komawa Shangai Shenhua

An bai wa Carlos Tevez izinin zuwa Argentina, amman sai da ya rattaba hannu kan wata takarda cewar shi zai koma kungiyar kwallon kafa ta Shangai Shenhua zuwa ranar 30 ga watan Agusta.

Akwai rahotannin da ke cewa, Tevez mai shekara 33, wanda ya koma Shanghai daga Boca Juniors a watan Disamba, yana son barin kulob din.

Tsohon dan wasan gaba na Manchester City din ya nemi Shanghai ta kyale shi ya koma gida jinyan ciwon da ya ji a kafa.

Tevez, wanda ya rattaba hannu akan yarjejeniyar shekara biyu, ya sha kwallaye biyu a wasanni 11.

Tevez
Getty Images

Chelsea na son dan wasan Ajax

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tana sha'awar dan wasan baya Davinson Scanhez, amman Ajax ta hakikance cewar Sanchez ba na sayarwa ba ne, in ji jaridar Daily Star.

Davinson Sanchez
Getty Images

'Ina son in koma Tottenham'

Dan wasan bayan Colombia, Davinson Sanchez, mai shekara 21, ya shaida wa kungiyar kwallon kafarsa ta Ajax cewar shi yana son komawa Tottenham kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa, in ji jaridar Independent.

Davinson Sanchez
Getty Images

Diego Costa ya yi 'abin kunya'

Rashin komawar dan wasan gaban Chelsea, Diego Costa, atisaye 'abin kunya ne', in ji tsohon dan wasan gaban Arsenal, Ian Wright.

Dan wasan mai shekara 28, wanda a yanzu haka yana kasarsa Brazil, ya ce an yi masa kamar shi babban mai laifi ne a Chelsea kuma yana son ya koma tsohuwar kulob dinsa, Atletico Madrid.

Diego Costa
Getty Images

Ajen din Mahrez na son Roma ta kara mar kudi

Ajen din wasan gefe na Leicester City, Riyad Mahrez, yana kokarin shawo kan kungiyar kwallon kafa ta Roma domin ta kara kudin da ta taya dan wasan mai shekara 26 zuwa fam miliyan 40 ciki har da kudaden da za a kara, in ji Sky Sports.

Mahrez
Getty Images

Komawar Ross Barkley Chelsea na cike da shakku

Komawar dan wasan tsakiyar Everton Ross Barkley zuwa Chelsea ko Tottenham ya kasance cike da shakku bayan dan shekara 23 din ya ji ciwo a lokacin ataisaye, in ji jaridar Sun.

Ross Barkley
Getty Images

Marco Asensio na son tattaunanwa kan Arsenal

Dan wasan tsakiya Marco Asensio, mai shekara 21, ya nemi a gudanar da tattaunawar gaggawa da Real Madrid bayan Arsenal ta nuna sha'awar son sayansa,in ji jaridar Sun.

Marco Asensio
Getty Images

Chelsea ta gindaya wa Diego Costa sharruda

Chelsea ta gindaya wa dan wasan gaba Diego Costa wasu sharruda da dole sai ya cika kafin ta yi tunanin sayar da dan wasan mai shekara 28, in ji jaridar Guardian.

Costa
Getty Images

'Zan yi kokarin shawo kan Coutinho'

Keftin din Liverpool, Jordan Henderson, ya ce shi zai yi kokarinsa wajen shawo kan takwaransa, Philippe Coutinho, ya tsaya a Anfield, yayin da dan Brazil din mai shekara 25 ke neman komawa Barcelona, in ji jaridar Daily Mirror.

Coutinho
Getty Images

An samu baraka tsakanin Conte da masu Blues

An samu rashin jituwa tsakanin kociyan Blues , Antonio Conte, da masu Stamford Bridge kan adadin yan wasan da ya kamata kungiyar ta saya yayin da kociyan dan asalin Italiya yake son sayan 'yan wasa masu kwarewa wadanda sake sayar da su ba zai yi kudi ba, in ji Times.

Conte
Getty Images

Barcelo ta cimma matsaya da Borussia Dortmund kan Ousmane Dembele

Barcelona ta cimma yarjejeniyar biyan Borussia Dortmund fam miliyan90 domin sayan dan wasan gaba mai shekara 20 Ousmane Dembele kamar yadda Daily Express ta ruwaito daga Sport.

Ousmane Dembele
Getty Images

Chelsea na samun kwarin guiwar cewar za ta sayi Chamberlain

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tana kara samun kwarin guiwar cewar za ta cimma matsaya da Arsernal domin cinikin dan wasan tsakiya Alex Oxlade-Chamberlain, mai shekara 23, kan kudi fam miliyan 35, in ji jaridar Evening Standard.

Chamberlain
Getty Images

Man City za ta nemi Arsenal ta sayar mata da Sanchez

Manchester City za ta yi kokarin ta sa Arsenal ta sayar mata da dan wasan gabanta Alexis Sanchez ta hanyar taya shi kan kudi fam miliyan 60 kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa, in ji jaridar Telegraph.

Sanchez
Getty Images

Barka da hantsi

Barkanku da shigowa shafin da ke kawo muku labaran wasanni kai tsaye.