Yadda cutuka ke taruwa a ƙarƙashin farce

Wanke hannu shi ne babbar kariya daga dukkan wasu cututtuka masu illatarwa. To amma shin kana wanke ƙarƙashin faratan ka?

Wataƙila ka san cewa wanke hannu shi ne babban matakin kare yaɗuwar cututtuka. A ko ina jami'an lafiya na tabbatar da cewa masu aiki a gidajen abinci na wanke hannun su yadda ya kamata. To amma fa ko ya ka kai da wanke hannu babu yadda za a yi ka raba su da ƙananan halittu na Bactariya da za su iya haifar da cutuka.

Domin gujewa yaɗuwar irin waɗannan ƙananan halittu na Bactariya a hannu ya sa likitoci da masu jinya ke sa safar hannu a lokacin da za su duba mara lafiya.

Wasu masu bincike da suka yi aiki kusan shekaru 100 da suka gabata, sun gano cewa ƙananan halittun na Bactariya na ƙara haɓaka, ko da kuwa sau nawa ka wanke hannu.

To amma sai wajen shekarun 1970 masu bincike su ka fara gano dalilan da ke sa ƙananan halittun na bacteria ke da naci.

Rufe farata na daga abubuwan da ke sa hannu ya dade a tsaftace, to amma fa ba a saman faratan ne cutuka ke samun mafaka ba, suna laɓewa ne a ƙarƙashin farata. Kuma ƙarƙashin farce shi ne ma ya ke renon kwananan halittun na bacteria.

Hakkin mallakar hoto Getty

Kuma sai a ƙarshen shekarun 1980 ne masana suka fara bincika ƙarƙashin faratan, don ganin irin halittun da suke rayuwa a wajen.

A shekarar 1980 wasu masu bincike uku a sashin fata na jami'ar Pennsylvania sun yi nazari kan ma'aikata 26 na jami'ar a ɓangaren kula da lafiya, waɗanda kuma ba bu wanda ya yi mu'amala da mara lafiya a cikin su.

Sun gano cewa tazarar da ke ƙarƙashin farata da fata wani muhimmin wajen ƙyanƙyasar ƙananan halittun na bacteria ne.

An kuma gano cewa sauran sassan hannayen mutanen, waje ne da dubban ɗaruruwan halittun bacteria ke hayayyafa.

Masu binciken sun kuma ce me yiwuwa tazarar da ke akwai tsakanin fata da kuma ƙarƙashin farcen shi ne ya ke bada wannan dama ta bunƙasar bacteria.

Ka yi tunanin cewa, tazarar da ke tsakanin farce da kuma fata tana tara ƙwayoyin cuta, hakan na nufin cewa ya kamata mu nemi hanyoyin da za mu ringa kawar da yaɗuwar ƙwayoyin cututtuka a wajen.

Wannan fa ba wai ana magana ne kawai kan farata na jiki ba, har ma faratan da ake ɗorawa a matsayin ƙari, har ma da 'jan farce' da ake yin ado da shi.

Hakkin mallakar hoto Getty

Shekara ɗaya bayan binciken na jami'ar Pennsylvania, wasu ma'aikatan jinya sun rubuta cewa; "duk da ya ke ba a samar da cikakkun bayanai ba kan illar ƙarin farce da sa jan farce ba, ma'aikatan lafiya mata da dama sun dakatar da yin ado da su.

Wasu masu bincike sun gano cewa jami'an jinyar da ke da farata da yawa da kuma masu ƙarin farce sun fi tara ƙwayoyin halittar bacteria a hannayen su.

To sai dai hakan ba ya na nufin cewa suna sakawa marasa lafiya ƙwayoyin ba.

Ana tunanin cewa gwargwadon yawan ƙwayoyin halittar na bacteria da ke hannun mutum, gwargwadon yawan cutukan da za su haifar a hannun.

Ana kuma nuna fargabar cewa idan mutum ya karce farcen sa nan ma zai zama wajen ƙyanƙyasar ƙwayoyin bacteria.

Binciken ma'aikatan jinyar ya samu hujjar cewa masu ƙarin farce ba sa wanke hannu sosai, abinda hakan ke nuna cewa za a samu matsalar ƙaruwar ƙwayoyin cuta.

Kuma masu ƙarin farce na saurin yaga safar hannu a lokacin da suke duba marasa lafiya.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wanke hannu kawai bai isa ba, dole ne ka tabbatar da cewa faratan ka suma a tsaftace su ke.

Masu binciken dai sun yanke hukuncin cewa yanke farce da kuma wanke shi, shi ne mafi mahimmanci daga sa jan farce, ko kuma ƙarin farcen.

Mutane miliyan biyu zuwa uku suna mutuwa a kowace shekara sakamakon cutar gudawa. Ana ganin dai cewa yin amfani da sabulu wajen wanke hannu zai taimaka wajen rage yawan miliyoyin cututtukan da ke damfare a hannun.

Wani abu mai mahimmanci baya ga wanke hannu, shi ne mayar da hankali wajen tsaftace karkashin farce a lokacin wanke hannun. Kuma yanke farce shi ne mafi a'ala kasancewar sa maboyar ƙwayoyin cuta.

To amma wani abu mafi muhimmanci shi ne idan kana son kan da arziki ka daina cire farce da haƙori.

Idan kana son ka karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. What lives under your fingernails?