Ka kasa samun aiki? To ga shawara

Hakkin mallakar hoto Alamy

Akwai abubuwa da yawa da za ka yi wadanda za su fadada damarka ta samun aikin da kake cike da burin yi. Amma kuma mutane da yawa ba kasafai suke jarraba abubuwan ba.

Ga bayanin Elizabeth Garone

Karutan jami'a ya zo ya tafi, kuma duk irin roman-bakan da ke tattare da shi na zama wata muhimmiyar hanyar samun aiki ga sabbin wadanda suka kammala jami'a, har yanzu kana gefe guda, aikin bai samu ba.

Ka aika da takardar neman aiki sau shurin-masaki. Amma har yanzu shiru kake ji, kamar ka shuka dusa.

Daga nan hankalinka ya fara tashi. Ka fara tunanin cewa duk wannan shekaru da ka kwashe kana karatu, abin ya tafi a banza?

Ka duba ka gani idan za ka iya kokari ka samu wani horo ko 'yar kwarewa ta aiki da za ka kara a takardarka, wannan zai iya kara ba ka damar samun aikin da kake fata, domin zai sa masu daukar aiki su ga cewa ka dace.

Ka dauka kamar kana da aiki.

''Shawarar da ta fi kyau mai sauki ce, amma masu fafutukar neman aiki ba kasafai suke binta ba,'' in ji Ginger Porter, manajar darektar ofisoshin Dallas da Atalanta na kamfanin sadarwa na Golin. Ta kara da cewa, '' Ka soma kowace rana kamar ranar aikinka ce.''

Kada ka je ka zauna a daki kana ta kallon finafinai duk tsawon rana. Ka yi wanka ka sa kayanka masu kyau kamar daman kana da inda za ka je: neman aiki.

Shawarar Porter ita ce, ka rubata jerin sunan duk mutumin da ka sani, ko kake iya tunawa a fannin aikin da kake so. Mutanen su kasance wadanda za su iya taimakawa ne game da bukatarka ta neman aiki.

Ka nemi kowannensu damar wani dan zama da shi (na shan gahawa), ko 'yar tattaunawa ta waya ko ta wasikae email. Kada ka tambaye shi aiki.

''Ka gaya wa kowanne daga cikinsu abin da kake nema, kuma ka fayyace musu ainahin abin da kake son, misali ''ina neman matsayi kaza a ma'aikata iri kaza, inda zan yi amfani da kwarewata a fanni kaza da kaza. Akwai wata shawara da za ka iya ba ni?''' In ji Porter, ta kara da cewa, ''ta haka mutane za su ba ka shawara, kuma yin hakan ya fi a ce kana neman ganawa da su domin ka nemi aiki a wurinsu.''

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu neman aiki

Idan za ka yi ganawa ta keke-da-keke ne da mutumin, to ka gabatar da kanka yadda ya kamata wato kamar ma'aikaci, domin kana neman taimako ne, kuma kila ma ya tura ka wurin da za a dauke ka aikin.

Ka je a shirye, da misalan yadda ka yi amfani da kwarewar da kake da ita a baya, walau a rubutun da ka yi na kammala digirinka ne ko a wurin sanin makamar aiki ne. Manufarka a nan ita ce ka burge shi, ka nuna ka cancanta.

Kafin ka tafi daga wurinsa, ka tambaye shi ko akwai wurin wanda zai iya hada ka da shi. Ka yi haka da dukkanin sauran mutanen.

Porter ta ce, ''wannan mataki ne da zai iya daukar ka lokaci mai tsawo, domin karshenta za ka kai ga magana da mutane 100 ta wannan hanya, kuma ina tabbatar maka cewa daga cikin mutanen akwai wanda yake da aikin da ya dace da kwarewarka.''

Aikin da ba shi kake bukata ba

Idan ana gayyatarka ganawar daukar aiki, amma kuma ba aikin da kake da kwarewa a kai ba ne, kuma ba wanda kake sha'awa ba ne, to ka yi kokarin samun karin kwarewa a fanninka, in ji manajan darektan kamfanin daukar ma'aikata na Nonstop Recruitment Schweiz AG, wanda ke Prague, Oliver Donoghue.

Ka ga wannan na nufin kenan kila ka samu matsayin da ma ya dandara wanda kake sa rai.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Kada ka karaya

"Ba wai sai horon ya kasance wani babba ba. Ko da na dan lokaci ne a wurin aikin da ya dace da abin da ka karanta, domin zai nuna wa masu daukar aiki cewa lallai ka ba aikinka muhimmanci, kuma kana da burin samun kwarewa,'' ya ce.

Gabatar da kanka a takarda

Idan har ka yi wani zama na sanin makamar aiki a wani wuri a lokacin da kake makaranta, wanda yake da nasaba da fannin da ka karanta, kada ka rubuta shi kawai, ka yi bayani a kan shi da kyau, ta hanyar irin aikin da ka yi, a lokacin da kake wurin aikin, in ji Payal Vasudeva, manajar darektar a ofishin kamfanin Accenture Strategy da ke Landan.

Ta ce, "nuna irin kwarewar da ka samu a wata ma'aikata ko wurin aiki, walau ta hanyar neman sanin makamar aiki ne, ko ta hanyar aikin sa-kai da makamantansu, hakan na kara maka damar samun aiki.''

Idan kana bukatar kara darajar takardar bayanin karatunka da kwarewa (CV), to ka duba yadda za ka yi wani kwas na samun horon koyon aikin hannu wanda hakan zai kara maka kwarewa a fannin karatun da ka yi, kuma samunn wannan karin kwarewa wata dama ce a gare ka ta samun aiki, kamra yadda

Masu daukar mutane aiki za su rika duba wata alama ce da za ta nuna cewa ka dora a kan iya abin da ka nazarta a makaranta kamar yadda Donoghue ta ce.

Akwai hanya mai sauki ta yin haka: ka yi kwas a fannin fasahar zamani ko da kuwa ba a fannin fasahar zamanin za ka yi aiki ba. Wanna ilimi na da muhimmanci a zamanin yau da kuma gaba, saboda haka yana da muhimmanci ka lakance wannan ilimi, kamar yadda Sharon Schweitzer kwararre a harkar daukar aiki a Texas da ke Amurka ya ce.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Me neman aiki ta intanet

Schweitzer, ya ce, ''mun fahimci cewa ka san yadda za ka yi amfani da Pokémon Go, amma masu daukar ma'aikata na son sanin ko kana da kwarewa a kan wasu shafukan sada zumunta da muhawara na intanet, kamar su Instagram da Tumblr da YouTube, da kuma Twitter. Ka bunkasa kwarewarka.''

To da zarar ka yi wannan, ka nuna kwarewarka idan dama ta samu. ''Kana cikin 'yan zamani wadanda suke amfani da wayar komai-da-ruwanka da shafukan sada zumunta da muhawara wajen yin kusan komai, kama daga magana da abokai zuwa siyayya,'' in ji Vasudeva.

"Yayin da ka kai wannan matsayi a fannin aikinka, to ka rika duba jerin ayyukan da ake neman ma'aikata ta hanyar manhajojin tallata ayyuka. Ka rika amfani da da shafin Likedln da sauran shafukan sada zumunta na intanet, kuma ka nuna kwarewarka ta wannan fanni da kuma ta sanin aiki.''

Kana da tarin ilimi amma ba ka da kwarewa mai yawa ta taba yin aiki

Idan ba ka taba yin aiki ba a wata ma'aikata , to ka yi kokari ka koma fannin da za ka samu kwarewa ta hannu, kamar yadda Sally Walker, kwararriya a fannin horar da ma'aikata ta kasa da kasa da ke Landan.

Ka yi amfani da shafin farko, ka jera tare da bayar da bayyana fannoni zuwa biyar da ka samu horo na zahiri a cikinsu, wadanda duk suna da alaka da aikin da kake nema.

Ka fito da irin nasarorin da ka samu da wanna ilimi. Idan har yanzu kana ganin ba ka koshi ba, to ka yi kokarin samun kwarewa a fannonin bangaren da ka yi karatu.

''Ka sanya muhimman abubuwan da ka yi da kuma nuna irin nasarar da ka samu in har za ka iya nuna hakan, '' in ji Walker.

Misali za ka iya nuna irin aikin agajin da ka shirya a lokacin da kake jami'a. Ka nuna yadda za ta fito da cigaba da ka samu karara.

Ka kulla dangantaka ta zamani
Hakkin mallakar hoto alamy

Kulla alaka da mutane da yawa har yanzu muhimmiyar hanya ce ta yadda masu neman ma'aikata za su same ka in ji Donoghue.

Amma idan ba ka da lokacin da za ka halarci taron da kanka, za ka iya aiwatar da shi ta hanyar intanet kamar ta LinkedIn da Xing.

Ka tabbatar komai na bayaninka ka sabunta shi kafin ka fara kokarin kulla alaka da kamfanoni ko manajoji.

Amma fa ka kwana sanin cewa babu wata hanya da tafi ta ganawa da mutum gaba da gaba, kuma dole ne a wani lokaci ka je ka samu mutum da kanka in ji Donoghue.

Ka fadada fanninka

''Ba lalle ba ne damar aikin da za ta zo maka a ce ta shafi abin da ka karanta kai tsaye, kuma wani lokaci dole sai ka karkata zuwa wani fannin daban da na karatunka, kafin ka cigaba a fannin aikin naka,'' in ji shi.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Can't find a job? Try this simple advice