Tasirin masarauta kan gwamnatin Birtaniya

Image caption Firaiministar Burtaniya, Theresa May ta rusuna a gaban sarauniya domin neman tubaraki

Hotuna sun nuna yadda sabuwar firai ministar Birtaniya, Theresa May ta durkusa a gaban sarauniya Elzaban. Kelly Grovier ya yi nazari kan wani hoton sassaka da aka yi tun karni na 16 wanda ya nuna irin wannan rusinawar da Theresa ta yi a gaban sarauniyar.

Bayan dai kwashe lokaci ana saɓata-juyata a siyasar zauren dokokin majalisar Burtaniya, Theresa May ta zama raba-gardama, a inda ta bayyana a matsayin firaiministan kasar wadda ta maye gurbin tsohon firaiminista, David Cameron, mai murabus.

Ranar Laraba kuma 13 ga watan Yuli ne sarauniyar ta Ingila ta karbi bakuncin sabuwar firaiministan, Theresa May.

A yayin ganawar ta Theresa da Sarauniya Elzaban, hotuna sun nuna yadda Theresa ta dukufa a gaban sarauniyar, a wani yanayi na ban girma ka masarauciyar.

Wannan dukufawa da shugabar jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya,Theresa May ta yi, a gaban sarauniya wadda ta gayyace ta domin tattaunawa kan yadda za a kafa sabuwar gwamnati, wani abu ne mai kayatarwa a kundin tarihin Burtaniya.

Idan za a kalli ma'anar hoton ta zahiri, to hakan na yin nuni da cewa har yanzu tsarin sarautar gargajiya na Burtaniya na da matukar tasiri a kan mulkin dimokradiyyar kasar.

Duk da cewa hoton yana cike ne da irin yadda matan guda biyu suke cike da fara'a ga juna da kuma irin ado da kayan ƙawa da sarauniya da firaiministan suka yi to amma hoton bai bayyana ko Elzaban da Theresa sun yi magana ba.

Alamun shiru tsakanin matan biyu ya kore duk wani hasashe da wani zai yi kan batun da suka tattauna.

Alamun shirun tsakanin sarauniya Elzaban wadda ta karbi Theresa hannu biyu-biyu, da ita kuma Theresar wadda ta kasance mai girmama sarauniyar, tarihi ne ya maimaita kansa domin hakan ya faru a baya kamar yadda wani hoton sassaƙa da aka yi, a karni na 16, a cocin Bacto da ke Herefordshire, ya nuna.

Image caption Hoton sassaka da ya nuna Blanche Parry ta zube gwiwa biyu-biyu a gaban sarauniya Elzaban ta 1, a karni na hudu.

Hoton sassaƙar dai ya yi nuni da cewa kame baki daga yin magana ga sarauniya wani daɗaɗɗen al'amari ne.

Kuma abin da hoton da fadar Buckingham ta fitar da yammacin ranar Laraba, yake nunawa shi ne girmamawar da firaiminista ta yi wa sarauniya, a inda ta risuna a gabanta.

Hakan kuwa ya yi dai-dai da yadda Blanche Parry, mai yi wa sarauniyar Ingila, Elzaban ta 1, hidima, ta ke faduwa ta yi gaisuwa a gaban sarauniyar.

Tun dai sarauniyar ta 1 tana karama aka sanya Blanche ta rika yi mata hidima kuma har ta zama aminiyar sarauniya.

Akwai wasu lokutan ma da sarauniya take dorawa Blanche wasu ayyukan masarautar da suka wuce mukaminta na asali na mai hidima.

Ta zamo mai kula da kayan yari da akwati da kuma litattafan sarauniyar.

Blanche ta zama mai kebewa sannan wadda ta san sirrin sarauniyar, har ma ta kai ga tana da ikon fada aji a sha'anin siyasar kasar.

To tambaya a nan, ita ce ko mene ne ya ba wa Blanche irin wannan karfin fada aji a Burtaniya?

Iliminta ne ko kuma basirar da Allah ya huwace mata? Ita dai sarauniya Elzaban ta 1, tana matukar kaunar biyayya, irin biyayyar da ake nunawa idan aka rusuna a gaban mai sarauta, ko da a zuci kuwa ba haka abin yake ba.

A wannan zamanin, sarauniya Elzaban ba ta da hotunan ban girma da kyaututtuka daga masu mulki masu yawa kamar yadda wadda ta gabace ta ta maƙala a fadar tata.

Irin gaisuwar ban girman da firaiministan Burtaniya, Theresa May ta yi wa sarauniya Elzaban, ƙarara ta yi nuni da irin biyayyar da ban girma da Blanche Parry take yi wa shugabarta ƙarni hudu da suka gabata.

Ma'ana yayin da ka Blanche ta yi ƙasa-ƙasa da kanta domin ban girma, daga ƙarshe sai abin ya juya ya zamo mata alkairi domin ta samu ɗaukakar da ba ta taba zata ba.

idan kana bukatar karanta cikakken labarin a harshen Ingilishi sai ka latsa wannan: The secret pantomime of power