Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Real Madrid na son Neymar da Hazard da Lewandowski
  2. Ina ganin Sanchez zai koma Man United — Wenger
  3. Liverpool ta gaya wa Sevilla cewar ba za ta sayar mata da Sturridge ba

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

Sai gobe!

Karshen labarai da sharhin kenan game da kasuwar musayar 'yan wasa. Sai gobe!

Juventus na son dan wasan Arsenal

Hector
Getty Images

Nan gaba kadan ne kungiyar kwallon kafa ta Juventus za ta nemi dan wasan bayan Arsenal, Hector Bellerin a lokacin bazara. Kungiyar da ke kan gaba a gasar Serie A ta fara bibiyar dan kasar Spaniyan mai shekara 22 ne tun shekarar 2014.

Conte zai taya Fernando Llorente

Fernando Llorente
Getty Images

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Antonio Conte, yana son ya sake taya dan wasan Tottenham, mai shekara 32 Fernando Llorente, in ji Independent.

Ejen din Henrikh Mkhitaryan ya je Landan kan tafiyarsa Arsenal

Daily Mirror tana bayar da rahoton cewa ejen din Henrikh Mkhitaryan,Mino Raiola, yana Landan domin kulla yarjejeniyar komawar dan wasan tsakiyar Arsenal daga Manchester United.

A baya dai Arsene Wenger ya tabbatar da cewa an kusa cimma yarjejeniya kan dan wasan, yayin da ake sa ran Alexis Sanchez zai koma Manchester United.

Ejen din Mkhitaryan, Mino Raiola, shi ne ke wakiltar Romelu Lukaku da Zlatan Ibrahimovic da kuma Paul Pogba
Getty Images
Ejen din Mkhitaryan, Mino Raiola, shi ne ke wakiltar Romelu Lukaku da Zlatan Ibrahimovic da kuma Paul Pogba

Ko Guardiola zai sayi dan West Brom?

Jonny Evans
Getty Images

An shaida wa kocin Manchester City, Pep Guardiola, cewar za a sayar da dan wasan West Brom, Jonny Evans, mai shekara 30, kan kudi fam miliyan 23.5.

Kuma nan ba da jimawa ba ana tsammanin zai nemi sayen dan wasan, in ji Sun.

Pique ya tsawaita kwantiraginsa da Barca

Pique
Getty Images

Dan wasan bayan Barcelona, Gerard Pique, ya cimma yarjejeniyar tsawaita zamansa a kulob din zuwa shekarar 2022.

Sabon kwantiragin dai ya hada da zabi na fansa da ya kai kudi fam miliyan 440.

Ozil ba zai tafi ba — Wenger

Mesut Ozil
Getty Images

Kocin Arsenal ya hakikance akan cewar Mesut Ozil ba zai tafi ko ina ba a wannan watan.

Da aka tabaye shi akan ko Ozil zai bar Emirates a wannan kocin, sai ya ce a'a, yana mai karawa da cewa dan wasan zai ci gaba da taka leda a kungiyar.

Real Madrid na son Neymar da Hazard da Lewandowski

Real Madrid
Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta yi imanin cewa lokaci ya yi ta sayi dan wasan PSG, Neymar, da dan wasan Chelsea, Hazard da kuma dan wasan Bayern Munich Robert Lewandowski, in ji Marca.

Liverpool ta ce Sturridge ba na aro ba ne

Sturridge
Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta sanar da kulob din Sevilla cewar ba za ta sallamar mata da dan wasan gaban Ingila, Daniel Sturridge, mai shekara 28 ba, bisa yarjejeniyar aro zuwa karshen kaka ba, in ji Mail.

Wenger na ganin Sanchez zai koma Man United

Wenger
Getty Images

Kocin Arsenal, Arsene Wenger, ya ce yana kyautata zaton cewar dan wasan gaba Alexis Sanchez zai koma kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ne.

Kwantiragin Sanchez, mai shekara 29, zai kare a watan Yuni, kuma ana tunanin cewar ya cimma yarjejeniya da kungiyar ta Old Trafford bisa sharruda na kashin kansa.

Kun san kudin da Man United za ta bai wa Sanchez?

Sanchez
Getty Images

Yarjejeniyar da Manchester United take son ta kulla da dan wasan gaban Chile, Alexis Sanchez, daga kungiyar Arsenal, zai kai fam miliyan 180 bayan ya amince da kwantiragin shekara hudu da rabi, in ji Telegraph.

Man United ta fara tattaunawa da David de Gea

de Gea
Getty Images

Manchester United ta fara tattaunawa da mai tsaron gida David de Gea, wanda kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta dade tana hako, in ji Telegraph.