Ko sabon fim din Jason Bourne zai ƙayatar?

Hakkin mallakar hoto Universal

Masu tsara fina-finai a Amurka, Matt Damon da Paul Greengrass, sun sake haduwa omin yin wani sabon fim mai suna Jason Bourne, bayan kusan shekara goma. Abin tambaya a nan shi ne shin ko za su iya tsara wani fim mai kayatarwa kamar irin wadanda suka yi a baya? Nicholas Barber ya yi nazari kan hakan.

Kwatsam, bayan kusan shekara goma da fitowar fim mai taken 'Bourne Ultimatum', wanda fitaccen jarumin nan, Jason Bourne ya bayyana a ciki, sai wani fim daban mai suna 'Bourne Again', ya sake fitowa wanda kuma Matt Damon da fitaccen mai shirya fim Paul Greengrass, suka yi tarayya wajen hada shi.

Tauraruwar jarumi Jason Bourne dai ta fara haskakawa ne a cikin littafin Robert Ludlum.

Kuma ya fara bayyana ne a fim mai suna 'The Bourne Identity' wanda Doug Liman ya tsara shi. Sai dai kuma Damon da Greengrass sun sanya hannu a jerin fina-finan.

A ganin karshe da muka yi masa, Bourne ya koma dan dambe. Abin dai yana da takaici ganin ba ya amfani da kwarewar da yake da ita wajen nuna jarumta a fina-finai.

Sai dai kuma ba laifin Bourne ba ne rashin yin amfani da kwarewar tasa, illa iyaka dai rawar da ya taka a matsayin mai kisan jama'a a fina-finai, ce ta yi tasiri a kansa.

A fim din na 'Bourne Identity' zance mafi shahara dai shi ne neman sanin wane ne Bourne da Julia Stiles ta yi ne ya sa mutane suka farga da wane ne Jason.

An kuma rikita Jason wajen neman sanin hakikanin shi wane ne, to amma tsawwalawar da Jason ya yi wajen yin tambayoyi sun fusata Tommy Lee Jones wanda shi ne shugaban Hukumar Binciken Laifuka ta Amurka wato CIA.

Tommy ya yi imanin cewa a samu wani makashi mai suna Vincent Cassel, ya aiki Jason domin daukar ran wasu iyalai, a inda ita kuma Alicia Vikander ta nemi da a janyo hankalin Bourne ya koma Hukumar ta CIA.

Bourne ya kasance yana watangaririya daga wannan birni zuwa wancan a nahiyar Turai. Kuma duk inda ya je, idanun makiyansa na kansa.

Greengrass, wanda ya tsara fim din ya yi amfani da karamar na'urar daukar hoto mai motsi ta hannu sannan kuma an hada hotunan ta yadda za su sanya mai kallo ya ji kamar za a iya harbin sa.

Masu tsara fina-finai dai suna ta fama kwaikwayon yadda aka tsara fim din, tun bayan fitowarsa.

Bourne, Jason Bourne

Ko da a ce Jason Bourne zai sake fim din da zai kayatar da masu kallo, to fa ba zai yiwu ba ya kayatar kamar yadda ya yi a baya ba.

Hakan kuwa ba zai rasa nasaba da karin maganar nan da ke cewa Kowa da zamaninsa.

Greengrass da Damon da kuma watakila Liman sun yi amfani da kimiyya wajen banbanta fim din Bourne da saura fina-finai.

Sun san abin da ya kamata su yi amfani da shi, a fim din domin banbanta shi da dukkanin wasu fina-finan leken asiri.

To amma yanzu zai yi wuya su kyale shi ya yi abin da ya ga dama ko kuma ya taka rawa da tafi wadda ya taka a fina-finan da ya yi kamar 'bourne Supremacy' da 'bourne Ultimatum'.

Ko ma dai zai taka irin waccan rawar to ba za ta kyayatar da masu kallo ba kamar a baya.

Kuma ma ai kamata ya yi sunan fim din ya zama 'chasin' Bourne.

Wasu lokutan, maimaita abu yana sanya mai kallo ya ki kallo. Haka abin yake, misali idan aka ce har yanzu Hukumar CIA tana farautar Bourne, abin da hukumar ta fara shekaru 14 a fim din 'Bourne Identity'.

Bisa la'akari da irin makudan kudin da suke da su da ma'aikata da kuma kayan aiki masu amfani da fasahar zamani, ya kamata ace sun kama shi.

Shin ba zai fi ba idan suka mayar da hankalinsu a wajen farautar 'yan ta'adda ba?

Wata matsala da ake gani ga sake haduwar Greengrass da sauran wadanda suka tsara fim din 'Bourne Identity', ita ce yanzu haka Greengrass ya fi mayar da hankali kan fina-finan leken asiri fiye da a baya.

Sannan yana amfani da hotuna marasa inganci wadanda masu kallo ba sa son irin su.

Wata matsalar har yanzu dai ita ce shi Greengrass yana kokarin yin fina-finai biyu ne a lokaci daya kamar yadda ya yi a baya.

Kamata ya yi sunan fim din dai ya zama "Chasin' Bourne".

Sabon fim din dai yana kwaikwayon shafin nan mai tona asiri na Wikileaks da kuma mutumin da ya yi suna wajen bankada bayanai sirri na kasar Amurka, Edward Snowden.

Tuni wasu masu tsara fina-finan suka fara kwaikwayon hakan. Idan kana son karanta labarin na Turanci, za ka iya latsa wannan Is Jason Bourne worth the Waiting?