Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Sanchez zai buga wasan Liverpool
  2. Chelsea ta sake taya Chamberlain
  3. Ronaldo zai iya barin Madrid

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

Sai makon gobe!

Abun da ya samu kenan. Sai mako mai zuwa.

Neymar zai maka Barca kotu

Dan wasan gaba Neymar zai maka tsohuwar kungiyarsa kotu kan kyautar fam miliyan 23.97 na cikin yarjejeniyar da ya saka wa hannu a watan Nuwamban bara da ba a biyashi ba.

Wanna na zuwa ne bayan Barca ta ce za ta kai karan sabon dan wasan PSG din kan kudi fam miliyan 7.83 da take son ya mayar.

Neymar
Getty Images

Yaushe za a buga wasannin?

Ranar wasa ta daya: 12-13 ga watan Satumba

Ranar wasa ta biyu: 26-27 ga watan Satumba

Ranar wasa ta uku: 17-18 ga watan Oktoba

Ranar wasa ta hudu: 31 ga watan Oktoba zuwa 1 ga watan Nuwamba

Ranar wasa ta biyar: 21-22 ga watan Nuwamba

Ranar wasa ta shida: 5-6 ga watan Disamba

ucl
Getty Images

Cikakaken jadawalin rukuni-rukunin!

Ga cikakaken jadawalin rukuni-rukunin da za su fafata a mataki na gaba a gasar zakarun Turai:

Rukuni na A: Benfica, Manchester United, Basel, CSKA Moscow

Rukuni na B: Bayern Munich, Paris St-Germain, Anderlecht, Celtic

Rukuni na C: Chelsea, Atletico Madrid, Roma, Qarabag

Rukuni na D: Juventus, Barcelona, Olympiakos, Sporting

Rukuni na E: Spartak Moscow, Sevilla, Liverpool, Maribor

Rukuni na F: Shakhtar Donetsk, Manchester City, Napoli, Feyenoord

Rukuni na G: Monaco, Porto, Besiktas, RB Leipzig

Rukuni na H: Real Madrid, Borussia Dortmund, Tottenham, Apoel

CL
Getty Images

Rukuni na A: Man Utd za ta koma Moscow

Rukuni na A: Benfica da Manchester United da Basel da kuma CSKA Moscow

Yadda rukuni na H yake

Rukuni na H: Real Madrid da Borussia Dortmund da Tottenham da kuma Apoel

Rukuni na D

Rukuni na D: Sporting Lisbon za ta hadu da Juve da Barca da kuma Olympiakos a rukuni na D.

Yadda rukuni na C yake

Rukuni na C: Chelsea, Atletico Madrid, Roma, Qarabag.

Yadda rukuni na G yake

Rukuni na G: Monaco, Porto, Besiktas, RB Leipzig.

Yadda jadawalin yake a yanzu

Rukuni na A: Benfica, Manchester United, Basel

Rukuni na B: Bayern Munich, Paris St-Germain, Anderlecht

Rukuni na C: Chelsea, Atletico Madrid, Roma

Rukuni na D: Juventus, Barcelona, Olympiakos

Rukuni na E: Spartak Moscow, Sevilla, Liverpool

Rukuni na F: Shakhtar Donetsk, Manchester City, Napoli

Rukuni na G: Monaco, Porto, Besiktas

Rukuni na H: Real Madrid, Borussia Dortmund, Tottenham

Liverpool!

Liverpool da Spartak da kuma Sevilla na cikin rukuni na E ne.

Klopp
Getty Images

Yadda rukunin A da na B suke a yanzu

Rukuni na A: Benfica, Man Utd, Basel

Rukuni na B: Bayern, PSG, Anderlecht

Man Utd
Getty Images

Yadda jadawalin yake a yanzu

Rukuni na A: Benfica

Rukuni na B: Rukuni na C: Chelsea

Rukuni na D: Juventus

Rukuni na E: Spartak Moscow

Rukuni na F: Shakhtar Donetsk

Rukuni naG: Monaco

Rukuni na H: Real Madrid

Monaco!

Monaco za ta fafata ne a rukuni na G a matakin rukuni-rukuni na gasar zakarun Turai.

Chelsea!

Chelsea za ta fafata ne a rukuni na C a matakin rukuni na gasar zakarun Turai.

Conte
Getty Images

Spartak Moscow

Spartak Moscow, Zakarun Rasha za su fafata ne a rukuni na E a matakin rukuni na gasar Zakarun Turai.

A karon farko cikin shekara 9...

A karon farko tun kakar 2007/2008 kulob shida daga Birtaniya za su fafata a matakin rukuni na gasar zakarun Turai.

Kungiyoyin sun hada da: Tottenham da Manchester United da Manchester City da Liverpool da Chelsea da kuma Celtic.

Man Utd
Getty Images
Lashe gasar Europa na da nashi alfanun

Dan wasan Southampton ya tsawaita kwantiraginsa

Dan wasan bayan Southampton, Maya Yoshida, ya rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar shekara uku da kulob din gasar Firimiyar din.

Dan wasan mai shekara 29 dan asalin kasar Japan ya buga wasanni 138 tunda ya koma Southampton daga VVV-Venlo a shekarar 2012

Yoshida
Getty Images

Barca na son sayan dan wasan Chelsea

Barcelona tana shirin sayan dan wasan Chelsea mai shekara 29, Willian, in ji Times.

Willian
Getty Images

Ibrahimovic ya sabunta kwantiraginsa da Man Utd

Zlatan Ibrahimovic ya sabunta kwantiraginsa a Manchester.

Dan wasan mai shekara 35 wanda ya buga wa Uinted wasa 46 tare da cin kwallaye 28 akakar bara, ya rattaba hannu ne kan yarjejeniyar shekara daya.

.
.

Swansea na dab da sayan dan wasan gaban Man City

Swansea City tana dab da sayan dan wasan gaban Manchester City, Wilfried Bony .

City ta biya Swansea kudi fam miliyan 25 wajen sayan dan wasan gaban, Ivory Coast din shekaru biyu da rabi da suka gabata.

Kawo yanzu dai kungiyoyin biyu ba su cimma kudin cinikin dan wasan ba, kuma za su iya ci gaba da tattaunawa har zuwa cikin mako mai zuwa, amman ana tsammanin Bony zai koma kudancin Wales kan kudin da ya yi kasa da rabin abun da aka abiya daga farko.

Swansea
Getty Images

Hull City za ta kammala sayan dan Arsenal

Ana tsammanin Hull City za ta kammala sayan dan wasan gaban Arsenal, Jon Toral, mai shekara 22, ranar Alhamis, kuma za ta kara wani dan wasan gaba a jerin 'yan wasanta, in ji jaridar Hull Daily Mail.

Jon Toral
Getty Images

West Ham ka iya taya dan Sunderland

West Ham za ta iya taya dan wasan tsakiya na Sunderland, Didier Ndong, mai shekara 23, bayan ta kasa cimma yarjejeniya da Sporting Lisbon kan William Carvalho, mai shekara 25, in ji London Evening Standard.

Didier Ndong
Getty Images

Aston Villa na son sayan Jack Wilshere

Kociyan Aston Villa, Steve Bruce, yana son sayan dan wasan tsakiyar Arsenal, Jack Wilshere, mai shekara 25, kuma zai iya daukan aron dan wasan gaban West Ham,Robert Snodgrass, mai shekara 29, in ji Talksport.

Jack Wilshere
Getty Images

Har yanzu Man City na son Sanchez

Har yanzu Manchester City na son sayan dan wasan gaban Arsenal, Alexis Sanchez, mai shekara 28, kafin a rufe kasuwar 'yan wasa a mako mai zuwa, in ji jaridar Daily Mail.

Sanchez
Getty Images

AC Milan na son sayan Diego Costa

AC Milan na son sayan dan wasan gaban Chelsea, Diego Costa, duk da cewar dan shekara 28 din ya hakikance cewar shi Atletico Madrid yake son komawa, kamar yadda Express ta ruwaito daga Corriere dello Sport.

Diego Costa
Getty Images

Huddersfield ta dau aron Hadergjonaj

Huddersfield Town ta dau aron dan wasan baya na Ingolstadt, Florent Hadergjonaj, na tsawon kaka

Dan wasan Switzerland din mai shekara 23 ya buga wasannin gasar Bundesliga 25 a kakar bara.

Zai iya buga wasanshi na farko a fafatawar da Huddersfield za ta yi da Southampton ranar Asabar.

Kociya David Wagner ya ce: "Abu ne muhimmi a lokacin kasuwar musayar 'yan wasannan mu samu dan wasa da zai yi gogayya da wanda ke buga mana baya ta dama, kuma Florent shi ne dan wasan da ya fi dacewa da hakan."

Huddersfield
Getty Images

Everton za ta shiga zawarcin Dennis Praet

Everton ta shirya domin gogayya da Newcastle United a kokarinta na sayan dan wasan tsakiya Dennis Praet, mai shekara 23, daga Sampdoria, in ji Times.

Dennis Praet
Getty Images

Coutinho na tunanin yin a-yita-ta-kare da Liverpool

Dan wasan Liverpool, Philippe Coutinho, mai shekara 25, yana tunanin fitar da wani sako da zai nuna rashin jin dadinshi a kulob din domin ya tilasta fitanshi, in ji Yahoo Sports.

Coutinho
Getty Images

Nan da sa'o'i shida za fitar da jadawalin gasar zakarun Turai

Nan da kimanin sa'o'i shida ne za a fitar da jadawalin wasannin zakarun Turai, wato Champions League Group Stage a Ingilishi.

CL
Getty Images

Barca na dab da sayan di Maria

Barcelona tana dab da cimma yarjejeniya da PSG ta sayan tsohon dan wasan tsakiyar Real Madrid, Angel di Maria, mai shekara 29, kamar yadda ESPN ta ruwaito daga Sport .

Angel di Maria
Getty Images

Wenger ya hakura da sayan dan Monaco

Wenger ya ce yarjejeniyar sayan dan wasan Monaco mai shekara 21, Thomas Lemar, ta "mutu".

Kociyan Arsenal din ya yi tsokaci game da Wayne Rooney, wanda ya bayyana daina taka wa Ingila leda ranar Laraba.

"Dan wasan daya ne daga cikin zakarun wannan karnin," in ji Wenger.

Thomas Lemar
Rex Features

PSG na son sayan mai tsaron gidan Napoli

Paris St-Germain na son sayan mai tsaron gidan Napoli kuma tsohon mai tsaron gida na Liverpool Pepe Reina, mai shekara 34, in ji AS.

Pepe Reina
Getty Images

Chlsea na shirin taya Drinkwater

Chelsea na shirin taya dan wasan Leicester City, Danny Drinkwater, mai shekara 27, kan kudi fam miliyan 32, in ji jaridar Sun.

Danny Drinkwater
Getty Images

Mahaifin Messi ya yi magana da Man City

Mahaifin Lionel Messi ya yi magana da Manchester City kan yiwuwar dan shekara 30 din na Barcelona ya koma filin wasan Etihad da taka leda, in ji jaridar Sun.

Messi
Getty Images

Inter Milna ta taya Mustafi na Arsenal

Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ta taya ma tsaron bayan Arsenal, Shkodran Mustafi, mai shekara 25, kan kdu fam miliyan 20, amman na aron kaka daya, in ji jaridar Mirror.

Mustafi
Getty Images

Dan wasan Benfica na dab da komawa Watford

Za a yi wa dan wasan geefen Benfica, Andre Carillo, gwaje-gwaje yau a Watford kafin su rattaba hannu kan yarjejeniyar komarwashi kulob din Firimiyar na aro.

Kociyan Watford, Marco Silva, ya yi aiki da Carillo a Sporting Lisbon, inda dan wasan ya shafe shekara biyar kafin ya koma Benfica mai hamayya a lokacin bazarar bara.

Andre Carillo
Getty Images

Chelsea ta sake taya Chamberlain

Chelsea ta sake taya dan wasan gefen Arsenal Alex Oxlade-Chamberlain, mai shekara 24, kan kudi fam miliyan 35, in ji jaridar Telegraph.

Chamberlain
Getty Images