Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. United ta ci wasa biyu a jere kuma kowanne 4-0
 2. Barcelona ta sake taya Coutinho karo na uku
 3. Sharhin Premier: Liverpool da Crystal Palace
 4. An fara makon farko a gasar La Liga ta 2017/18
 5. Yadda kasuwar 'yan kwallon Turai ke ci
 6. Konta ta kai wasan daf da na kusa da na karshe

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

Nan muka kawo karshen shirin da fatan za ku tara a ranar Litinin.

Damben gargajiya

Dan Sama'ila da Abba Shagon Shamsu Kanin Emi a wani dambe da suka yi a unguwar Dei-Dei da ke Abujar Nigeria.

Da farko damben ya zo da takaddama, amma da aka sake karawa sai Dan Sama'ila daga Kudu ya yi nasara a kan Abba daga Arewa.

Firimiyar Nigeria wasannin mako na 35

A ranar Lahadi za a ci gaba da gasar cin kofin Firimiyar Nigeria wasannin mako na 35.

Kai tsaye
LMC NPFL

Liverpool da Crystal Palace

'Yan wasan da za su buga karawa tsakanin Liverpool da Crystal Palace da wadan da za su yi jiran kar-ta-kwana da alkalin wasa.

Kai tsaye
BBC Sport

United ce ta daya a kan teburi

Rabon da Manchester United ta ci kwallo hudu ko fiye da haka a wasa biyu a jere a farkon bude gasar Premier tun 1907-08 shekara 110 kenan.

1907-08 - Manchester United have scored 4+ goals in their opening two league games of a season for the first time i… twitter.com/i/web/status/8…

Yadda aka murza-leda tsakanin Swansea da United

Kai tsaye
BBC Sport

Swansea 0-4 Man United

An tashi daga wasan

Pogba da Lukaku sun ci kwallo

'Yan wasan da United ta saya Paul Pogba kan kudi fam miliyan 89m a bara da Romelu Lukaku fam miliyan 75 a bana sun ci mata kwallo a karawar da ta doke Swansea 4-0

Kai tsaye
Reuters

Swansea 0-4 Man United

Anthony Martial

Kai tsaye
BBC

Swansea 0-3 Man United

Paul Pogba

United ta ci kwallo biyu a minti biyu

Kai tsaye
BBC

Swansea 0-2 Man United

Romelu Lukaku

Lukaku sai da ya kara da Swansea sau shida bai samu zura mata kwallo a raga ba sai a wannan karon.

Kai tsaye
BBC

Swansea 0-1 Man United

United ta yi canjin 'yan wasa

 • Fellaini ya canji Mata
 • Martial ya canji Rashford

Spanish La Liga makon farko

Asabar 19 ga watan Agusta

 • Celta Vigo da Real Sociedad
 • Girona da Atletico Madrid
 • Sevilla da Espanyol
Kai tsaye
Getty Images

Swansea 0-1 Man United

Wannan ne karon farko da Eric Bailly na Manchester United ya ci kwallo a gasar Lig a tarihinsa na tamaula, duk da hare-hare 67 da ya kai jumulla.

Kai tsaye
Getty Images

Wasannin damben Katsina

Wadan da za a buga a ranar Asabar 19 ga Agusta

Kwankwasiya Abuja za su karasa wasansu guda biyu tsakaninsu da jihar Ogun .

Dan Zabarma na Ogun da Bahagon Samaila na kwankwasiya Abuja sai Shagon Shagon Buhari na Ogun da Shagon Shaf Shaf na kwankwasiya

Bayan an kammala sai fara dambatawa tsakanin jihar Kano da Kebbi

Kai tsaye
BBC

Swansea 0-1 Man United

An ta fi hutun minti 15 sannan a dawo fili

Kai tsaye
Getty Images

Swansea 0-1 Man United

Erik Bailly

Kai tsaye
BBC

Gasar damben Katsina

Wadan da za su buga wa jihar Kano dambe.

Kai tsaye
BBC

Nigeria za ta karbi bakuncin Benin

A yammacin Asabar 19 ga watan Agusta tawagar Super Eagles ta Nigeria za ta buga wasa da ta Benin a karawar share fagen shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 'yan wasan da ke murza-leda a cikin nahiyar.

Za a yi wasan ne a filin Kano Pillars mai sunan Sani Abacha da ke kofar Mata a Kano, Nigeria da karfe hudu agogon Nigeria da Niger.

Kai tsaye
The NFF

Gasar damben Katsina

'Yan damben jihar Katsina

Kai tsaye
BBC

Swansea 0-0 Man United

Dan kwallon Manchester United, Marcus Rashford da mai tsaron bayan Swansea City Alfie Mawson

Kai tsaye
Getty Images

Sakamakon makon farkon La Liga

A ranar Juma'a aka yi wasa biyu

 • CD Leganes 1 : 0 Deportivo Alaves
 • Valencia C.F 1 : 0 Las Palmas

Wasa uku za a yi a ranar Asabar 19 Agusta

 • Celta de Vigo da Real Sociedad
 • Girona da Atletico de Madrid
 • Sevilla FC da RCD Espanyol
Kai tsaye
Getty Images

Damben gasar Katsina

'Yan damben Kwankwasiya Abuja

Kai tsaye
BBC

Karawar da Mourinho ya yi da Swansea

Mourinho ya jagoranci karawa da Swansea City sau bakwai, inda ya yi nasara a fafatawa biyar ya yi canjaras sau biyu. Daga cike ya doke Swansea sau uku a filin wasa na Liberty.

Kai tsaye
BBC Sport

Swansea da Manchester United

Wasan mako na biyu a gasar Premier

'Yan wasan da za su buga wa kungiyoyin biyu tamaula da wadan da za su yi jiran kar-ta-kwana da alkalin wasa a Old Trafford.

Kai tsaye
BBC Sport

Barcelona ta kara taya Coutinho

Jaridar Daily Mirror ta zayyana abubuwa da dama da ya kamata Barcelona ta cika idan har tana son daukar Philippe Coutinho daga Liverpool. Barcelona ta taya dan wasan na Brazil karo na uku fam miliyan 114 a ranar Juma'a, sai dai Liverpool ba ta sallamar ba.

Kai tsaye
Daily Mirror

Gasar damben gargajiya ta jihar Katsina

Jihar Nassarawa ta cinye Kaduna da kisa hudu da babu ko daya.

Inda Kunnari ya kashe fijo. Bahagon Audu Argungun ya kashe dogon Minista sai dogo mai Takwasara ya kashe Shagon 'Yarbalala da wasan da Jonsina ya kashe Shagon Bahagon Sarka.

Kwankwasiya abuja Takara da jihar Ogun.

Koriyo daga Ogun ya kashe Dan Ibro na Kwankwasiya da karawar da Shegun na Ogun ya kashe Dan aliyu na kwankwasiya abuja

Kai tsaye
BBC

Gasar Premier mako na biyu

Wasannin da za a yi a ranar Asabar 19 ga watan Agusta

 • Swansea City da Manchester United
 • Liverpool Crystal da Palace FC
 • Southampton FC da West Ham United
 • Leicester City da Brighton & Hove Albion
 • Burnley FC da West Bromwich Albion FC
 • Bournemouth FC da Watford
 • Stoke City FC da Arsenal FC

Liverpool da Crystal Palace

A shirinmu na sharhi da bayanai a gasar cin kofin Premier kai tsaye.

Wannan makon za mu kawo muku fafatawar daya daga wasannin mako na biyu ne tsakanin Liverpool da Crystal Palace.

Za mu fara gabatar da shirin da karfe biyu da rabi agogon Nigeria da Niger, za kuma ku iya bayar da gudun mawarku a lokacin da ake gabatar da shirin a dandalinmu na muhawara da sada zumunta na BBC Hausa Facebook.

Kai tsaye
Getty Images

Barkanmu da shiga labarain wasanni kai tsaye, inda yau za a yi wasannin mako na biyu a gasar Premier Ingila, an kuma fara La Liga a ranar Juma'a da sauran labaran wasanni da ke faruwa a sassan duniya.