Garejin mota ya fi gida tsada a Turai

Hakkin mallakar hoto b

Ba za ka iya zama a wurin da ake ajiye mota ba amma za ka iya biyan kudin da ya kai na sayen gida, a kan motar.

Kamfanin saye da sayar gine-gine na James Forbes, ya sayar da wani wuri a London a kan £1m kwatankwacin $1.33m.

Sai dai kuma wurin ba wani katafaren gida ba ne, illa dai wani kewayayyen filin ajiye mota a birnin Chelsea da ke a bayan gidan mutumin da ya sayi wurin wanda gidan nasa kansa ya kai Fam miliyan 25.

Masu harkar saye da sayarwar gidaje dai sun ce kudin gida mai aki biyu a Chelsea shi ne Fam Miliyan 1.4, a inda a Knightsbridge ma kudin na gida mai daki biyu shi ne Fam miliyan 1.9.

Kamfanin ya ce "Idan ka kalli irin yawan kudin filin fakin, za ka ga abin ya yi yawa amma dai kam filin na fakin na da darajar gaske."

Ba wai kawai a birnin London ba ne wurin ajiye motoci yake da tsada ba . Mutane kuma a birnin a shirye suke su biya ko nawa ne domin su samu wurin ajiye motocin.

A bara, an sayar da filin ajiye motoci a Kiribilli wata unguwa a Sydney, a kan Dala 90,900, a lokacin da ake yin gwanjon filin.

Kafin nan kuma an sayar da wani wurin ajiyar motocin a wani birni a kasar Australia, a kan Dala 195,150. Haka al'amarin yake a birane kamar New York da Boston.

Zuba makudan kudade a kan filin fakin "dai-dai yake da kudin sayen gida a wajen birane." In ji Rick Palacios, wani darekta a kamfanin saye da sayar da gidaje, a kuancin California.

Kamar dai yadda gidajen zama suke, mutane suna shiga kasuwa domin neman filin ajiye mota.

A birnin London, misali, darajar filayen ajiyar motoci ta kara dagawa, a 'yan shekarun baya, a cewar Charles Cridland wani wanda ya kafa sahfin intanet domin masu neman wurin ajiyar mota.

Ya kara da cewa masu son zuba jari a bangarori biyu sun yi wa kasuwar birnin London tsinke.

Ajin farko na masu zuba jarin sun karkata ne a fannin harkar saye da sayar da gidajen zama, a inda ajin masu zuba jarin na biyu suka mayar da hankalinsu wajen neman sayen wurare su kuma bayar da su haya domin riba.

Cridland ya ce bisa kididdiga, a birnin London, masu son zuba jari da ke sayen wurare ajiye motoci domin su bayar da su haya, za su iya samun ribar kaso 10 ko 15 na kudin a suka zuba suka saya. Ya kara da cewa "ko da masu saye da sayar da gidaje sun tsunduma a harkar yanzu kuma na fuskanci cewa sun fara tallan wuraren ajiyar motocin ga masu saye."

Faduwar kasuwar gidaje

Miller ya yi imanin cewa miliyoyin da ake kashewa a matsayin farashin wurin ajiye mota ba zai dore ba. In ji Jonathan Miller, shugaban kamfanin harkokin gidaje na Miller Samuel Inc. Ya ce masu wuraren ajiye motoci za su daina tsawwalawa saboda kasuwar gidaje ta yi kasa.

Kasancewar gida yana da wurin ajiye mota bai zama lallai ya hana ciniki ba.

Brian Lewis, wani mai saye da sayar da gidaje a kamfanin Halstead Property da ke birnin New York, ya ce masu gina gidaje suna samun karin basirar magance matsalar wurin ajiye motoci, a inda suke gina gidaje tare da yin garejin mota na karkashin kasa. Idan kana sha'awar karanta labarin na turanci za ka iya latsa wannan The parking space that costs more than a House