Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Fiorentina 1-1 AC Milan
 2. Liverpool 2-1 Leicester City
 3. Djokovic zai ci gaba da yin jinya

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

Bayyana ra'ayinka

Nan muka kawo karshen shirin da fatan za ku tara a mako mai zuwa

Liverpool 1-1 Leicester

Mohamed Salah

Liverpool 0-1 Leicester

Kai tsaye
Reuters

Liverpool 0-1 Leicester

Kai tsaye
BBC Sport

Muhawarar da kuke yi a BBC Hausa Facebook

Auwalu England Geographer - Up Liverpool duniyar kwallo za mu ci Leicester city 2-0.

Isyaku Hamza Gogori - Gaba dai gaba dai kungiyar kwallon kafa ta liverpool muna fatan zaku ci 3-0.

Bashir Bala Bunkure - In Allah ya yarda za a doke Liverpool da ci 1 mai ban haushi.

Newcastle 0-0 Brighton

Kai tsaye
Reuters

Chelsea 3-0 Stoke

Pedro

Kai tsaye
Reuters

Chelsea 2-0 Stoke City

Kai tsaye
EPA

Liverpool 0-1 Leicester

Kai tsaye
Reuters

Chelsea 1-0 Stoke

Antonio Rudiger

GOAL - Liverpool 0-1 Leicester

Jamie Vardy

Kai tsaye
Reuters

Bournemouth v Everton

Kai tsaye
BBC Sport
Kai tsaye
BBC Sport

Watford v Swansea

Kai tsaye
BBC Sport
Kai tsaye
BBC Sport

Newcastle v Brighton

Kai tsaye
BBC Sport
Kai tsaye
BBC Sport

Huddersfield v Burnley

Kai tsaye
BBC Sport
Kai tsaye
BBC Sport

Labarai da dumi-dumiChelsea v Stoke

Eden Hazard na Chelsea yana kan benchi shi kuwa Danny Drinkwater zai buga wa Stoke wasa.

Liverpool v Leicester

Kai Tsaye
BBC Sport
Kai Tsaye
BBC Sport

Ba na tsoron tafiyar Sanchez duk da cin kwallon da yake - Wenger

Arsene Wenger ya ce ba shi da wata damuwa a kan rasa Alexis Sanchez a watan Janairu, duk da kwallo biyu da dan wasan na gaba ya ci wa kungiyar da ta doke Crystal Palace 3-2.

Kwantiragin dan wasan na Chile zai kare ne da Arsenal a karshen kakar da ake ciki, kuma ana danganta dan wasan mai shekara 29 da tafiya jagorar Premier Manchester City, wadda ta kasa sayensa a karshen kakar da ta gabata.

Kai tsaye
Getty Images

Djokovic zai ci gaba da yin jinya

Novak Djokovic ya fice daga gasar Qatar Open sakamakon raunin da ya yi a gwiwar hannunsa.

Shi kuwa Andy Murray zai kara da Ryan Harrisonko kuma Leonardo Mayer a gasar tennis da za a yi ta Brisbane International a makon mai zuwa. .

Kai tsaye
Reuters

Virgil van Dijk: Liverpool ta sayi dan wasan Southampton a kan £75m

Dan wasan Southamton Virgil van Dijk zai koma Liverpool ranar 1 ga Janairu da zarar an bude kasuwar cinikin 'yan wasa a kan fam miliyan 75.

Tun bara ake sa ran dan wasan dan asalin Holland zai koma Liverpool bayan da shi da kansa ya nemi a sayar da shi.

Amma hakan bai yiwu ba saboda an tuhumi Liverpool da zawarcin dan wasan ba tare da sanin kungiyarsa ba.

Kudin da za a biya Southampton ya fi na kowane dan wasan baya da aka taba saya a duniya.

Kai tsaye
Getty Images

Serena ta dawo buga kwallon tennis

Serena Williams za ta buga wasan kwallon tennis a karon farko a Abu Dhabi, bayan hutun wata hudu da ta yi sakamakon haihuwa da ta yi. Za kuma ta kara ne da Jelena Ostapenko.

Kai tsaye
Getty Images

Celtic 0-0 Rangers

Kai tsaye
Reuters

Muhawarar da kuke yi a BBC Hausa Facebook

Muttawakkil Gambo Doko - Hakika wasan Liverpool da Leicester sai an tashi ganin yadda kungiyoyin guda biyu suke da gwarazan 'yan wasa wadanda suke kan ganiyarsu da fatan Allah ya ba wa mai rabo sa'a.

Sade Saidu Daura - Wuyar aiki ba a fara ba, hakika wannan wasa ne mai ban sha'awa, sai muce Allah ya kaimu lokacin lafiya, dan ba a san ma ci tuwo ba sai miya ta kare.

Musa Usman Dutsinma - Ina fatan Leicester zata ci leverpool 3-0 domin Arsenal ta samu damar matsawa daga inda take a yanzu.

Swansea ta nada Carlos Carvalhal sabon kocinta

Swansea City da ke kasan teburin Premier ta nada tsohon mai horar da 'yan wasan Sheffield Carlos Carvalhal a matsayin sabon kocinta.

Carvalhal dan kasar Portugal zai ci gaba da horar da Swansea ne har zuwa karshen kaka amma da nufin tsawaita kwantaraginsa idan kakar ta yi kyau.

Swansea ta dauki Carvalhal ne bayan Sheffield da ke Lig mataki na biyu a Ingila ta sallame shi a jajibirin Kirsimeti yayin da kungiyar ke matsayi na 15 a tebur.

Yanzu shi ne mai horar da 'yan wasa na biyar da Swansea ta dauka a shekaru biyu bayan kungiyar ta kori Paul Clement.

Kai tsaye
Getty Images

Harry Kane ya wuce Messi da Alan Shearer a cin kwallo

Harry Kane ya zura kwallo uku rigis, ya kuma kawar da tarihin bajintar cin kwallo mafi yawa a Premier a cikin shekara bayan da Tottenham ta caskara Southampton a Wembley 5-2.

Dan wasan na gaba na Tottenham da Ingila ya ci bal dinsa ta 37 a Premier a wannan shekara ta 2017 a minti 22 da wasa, ya wuce bajintar da Alan Shearer ya yi, lokacin yana Blackburn a 1995.

Latsa nan domin ci gaba da karanta labarin

Kai tsaye
BBC

Kungiyoyi shida da ke kasan teburin Premier

Bayan da aka yi wasannin mako na 20

Kai tsaye
BBC Sport

Yadda Lawro yake hangen za ta kaya a wasannin Premier

 • Bournemouth 2-0 Everton
 • Chelsea 3-0 Stoke
 • Huddersfield 1-0 Burnley
 • Liverpool 2-0 Leicester
 • Newcastle 1-1 Brighton
 • Watford 2-0 Swansea
 • Man Utd 2-0 Southampton
Kai tsaye
Getty Images

Italian Serie A wasannin mako na 19

 • Fiorentina da AC Milan
 • Atalanta da Cagliari
 • Bologna da Udinese Calcio
 • AS Roma da US Sassuolo Calcio
 • Torino da Genoa
 • Sampdoria da spal
 • Benevento da Chievo Verona
 • Internazionale da Lazio
 • Stadio San Siro Guiseppe Meazza
 • Hellas Verona da Juventus
Kai tsaye
Getty Images

Sharhi da bayanan Premier a BBC Radiyo

A shirinmu na sharhi da bayanai a gasar cin kofin Premier kai tsaye da harshen Hausa.

Wannan makon za mu kawo muku fafatawar da za ayi ne a daya a daga wasannin mako na 21 tsakanin Liverpool da Leicester City.

Za mu fara gabatar da shirin da karfe uku da rabi na rana agogon Nigeria da Niger, za kuma ku iya bayar da gudun mawarku a lokacin da ake gabatar da shirin a dandalinmu na muhawara da sada zumunta na BBC Hausa Facebook.

Gasar Premier wasan mako na 21

Gasar Premier Lik wasannin mako na 21

 • Chelsea da Stoke City
 • Liverpool da Leicester City
 • Newcastle United da Brighton & Hove Albion
 • Watford da Swansea City
 • Huddersfield Town da Burnley
 • Bournemouth da Everton
 • Manchester United da Southampton
Kai tsaye
Getty Images

Jama'a barkanmu da saduwa a cikin shirin labarin wasannin karshen mako ciki har da gasar Premier wasannin mako na 21 da za a kara, tare da fatan za ku kasance tare da BBC Hausa.