Mutumin da ya lalata duk abin da ya mallaka domin suna

Wani sabon baje-kolin kirkira da fasaha da aka yi a birnin Basil da ke Switzerland, ya fito da irin ayyukan Michael Landy wanda ya shahara a shekarar 2001, bisa lalata duk wani abu da ya mallaka a duniya da sunan yin zane. Alastair Sooke ya hadu da wannan mutumi ga kuma yadda haduwar tasu ta kasance.

Image caption Machael Landy mutumin da ya lalata duk abubuwan da ya mallaka.

Wata rana a shekarun 1998, Michael Landy, wani mai zane dan Burtaniya, ya yi tunanin wata sabuwar hanyar zane, a inda ya lalata duk abun da ya mallaka a duniya kuma a bainar jama'a. Ya kuma cimma wannan burin nasa ne bayan da ya hada kai da wata kungiyar masu zanen da ba na kudi ba ta 'Artangel' wanda ta kware wajen zaluko masu zane da ba kasafai ake samun irinsu ba a wannan zamanin.

Shekaru uku bayan nan, wato a shekarar 2001, Michael Landy ya yi kididdigar dukkan abin da ya mallaka a duniya wadanda suka tasamma 7,227. Daga nan ne sai ya samu na'uar da ake zubawa kaya ta dauka ta kai zuwa inda ake so, sai ya zuba dukkan kayan nasa da ya kwashe shekaru 37 yana tarawa, a kan na'urar. Ita kuma na'urar ta tura su zuwa wani shagon da babu komai a ciki da ke Oxford Street a tsakiyar birnin London.

Image caption Na'urar da Michael ya yi amfani da ita wajen kwaso kayan daga gidansa zuwa injin markade

A wannan shagon ne kuma Michael Landy ya kwashe mako biyu yana rugurguza da balla da karya da nike da kuma yaga duk abubuwan nasa da suka hada tufafi da takardun soyayya da zane-zane da motar kirar Turbo.

Ya kuma cimma hakan ne bisa taimakon wasu abokan 'yan kungiyar tasu ta zane-zane su 12. Babu dai abin da ya rage wa Michale illa wata kwat dinsa mai launin zargina da ta dade a jikinsa. Michael dai ya yi wa wannan shiri lakabin Narkarwa ko kuma 'break Down' a turance.

Jim kadan bayan Michale Landy ya gabatar da wani jawabi kan yadda ya lalata kayan nasa, yayin wani taro a gidan tarihi na Tinguely da ke birnin na Barsel, ya shaida min cewa "Makonni biyun da na kwashe ina wannan aiki su ne suka zamo min lokacin da na fi farin ciki a rayuwata." A yanzu haka, ina jin kamar mutuwata ta zo saboda mutanen da na kwashe shekaru ban gan su ba sun zo nan wurin, kuma na yi tunanin za su halarci jana'izata ne kawai. Amma kuma mafi yawancin lokuta, ina jin farin ciki kan cewa ba a taba samun wani mutumin ba a baya da ya lalata dukkan abin da ya mallaka ba sai ni."

Mallakar abubuwa a rayuwa

Image caption Wasu daga cikin kayan da Michael ya markade

Shekaru 15 bayan balbalcewar kayan da Michael ya mallaka, an bayyana zane-zane na 'Break Down' wanda Michael din ya kirkiro da tsarin zanen da bacin rai ya haddasa a Burtaniya. Bugu da kari, saboda karuwar yawan kalle-kalle a Yammacin Turai daga shekarar 2001, kamar misali bayyanar marubucin nan na kafar sada zumunta ta YouTube, Zoella wanda ya sadaukar da dukkanin hotuna masu motsi da ya sanya a kafar, ga yadda ake ake iya zura hannu a cikin jakunkunan da mutane suke zuwa cefane da su, da manufar sanar da 'yan sane hanyar yi wa mutane sata. Hakan ya taka rawa sosai wajen koyar da dabi'ar sane.

James Lingwood wanda ya kwashe shekaru 25 a kungiyar Artangel kuma mutumin da ya gabatar da tsarin Michael na narkar da abubuwa ko kuma 'Break Down' a turance ya ce "muna kallon zane-zane ta mahangar abubuwan da muka fi damuwa da su."

Ya kara da cewa "irin matsuwar da mutane suke da ita ta son kalle-kalle ko kuma karance-karance ta zamo wani bangare da hallayar mutane a wannan zamani, kuma akwai rashin jin dadi dangane da cewa wadan nan al'adun baki ne. Michael, ta hanyar tsarinsa na Break Down, ya dauko dala babu gammo a wannan zamanin namu."

Duk da cewa baki ya sha banban kan tsarin na Michael na lalata abubuwan da ya mallaka da ya kira Break Down, amma an gudanar da tsarin a wani shagon sayar da kaya marasa tsada mai suna Primark.

Image caption Motar Michael kirar Turbo wanda aka nike ta

Michael ya ce "wannan shagon shi ne ya fi da cewa da wurin da ya kamata a narkar da kayan saboda nan ne mutane suke zuwa domin siyayya." Sannan kuma an gudanar da lalata kayan ne a Oxford Street da ke tsakiyar birnin London, inda jama'a suka fi yin kai-komo a Burtaniya domin saye da sayarwa.

A lokacin an ba wa mutane mamaki domin da farko sun dauka kayan sayarwa ne, a inda wasu 'yan mata guda biyu suka kawo tufafin da suka siya domin a fansa a ba su kudinsu. Ashe kawai lalata kayan za a yi da suna wata sabuwar hanyar nuna fasahar zane. Kuma mutane sun sha mamaki da rikicewa ganin yadda aka zuba makudan kayan Michael a na'urar markade kaya.

Shin ko me yasa su rikicewa? Lingwood na kungiyar masu zanen da ba na kudi ba ta Artangel ya amsa tambayar da cewa "ba wani abu ba ne ga mutane su shaida lalata kayan gida kamar kayan karau irin su tangaran amma abun mamaki ne su ga ana nike ko kuma lalata abubuwa kamar wasiku da hotuna da zane-zane. Hakan na sa mutane su kadu."

Yadda aka nike kayan Michael

Dubban mutane ne dai suka taru suna kallon yadda aka nike kayan Michael. Sai dai kuma mutanen suna cike da takaicin dangane kan yadda aka lalata kayan. Ta wani bangare, za a iya cewa tsarin narkar da kayan na Break Down, ya yi dai-dai da cinnawa abubuwa marasa amfani wuta domin share tarkacen da ya addabi Yammacin Turai.

Lingwood ya yi tambaya a inda ya amsa ta da kansa. "shin wane sako ya kamata a fahimta dangane da markade kayan da Michael ya yi?" sai kuma ya ce "irin yawan abubuwan da mutane suke da su ya sanya ake musu kallon wadanda suka rabauta a rayuwar duniya. Idan ace kowa mallaki kayan da yawansu ya kai 7,227, ka ga ke nan ai da ya yanzu babu wannan duniyar domin tarkace ne zai yi mata yawa."

Bugu da kari, tsarin narkar da kaya na Break Down a wannan zamanin zai zama wata shaida da duniya ba za ta taba mantawa da mutum ba domin a kullum za a tuna Michael da cewa shi ne mutumin da ya lalata duk abin da ya mallaka saboda haka babu wanda zai manta da shi.

Lingwood ya kara da cewa "akwai annashuwa a cikin zubar da duk abubuwan da ka mallaka.

Image caption Yadda wasikin Michael suka koma bayan inji ya kacaccala.

Lingwood ya yi amannar cewa tsarin narkar da kaya na Break Down ba wai yana yakar saye da tara abubuwa ne ba, amma dai ya nuna irin alakar da ke akwai tsakanin dan adam da abubuwan da ya mallaka. Abin da Break Down yake magana akai shi ne alakar Turawan yamma da soyayyarsu ga mallakar kayayyaki. Sannan kuma tsarin yana da alaka da mutum ya tambayi kansa: ni wane ne?

Kafin Michael ya lalata kayansa

A lokacin da Landy yake shawarar bullo da tsarin Break Down, ya kwashe dogon lokaci yana tunanin ta yadda zai lalata kayan nasa. Amma kuma daga karshe ya yi tunanin hanyar ta yin amfani da na'urar kwasar kaya wadda ta mika su zuwa shagon da kan titin Oxford Street domin jama'a su ga kayan, har na tsawon minti goma, da ke cikin farantin da ya zuba su mai launin ruwan dorawa.

To amma kuma duk da Michael ya barnatar da duk abin da ya mallaka, sai ga shi a dakin da yake aiki a teburi sannan akwai amsakuwa da komfuta da kujera mai mazunin mutum uku sannan kuma akwai wata katafariyar kantar ajiye litattafai wanda take cike da mukaloli a kan zane-zane. Wannan dai na nufin babu yadda za a yi mutum ya tsira daga saye da tara abubuwa a rayuwarsa. Hakan ba zai yiwu ba domin ai kamar shakar numfashi ne.