Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. An sanya Nigeria a Rukunin D
 2. Kasashe 32 ne za su kece raini
 3. Argentina ta fada Rukunin D
 4. Wacce kasa ce ta soma daukar Kofin?
 5. Da wadanne kasashe Nigeria za ta fafata?
 6. Ina za a sanya kasashen Afirka?

Rahoto kai-tsaye

Daga Nasidi Adamu Yahya

time_stated_uk

Anan muka kawo karshen wannan shiri na musamman. Da fatan kun ji dadin kasancewa tare da mu. Za ku iya ci gaba da samun lamaranmu a shafin intanet, bbchausa.com sanna ku bibiye mu a shafukanmu na sada zumunta da muhawara.

Rukunin H

Poland za ta hadu da Senegal
Getty Images

Rukunin G

Ingila za ta kara da Tunisia
Getty Images

Rukunin F

Jamus za ta fafata da Sweden
Getty Images

Rukunin E

Brazil ta fado Rukukin E
Getty Images

Rukunin C

Faransa za ta gwabza da Peru
Getty Images

Rukunin D

Nigeria za ta kara da Argentina
Getty Images

Rukunin B

Iran da Morocco za su kece raini
Getty Images

Kasashen da ke Rukunin A

Saudiyya za ta hadu da Masar
Getty Images

Labarai da dumi-dumiNigeria za ta soma wasa da Croatia

Sweden ta fada Rukunin mutuwa?

 1. Germany
 2. Mexico
 3. Sweden

Senegal na Rukunin H

Ga kasashen Rukunin

 1. Poland
 2. Senegal
 3. Colombia

Panama za ta kara da Ingila

Ga kasashen da za su fafata a Rukunin

 1. Belgium
 2. Panama
 3. Tunisia
 4. England

Korea ta Kudu na Rukunin F

Kasashen da ke Rukunin

 1. Germany
 2. Mexico
 3. Sweden
 4. South Korea

Labarai da dumi-dumiMorocco za ta fuskanci Spain

Kasashen da ke Rukunin

 1. Portugal
 2. Spain
 3. Morocco
 4. Iran

Labarai da dumi-dumiAn sanya Nigeria a Rukunin D

Kasashen da ke Rukunin

 1. Argentina
 2. Iceland
 3. Croatia
 4. Nigeria

Labarai da dumi-dumiRussia da Saudiyya ne za su soma fafatawa

Kasashen da ke Rukinin A

 1. Russia
 2. Saudi Arabia
 3. Egypt
 4. Uruguay

Labarai da dumi-dumiPoland ta shiga Rukunin H

Labarai da dumi-dumiBelgium ta tsinci kanta a Rukunin G

Labarai da dumi-dumiJamus ta fada cikin Rukunin F

Labarai da dumi-dumiBrazil na cikin Rukunin E

Putin ya hadu da Infantino

Shugaban kasar Russia Vladimir Putin da shugaban hukumar kwallon kafar Duniya, FIFA, Gianni Infantino yayin da suke gaisawa a wurin rabon jadawalin gasar cin Kofin kwallon kafa ta Duniya.

Mr Putin na shan caccaka a wasu kasashen
Getty Images

Labarai da dumi-dumiArgentina ta fada Rukunin D

Labarai da dumi-dumiFaransa tana Rukunin C

Labarai da dumi-dumiAn sanya Portugal a Rukunin B

Akwai baraka a tawagar Senegal?

Wannan ne karo na biyu da Senegal ke halartar gasar cin Kofin kwallon kafar Duniya, inda fitaccen dan wasan da aka buga gasar 2002 da shi, Aliou Cisse ke jagorantar tawagar kasar.

Ya zabi 'yan wasa masu kwazo cikinsu har da Kalidou Koulibaly da ke buga tamaula a Napoli, da Idrissa Gana Gueye da ke buga wa Everton da kuma Sadio Mane da ke fafatawa a Liverpool.

Sai dai ana rade-radin cewa akwai baraka a tsakanin 'yan wasan, sannan ana tababar salon horaswar da Cisseke amfani da shi.

'Yan wasan bana sun fi wadanda suka yi wasa 2002 kwazo bayan da suka bai wa duniya mamaki inda suka doke Faransa.

Ana tababar salon horaswar Cisse
Getty Images

Maradona ya isa wajen rabon jadawalin

Tsohon dan wasan Argentina Diego Maradona da mai dakinsa yayin da ya isa zauren rabon jadawalin Gasar Cin Kofin Duniya na 2018.

Maradona ya yi shaharar da ba kowanne dan wasa ne ya yi ba
Getty Images

Wanne hali Brazil ke ciki?

Brazil ce kasar da ta fi yawan daukar Kofin Duniya, inda ta lashe shi sau biyar - a shekarar 1958, 1962, 1970, 1994 da kuma 2002.

Sai dai Jamus ta doke ta da ci 7-1 a matakin kusa da na karshe a gasar da ta karbi bakunci shekara hudu da suka wuce.

Babban dan wasanta: Neymar. Dan wasan na gaba da aka saya kan £200m shi ne babbar kadarar Brazil, a cewar tsohon dan wasan kwallon kafar kasar Pele, wanda ya goyi bayansa domin lashe kyautar Ballon d'Or.

Neymar ne babbar kadarar Brazil, in ji Pele.
Getty Images

Samuel Eto'o ya halarci wajen rabon jadawalin

Tsohon dan wasan Kamaru Samuel Eto'o yayin da ya isa zauren jadawalin Gasar Cin Kofin Duniya na 2018.

Samuel Eto'o ya taka rawa sosai a Gasar cin Kofin Duniya
Getty Images

Muhawarar da kuke tafka wa a BBC Hausa Facebook

Mika'ilu Ahmad Usman: Mu'yan Najeriya Allah ya sa a ba mu rukuni mai sauki amma fa ba tsoron kowacce kasa muke ba.

Sama'ila Ala Kwankwason Fulatan:To hukumar Fifa muna fatan za ki tsara jadawalin gasar cin Kofin Duniya da zai gudana a kasar Rasha 2018 a kan tsari mai kyau da adalci.

Ashiru Lawal Nagoma: Muna yi wa gwarzayen 'yan kwallon kafarmu na Super Eagles fatan zuwa Rasha da kafar dama domin samun tabuka abun a zo a gani.

Anya ba za a samu matsala a tawagar Nigeria ba?

Tawagar Nigeria ita ce za ta je Russia da 'yan wasa mafi jini a jika, kuma wadannan matasan 'yan wasa sun sanya wa 'yan kasar kwarin gwiwar ganin sun fitar da kitse daga wuta.

'Yan wasan na rige-rigen ganin sun samu gurbi a bangaren kai hari, inda 'yan wasa irinsu Kelechi Iheanacho, Alex Iwobi, Odion Ighalo da kuma Victor Moses ke son ganin sun bai wa mara da kunya.

Kyaftin John Mikel Obi da Wilfried Ndidi za su kare tsakiya.

Sai dai ana tababa kan ingancin 'yan wasan da ke tsaron gida da kuma mai tsaron raga ko da yake nasarar da Nigeria ta yi kan Argentina da ci 4-2 a watan jiya ta sa kasar ta ja hankalin duniya.

Tawagar Najeriya na cike da matasa
Getty Images

Mai rike da kambu

Jamus ke ke rike da Kofin Duniya a yanzu haka bayan ta lashe shi a gasar da aka yi a shekarar 2014 a kasar Brazil. Ta soma shiga gasar ne a 1908 kuma wannan shi ne karo na hudu da ta dauki kofin, wato a 1954, 1974, 1990 da kuma 2014.

Sau hudu Jamus na daukar Kofin
Getty Images

Wanne rukuni ne zai fi yi wa Nigeria dadi?

'Yan Najeriya sun soma tofa albarkacin bakinsu kan rukunin da suke so kasar ta fada a ciki.

Mene ne ra'ayin 'yan Nigeria?

An raba kasashe tukunya-tukunya

Tukunya 1: Russia, Germany, Brazil, Portugal, Argentina, Belgium, Poland, France

Tunkunya 2: Spain, Peru, Switzerland, England, Colombia, Mexico, Uruguay, Croatia

Tunkunya3: Denmark, Iceland, Costa Rica, Sweden, Tunisia, Egypt, Senegal, Iran

Tunkunya 4: Serbia, Nigeria, Australia, Japan, Morocco, Panama, South Korea, Saudi Arabia

An raba kasashe tukunya-tunkunya
Getty Images

Takaitaccen tarihin Gasar Kwallon kafar Duniya

An soma Gasar cin Kofin Kwallon Kafar Duniya ne a shekarar 1930, kuma tun daga wancan lokacin ake fafatawa duk bayan shekara hudu domin lashe Kofin in ban da a shekarar 1942 da 1946 da ba a yi ba saboda Yakin Duniya na Biyu.

An soma gasar a 1930
Getty Images

Jama'a barkanmu da saduwa a wannan shiri da zai kawo muku bayanai da sharhi kai-tsaye kan jadawalin kasashen da za su fafata a Gasar cin Kofin Duniya a Russia a shekarar 2018, tare da Nasidi Adamu Yahaya. Za ku iya bayar da gudunmawa ko tafka muhawa a BBC Hausa Facebook.