Yadda kuda ke sanar da mu rayuwa

Wannan dan mitsitsin kwaron da mu ke kora daga kan abincinmu, shi ne silar gano wasu daga cikin manyan batutuwa na kimiyyar zamani.

‘Yan kananan kudaje, samfurin da a kimiyance ake kira Drosophila melanogaster, sun fi shekaru 100 su na taimakawa masana kimiyya wurin nazarce-nazarcensu.

Hakkin mallakar hoto Alamy

Dalili kuwa, saurin haihuwarsu na bai wa masana damar nazartar ‘ya’ya da jikoki cikin kankanin lokaci. Ga su da saukin kiwo. Macen kuda kan nasa kwayaye 30-50 a kullum har tsawon rayuwarta, kuma kwaikwayen kan kyankyashe cikin mako guda zuwa biyu. A cikin makonni 3-4 kuma su kan iya zama kakanni.

Kankantarsu ta sa ana iya kiwata miliyoyi a dakin bincike tare da ciyar da su wadataccen abinci, na dusar masara mai araha.

A 1933, Thomas Hunt ya lashe kyautar Nobel sakamakon nazarin yadda kudan Drosophila ke gadon kwayoyin halittar da ke sa shi ya yi jan ido ko fari. Wannan bincike shi ya kai gano cewa kwayoyin halittar da ake yi a cikin DNA na kunshe ne cikin abinda ake kira chromosome, wanda shi ne silar da ‘ya’ya da jikoki ke gadon kammanin iyayensu. Wannan shi ne tushen fannin ilimin nazarin gadon kwayoyin halitta da ma nazarin kwayoyin halittar kansu.

Hakkin mallakar hoto Alamy

Tun daga wancan lokacin, binciken da aka yi a kan Drosophila ya yi sanadiyyar lashe kyaututtukan Nobel har biyar a shekarun 1946, 1995, da 2011. Ilimin da mu ke da shi yanzu game da yadda muke girma, da dabi’o’inmu da kuma yadda mu ke tsufa duk an gina su kan ginshikin binciken rayuwar kudajen Drosophila.

Ana kara nazarinsu ana kuma kara gano kamanceceniyar da ke tsakaninsu da mutane: Kaso 75% na kwayoyin halittar dan Adam na da takwara a cikin kwayoyin halittar kudan Drosophila. Kudan Drosophila na da tagwayen chromosomes guda hudu, wadanda ke kunshe da kwayoyin halitta 14,000. Mutane kuma su na da kwayoyin halitta 22,500.

Hakkin mallakar hoto Alamy

Wannan kusanci na adadin kwayoyin halittunmu ya sa ana iya kwatanta sakamakon gwaji a kan kudan Drosophila da yin gwaji kan mutum. A kan ba su giya su yi tatul, domin nazarin tasirin giya kan bil’adama. A kan yi nazarin bacci da dangantakarsa da shan kofi, ta hanyar bai wa kudajen Drosophila kofi.

Ta wannan hanyar ne aka gano cewa kudajen da suka tsufa baccinsu bai kai na yara ba. A jikin kudan Drosophila aka fara gano kwayar halittar da ke sa gajiya idan an yi bulaguro a jirgin sama, daga bisani ne kuma a gano cewa mutane ma na da wannan kwayar halittar.

Dubunnan manazartan kimiyya na yin bincike kan Drosophila a sassa dabam-daban na fadin duniya, har ma da wajenta.

Hakkin mallakar hoto Alamy

Kudajen Drosophila ne halittar farko da aka harba wajen duniya zuwa Sararin Subhana. A yanzu haka kuma akwai dakin gwaji kan rayuwar kudan Drosophila na din-din-din a tashar bincike kan Sararin Subhana.

A wannan dakin binciken ne ake gudanar da nazarce-nazarce kan abinda ya sa ‘yan sama-jannati ke saurin kamuwa da cuta a wajen duniya

Idan har kusancin kwayoyin halittarmu na da irin wannan alaka ta kut-da-kut da kudajen Drosophila, ya aka yi siffar halittarmu ko kusa ko alama ba ta yi kama ba? Dr. Peter Lawrence, marubucin littafin “Yadda aka samar da kuda” ya bayyana wannan tambaya a matsayin “sirrin rayuwa na uku”.

Hakkin mallakar hoto Alamy

A wata hira da yayi da tashar Radio 4 ta BBC, Dr. Lawrence ya ce sirrin rayuwa na farko shi ne tsarin sauyawar halittu daga wani jinsi zuwa wani jinsin dabam, wanda Charles Darwin ya gano, abinda ya ce: “shi ne asalin duk wani tsiro da dabba dake fadin duniya”.

Ya kuma kara da cewa: “Sirrin rayuwa na biyu shi ne gano DNA - wanda yake kunshe da bayanan rayuwar kowacce halitta, tare da siffofi, da dabi’un ‘ya’yan da za ta haifa – domin kuwa ba don shi ba da ba mu san yadda rayuwa ke dorewa ba.”

Sirri na uku shi ne abinda Dr Lawrence ke kallo a matsayin mafi girman matsalar da masana kimiyyar rayuwar halittu za su yi kokarin warwarewa a nan gaba.

Ya ce: “Saboda abin ya zame mana jiki bama ko kulawa da shi. Me ya sa ake samun bambanci tsakanin mugun dawa da dorinar ruwa?”

“Idan ka duba kwayoyin halittarsu bambancin bai taka kara ya karya ba. To me ke sa kirar jikinsu ta bambanta sosai da sosai? A ina ne ake kunsa bayanin tsawon hancinka, kuma bisa wani tsari ne ya sa ka na girma hancin ke tsayawa a iyakar wani kayyadajjen tsawo? Me ke sa ‘ya’ya su yi kama da iyayensu? Me ke jawo bambanci a siffar fuskokinmu? Duk ba mu san wadannan ba.

“Ni a ganina wannan ita ce babbar tambayar da har yanzu ilimin nazarin halittu bai kai ga samo amsarta ba, kuma wannan shi na kira ‘sirrin rayuwa na uku’. Ga shi dai kullum yana faruwa amma mun rasa ta inda zamu tunkari neman amsarsa.”

Hakkin mallakar hoto Alamy

Manazartan kimiyya dai na kokarin binciko wannan amsa ta hanyar kudan Drosophila. A yanzu haka sun ware kudaje masu manyan fika-fikai da zimmar binciko wadanne kwayoyin halitta ne ke sa girman fika-fikansu su dara na saura.

Masanan sun kuma nazarci dangantakar da ke tsakanin dangogin kudaje masu kusancin kwayoyin halitta domin gano kwayoyin halittar da ke jawo bambanci a halittarsu ta zahiri.

Haka kuma sun gano cewa ‘yan matan kudaje sun fi son mazajen da fika-fikansu su ka fi yawan launuka masu haske.

Sai dai a ganin Dr Lawrence, wadannan nazarce-nazarcen da ake gudanarwa a yanzu, su na bada muhimmiyar gudunmawa wurin gano daidaikun abubuwa, amma ko kusa ko alama ba su ma tunkari alkiblar fara yunkurin amsa babbar tambayar ba, kuma akwai bukatar a fara tunkarar amsata.

Koma dai yaushe aka fara kokarin lalubo amsar, Dr Lawrence na kyautata zaton cewa ta hanyar nazarin kudajen Drosophila za a kai gare ta.

Idan kana so ka karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. How the humble fruit fly is answering life's big questions.