Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Kano Pillars da Niger Tornadoes sun tashi 1-1
  2. Kano Pillars tana nan a mataki na biyu da maki 21
  3. Lobi ce ta daya a kan teburi
  4. Akwa da Enyimba sun kai zagayen gaba a kofin zakarun Afirka

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

Bayyana ra'ayinka

Nan muka kawo karshen shirin tare da fatan za ku tara a nan gaba don kawo muku wasanni kai tsaye daga sashen Hausa na BBC. Sai anjiman ku.

Wasannin mako na 14

Kai tsaye
@NPFL

Pillars 1-1 Tornadoes

Junior Lakosa yana da kwallo 11 a gasar Firimiyar Nigeria, kuma shi ne ke kan gaba.

1 Junior Lokosa 11

2 Nafiu Kabuga 6

3 Stephen Alfred 5

4 Ndifreke Effiong 5

5 Samad Kadiri 5

Kai tsaye
@NPFL

Kano Pillars 1-1 Tornadoes

An tashi wasa sun raba maki dai-dai a tsakaninsu.

Kano Pillars 1-1 Tornadoes

An yi karin minti uku.

Pillars 1-1 Tornadoes

Pillars ta saka Nazifi a cikin fili, inda ya sauya Rabiu Ali.

Kano Pillars 1-1 Tornadoes (Lakosa)

Pillars 0-1 Tornadoes

Kano Pillars ta samu fenariti bayan da dan wasan Tornadoes ya taba kwallo da hannu a cikin gida.

Pillars 0-1 Tornadoes

Pillars ta yi canji inda Adamu Hassan ya maye gurbin Nwagua.

Pillars 0-1 Tornadoes

An bai wa dan kwallon Tornadoes, Ifeanyi Okoye katin gargadi, sakamakon keta da ya yi.

Pillars 0-1 Tornadoes

Pillars ta sauya Anaezemba, inda Mustapha Salisu ya maye gurbinsa.

Pillars 0-1 Tornadoes

Tornadoes za ta sauya 'yan wasa biyu wato Ahmed Liman da kuma Bashir Usman, inda Isiyaku da kuma Nasidi za su maye gurbinsu.

Isiyaku da Nasidi 'yan karamar kungiyar Tornadoes ne.

Pillars 0-1 Tornadoes

Babawon Pillar ya kai kora, inda ya bai wa Abdulrasheed Nasidi tamaula shi kuma ya buga ta yi waje.

Pillars 0-1 Tornadoes

Alassan na Kano Pillars ya buga kwallo ta rikir-kita mai tsaron ragar Tornadoes Aliko.

Pillars 0-1 Tornadoes

An koma wasa bayan da 'yan kwallo suka yi hutu na rabin lokaci.

Kano Pillars 0-1 Tornadoes

Yadda kungiyoyin suka murza-leda

Kai hari zuwa ragal: 11-3Wadanda suka nufi raga: 1-2Kwana: 5-2Yin laifi: 2-5Satar gida: 0-0Jan kati: 0-0

Pillars 0-1 Tornadoes

An tafi hutu.

Pillars 0-1 Tornadoes

Mai tsaron ragar Tornadoes Aliko ya fadi an kuma duba lafiyarsa ya koma wasan.

Pillars 0-1 Tornadoes

Pillars ta samu dama mai kyau ta hannun Lokosa... sai dai kwallon da ya sakawa kai nan take mai tsaron ragar Tornadoes ya rike ta cikin ruwan sanyi.

Pillars 0-1 Tornadoes

Rabi'u Ali ya yi bugun tazara amma kwallon ta bude.

Pillars 0-1 Tornadoes

Andrew Ikefe ne ya ci wa Tornadoes kwallo daga bugun da Babawo ya yi na kwana..

Sakamakon Confederation Cup

Juma'a, 16 Maris 2018

Super Sport (South Africa)2-1 Atletico (Angola) (0-0)

Ahly Shendi (Sudan) 2-1CS la Mancha (Congo) (0-3)

Asabar 17 Maris 2018

APR (Rwanda)2-1Djoliba(Mali)(0-1)

Hilal Obied (Sudan)6-0 Olympic (Burundi) (0-0)

Nkana (Zambia) 1-0CR Belouizdad (Algeria)(0-3)

El Masry (Egypt)0-0 Simba (Tanzania) (2-2)

Club Africain (Tunisia)0-1RS Berkane (Morocco)(1-3)

Nouadhibou (Mauritania)2-4Raja Athletic Club (Morocco)(1-1)

Lahadi 18 Maris 2018

Cape Town City (South Africa) 1-2Costa do Sol (Mozambique)(1-0)

Enyimba (Nigeria)3-2 Energie (Benin) (2-0)

Fosa Juniors (Madagascar)1-0 Port Louis (Mauritius)(2-0)

USM Alger (Algeria)1-1 AS Maniema (DR Congo) (2-2)

Deportivo Niefang (Equatorial Guinea)1-0 Motema Pembe (DR Congo) (1-1)

Akwa United (Nigeria)1-0 (3-2pen) Al Ittihad (Libya) (0-1)

Ben Guerdane (Tunisia) 3-1CARA (Congo)(0-3)

Zamalek (Egypt) 2-1 (3-4pen)Wolaitta Dicha (Ethiopia)(1-2)

Pillars 0-0 Tornadoes

Babawo ya buga kwallo. amma Obiozo ya je wurin da wuri ya karbe tamaular.

Pillars 0-0 Tornadoes

Kano Pillars ta kai harin farko ta hannun Rabi'u Ali, amma kwallon ya yi waje.

Pillars 0-0 Tornadoes

An fara wasa tsakanin Kano Pillars da Niger Tornadoes

Pillars 0-0 Tornadoes

Za a fara wasa

Pillars 0-0 Tornadoes

'Yan wasan Tornadoes da za su buga fafatawar

David Obiazo 22Victor Dennis 27Chris Madaki 11Jamil Muhammad Jamil 15Adamu Murtala 3Joel Djondang4Nzube Anaezemba 24Alassan Ibrahim 8Rabiu Ali (c) 10Nwagua Nyima 28Junior Lokosa 21

Masu jiran kar-ta-kwana

Danladi Isah 31Ifeanyi Nweke 2Fahad Usman 13Mustapha Salisu 40Nazifi Yahaya 20Adamu Hassan 19Kamal Sikiru 12

Kai tsaye
@Niger Tornadoes FC

Muhawar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

Malami Ruwa Yabo: To ta Malam dai ba ta wuce Amin, muna fatar Allah ya sa ayi lafiya a kanmala lafiya.

Abuu-Ihsan Mustapha Umpha: Ina yi wa Kano Pillars fatan samun nasara da ci 3 da nema akan Niger Tornadoes.

Alh Saminau Daura Saminau: Allah Sarki Kano Pillars kuma kunsan mulkin kano ya janza,bana mantawa da kuka dauki kofi sau 3 ajere.

Hussaini Muhammad Imam: Haba kanawa ku kauce ga dodanninku sun shigo gari up Tornadoes Manyan Yara!

Aminu Fatakai Ringim: Yau masu guri za su karbi abun su wato Kano Pillars za su ci Tornadoes 2 da nema up up masugida.

Yobe Stars ta ci Pillars 2-0 a wasan mako na 12

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta yi rashin nasara a gidan Yobe Stars da ci 2-0 a wasan mako na 12 da suka kara a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria a ranar Lahadi.

Latsa nan domin ci gaba da karanta labarin

Kai tsaye
@NPFL

Lakosa na Pillars shi ne kan gaba a cin kwallaye

Kai tsaye
@NPFL

Pillars 0-0 Tornadoes

'Yan wasan Kano Pillars

David Obiozo 22.

Victor Denis 27.

Chris Madaki 11.

Jamil Muhammad Jamil 15.

Adamu Murtala 3.

Joel Djondang 4.

Nzube Aneazemba 24.

Alassan Ibrahim 8.

Rabi'u Ali 10.

Nwagua Nyima 28.

Junior Lokosa 21.

Masu jiran kar-ta-kwana

Danladi Isah 31.

Ifeanyi Nweke 2.

Fahad Usman 13.

Mustapha Salisu 40.

Nazifi Yahaya 20.

Adamu Hassan 19.

Kamal Sikiru 12.

Wasu sakamakon wasannin mako na 13

A ranar Lahadi aka buga wasu wasannin mako na 13 a Gasar Cin Kofin Premier ta Nieria.

Kai tsaye
@NPFL

Pillars 0-0 Tornadoes Alkalan da za su hura karawar

Alkalin wasa: Grema Mohammed

Mataimaki na daya: Dauda Hassan

Mataimaki na biyu: Kabir Bashir

Mataimaki na hudu: Francis Ogwu