Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Sharhi game da musayar Alexis Sanchez da Henrikh Mkhitaryan
  2. Tattaunawar Arsene Wenger da manema labarai

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

Sai gobe!

Abin da ya samu kenan a labaran kasuwar musayar 'yan wasa. Sai gobe!

Rooney ya saka motarsa a kasuwa

Motar da Rooney ya saka a kasuwa
Getty Images
Motar da Rooney ya saka a kasuwa

Wayne Rooney ya saka motarsa samfurin BMW i8 a kasuwa, in ji Liverpool Echo.

Motar dai wadda ya saya cikin shekarar 2015 kan kudi kimanin fam 112,000 an saka ta a kasuwa kan kudi fam 64,995.

Cikin motar ce dai Rooney ya isa Goodison Park a taron manema labaransa na farko a watan Agusta.

A yanzu dai an hana shi tuki bayan ya amsa laifin tuki a lokacin da ya sha barasa a watan Satumba.

Wayen Rooney
Getty Images
Wayen Rooney

Javier zai bar West Ham

Javier Hernandez
Getty Images
Javier Hernandez

Dan wasan gaban West Ham, Javier Hernandez, zai iya barin kulob din a kasuwar musayar 'yan wasa ta watan Janairu kamar yadda ESPN ta ambato ejen dinsa yana cewa.

'Danny Welbeck ba zai bar Arsenal ba'

Wenger
Getty Images
Wenger

Kocin Arsenal, Arsene Wenger, ya ce dan wasan gaba Danny Welbeck ba zai bar kulob din ba a watan Janairu, duk da cewa Crystal Palace da Besiktas na son dan wasan, in ji Talksport.

Juventus na shakkar sayen dan Liverpool

Emre Can
Getty Images
Emre Can

Juventus ta amince tana tantama game da sayen dan wasan tsakiyar Liverpool, Emre Can, wanda kwantiraginsa zai kare a lokavcin bazara, in ji Mirror.

Palmieri ya yarda ya koma Chelsea

Emerson Palmieri
Getty Images
Emerson Palmieri

Dan wasan bayan Roma, Emerson Palmieri, ya yarda ya koma Chelsea kan wata yarjejeniyar shekara hudu yayin da ake ci gaba da tatatuanawa game da cinikin dan wasan da ya kai kudi fam miliyan 20. Komawar dan wasan mai shekara 23 Chelsea zai sa Kenedy ya koma Newcastle buga wasan aro, in ji Evening Standard.

Ajax ta sayi dan wasan Denmark

Kungiyar kwallon kafa ta Ajax ta bayar da sanarwar sayen dan wasan FC Midtjylland mai shekara 20, Rasmus Nissen.

View more on twitter

Madrid na son Salah

Real Madrid na shirin sayen dan wasan Liverpool, Mohamed Salah, mai shekara 25, a lokacin bazara kamar yadda Liverpool Echo ta ambaci shugaban hukumar kwallon kafa ta Masar yana cewa.

Salah
Getty Images

Arsenal za ta sake wata musaya?

Aubameyang
Getty Images
Aubameyang

Kungiya kwallon kafa ta Borussia Dortmund tana neman Arsenal ta ba ta dan wasanta Olivier Giroud, mai shekara 31, in har tana son ta ba ta dan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 28, ko kuma a dakatar da cinikin zuwa lokacin bazara, in ji Mirror.

Magoya bayan Arsenal, kun yarda a yi musayar Giroud da Aubameyang?

Kocin Liverpool ya nemi gafara

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp, ya nemi gafara game da ce-ce-ku-cen da ya kaur tsakaninsa da wani magoya baya a lokacin da kulob dinsa ya sha kaye a hannun Swansea ranar Litinin.

Jurgen Klopp
Getty Images
Jurgen Klopp

Wenger ya tabbatar Arsenal na son Aubameyang

Wannan ya nuna cewa Wenger ya tabbatar a hukumance cewar kulob dinsa na neman Aubameyang.

Mutane zao su so su yadda za ta kaya.

Aubamenyang
Getty Images
Aubamenyang

Shin Mkhitaryan da Ozil za su iya taka leda a kulob daya?

Wenger ya hakikance akan wannan.

ya ce: "Za su iya wasa tare mana."

Mkhitaryan
Getty Images
Mkhitaryan

Ku kalli bayan jaridu...

The i
The i

Ku kalli labaran wasannin da jaridu suka wallafa tukunna....

Daily Mirror
Daily Mirror
Daily Telegraph
Daily Telegraph

Manchester United ta fi samun kudi

Man United
Getty Images
Man United

kafar Deloitte ta wallafa wani rahoton da ke bayani game da irin kudaden da kulob-kulob na duniya ke samu inda ta ce kungiyar Man United ce ta fi samun kudi cikin shekara biyu a jere.

Rahoton ya ce kudin da Old Trafford ta samu na baya-bayan nan shi ne fam miliyan 581.

Sanchez ya rattaba hannu...

Sanchez na rattaba hannu
Getty Images
Sanchez na rattaba hannu

Baya ga musayar Alexis Sanchez da Henrikh Mkhitaryan tsakanin Man United da Arsenal, za mu tattauna kan abubuwa da dama ciki har da kayen da Liverpool ta sha a Swansea

Man City na son Aymeric Laporte

Aymeric Laporte
Getty Images
Aymeric Laporte

Manchester City tana son Aymeric Laporte kuma tana tunanin biyan fam miliyan 60 na sayen dan wasan daga Athletic Bilbao, in ji Sun.