BBC Hausa

Shafin Farko > Wasanni

Libya ta shiga sahun kasashe 50 a fagen tamola

Facebook Twitter
11 Apr 2012 14:32 GMT
Tawagar kwallon Libya

A karon farko a tarihi kasar Libya ta shiga sahun kasashe 50 da ke kan gaba a fagen kwallon kafa na duniya.

Libya ce kasa ta 46, watanni biyu bayan da suka halarci gasar cin kofin kasashen Afrika a karon farko tun shekara ta 1982.

Har yanzu Ivory Coast ce ta daya a nahiyar Afrika, inda kuma ta ke matsayi na 15 a duniya, yayin da Ghana ta motsa zuwa mataki na 22 a duniya.

Algeria da Mali da kuma zakarun Afrika Zambia, da Gabon su ne ragowar kasashen Afrikan da suka samu shiga rukunin kasashe 50 na farko.

Tunisia da Najeriya ne suka cike gurbin kasashe goma na kan gaba a nahiyar Afrika.

An fitar da Libya ne a zagayen farko a gasar ta Equatorial Guinea da Gabon, sai dai sun taka rawar gani bayan da suka doke Senegal da ci 2-1, sannan suka yi 2-2 da Zambia wacce ta lashe kofin.

Zakarun duniya da na Turai Spain su ne kan gaba a duniya, yayin da Jamus ta koma mataki na biyu, sai kuma Uruguay ta hauro mataki na uku a karon farko.

Tura wannan bidiyon

Email Facebook Twitter